← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 67

Sashe 16

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🅿️ 37__38
*Ban manta dake ba yayata takai na SARAH ina alfahari dake* *Allah ya bar kauna da zumunci ina yinki irin sosai dinnan*
*Up up up STAR .W.A hakika ina* *alfahari da ku yan kungiyar mu musamman ma*
*Antyna Momyn Mufeedah* ..
*Hadjara (Arfat)*
*Mimsqueen*
*Ummu Usmane* *(i miss you keda* )
*My in-law Queenbaby* ..
*Allah ya qara hada kammu ina kaunar irin totally dinnan* .
Dedicated to all my fans
37--38
```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya na daga alamar kyawun musulunci mutum ya bar bin duk wani abun da bai shafe shi ba "
Tirmizi ne ya rawaito shi.
```
A bangaren Maysam kuwa tana shiga falon da sallama a bakinta amma setaji shiru wata hamdalah tayi tare dasakin murmushi jin dadin dabata taras dashiba isa dining tayi ta aje mishi tea din sum2 cikin sauri tayi hanyar futa amma mi se taji yace ke zo nan...
Dan danan dariyar jin dadin data ke ta gushe ta tsaya cak ta kasa gaba kuma taka sa yin baya ...
wata uwar tsawa ya daka mata dan tsoro bata san lokacin data zube nan ba dan kafafuwanta gaza daukar ta sukayi dan ta razana sosai ...da rarafe ta isa inda yake tuni har kwalla ta cika mata ido. Tayi kalar tausayi
Se kawai yaga kamar sweetbaby shi idan tayi b'anna wato idan tayi laifi ko kuma idan taji tsoro ....
Runtse idon shi yayi wata zuciyar tace ka tausaya mata mana ko dan tana kama da babynka...
Wata zuciyar tace mishi a a kada ka raga mata ai dan tana kama da ita ne ma ya kamata ka bata wahala kamar yanda take ba zuciyarka duba da tun da tashigo rayuwarka ta tado maka da ciyon daya dade da warkewa ....beyi wata2 ba yabi umarnin zuciyarshi ya zare belt dinshi ya zula mata daya yace wannan na qara hawa cinyar Momy ne
seda ta gantsere saboda zafi.
Ya dadage iya karfinshi se qara mata ...
Mi Maysam zatayi da gudu ta shige jikin shi ta cukukuye shi
Wani mayan shock yaji gaba daya jikinshi ya saki yayi tagal2 suka zube bisa kujerar palon ...
Maysam wacce tun dazu idonta ke rumtse se yanzu ta bude su jin sun zube ..
Waro idon tayi ta kama bakinta ...
Shi kuma gogan sandarewa yayi sakin baki da hanci yayi ya zuba mata ido bako kiftawa itama Maysam din kasa janye idanunta tayi dan ta tsorata jiran hukunci kawai take
Sun jima a haka ita tana son tserewa amma gogan ya kasa ya tsare ya riketa da hannushi ...kuma ya fada kogin tunani.....
Mutsu2 da take ya dawo dashi da sauri ya tureta taee da hankada ta lokaci guda kuma ya daka mata tsawa ta fice mishi a daki ..
Gaba daya ya gigita ta ..tama rasa ina ne kofar fitar seda taga ya taso ya nufo ta cikin tsawa yake fadin "je dis sors de ma maison "
da gudu ta fice kan kace mi har ta isa bangaren Fulani se haki take ..nan kofar palon ta tsaya tana meda numpashi seda taji normal tukon ta shiga "heureusement"(luckily) Fulani bata palon direct room din ta tashige a ranta tayi hamdalah da Allah ya kubutar da ita a hannunshi da taci na jaki yau ta shafa bayanta tace nasan kila da ya qara min wata da bayan nan ya gama moruwa.....
A bangarenshi kuwa rasa abunda yake mishi dadi yayi kwata2 yarinyar nan ta haddasa mishi fadawa tunanin babynshi a ranshi yace kai dolema na kaita school gobe2 nan ko zanma dena ganinta kwata2...yaja dogon tsaki mtssss
Washe garin kuwa suka kama hanyar Maradin dayake tun a daren ya sanarwa Fulani da me martaba a cewarshi wai an tsere mata a karatun dan haka gwara ta tafi kota cin munsu
Tun adaren tashirya kayanta tsaf akwati ukku manya komi na bukata ta dauka wanda kuwa bata da se gobe yarima ya kaita shopping .
A shopping dinma tsayawa tayi bata dauki komi ba seda taga Murad yayi mata jan ido tukon ta dauki mai da turaruka shima bawai dan batada suba aa kawai dande tsoran fadan yarima
Shikuma wurin kayan ci ya tafi yasa yaran wurin suna jidowa kamar madara lipton Milo etc...komi a wadace ya saye dan Momy seda tayi mishi kashe kwakwara kafin su fito
Haka ya biya kudin aka jida musu a motar da kuyangi duke suka fice se Maradi.
Yana tuki a ranshi yace ya akayi bega yarinyar nan ta dauki pad..wata zuciyar tace mishi peut etre (may be) bata faraba ma..yace amma walahi angama dani (jifa to mi ruwanka ciki kawai iyayi
)
Juyowa yayi yana kallonta ..ita kam se sharara bacci take ..besan lokacin dayace bacci nayi miki kyau...se kuma yace to mi ruwana ciki..tsuka yaja ya cigaba da tukinshi...(kadeji da gulmarka ehe)
Tafiyar awa ukku sukayi suka iso wani shago ya shiga ya sayo mata simkin pad din gabad'aya...
Har llokacin bata farka ba..
Wani haushin ta ya karaji
Tana baccita me dadi cike da mafarkai masu dadi taji saukar ruwan sanyi a fuskarta firgit ta bude ido kamar zatayi kuka amma ganin dodonta ne seta sadda kanta kasa..
Suna isa makarantar dayake abun na sune nan aka cicika komi ya zuba kudin shekarun shidda dazatayi wato secondary
da kudin furniture dana uniform duka komi ya biya
Har dakinta kuyangi sukakai mata kayanta ......daza su tafi da kyar suka rabu da kuyangin...barema da jakadiya rumgume ta tayi se rusa kuka take...
Lallashin ta tayi tace kiyi hakuri naso zama nan kai hatta fulani taso a baki koda kuyanga dayane amma yarima yace aa a barki ai school kikazo ba hutu ba .shiyasa nakeso kidage kiyi karatunki banda wasa..kada kiyi kuka kijawa kanki ciwon kai dama gana safe dakikayi wajen rabuwa da fulani...
Share hawayenta tayi tace shikenan zan baku mamaki in sha Allah ..
Yarima murad seda ya biya gidansu Mahmud ya gaisar da iyayenshi sannan suka kama hanyar komawa
A bangaren su waziri kuwa samako yayi ya nufi wurin boka amma har yamma be samu wajen ba ya gaji likis dole ya hakura ya dawo gida
Ya labartawa Madina komi wani bacin rai taji tace mu bari har murza taji dan sauki se muje ta nuna muna amma kada ya fice satin nan dan asabar din nan ze koma England nan da 6 jours kenan......
Kuma wani babban bakin ciki yau yayi tafiya shida kucakar matarshi abunda ya kullar dani ma shine da kanshi ya jasu ashe dana sani da munyi anfani da wanna damar mu qara cire musu burki..
bansan da tafiyar ba seda zasu tafi shima a bakin jakadiyata naji koda na fito tuni har sun bar cikin fadar ..takaici kamar na mutu...
Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba..
Love all fans
[8/17, 1:57 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[8/17, 2:00 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 16 · 0% Book details