← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 67

Sashe 63

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wuyar data ke sha tana ganinshi ta mika mishi hannu alamun yazo ..ai da gudu ya isa yasa guiyoyin shi kasa tare da rike mata hannu ...idon nan nashi yayi jajur alamun yasha kuka kenan ....ita ma ido duk su firfito se zufa take...tana jujuya kai kukan ma yaki zoma ta ....

Likitoci kam kallon ikon Allah suke ..shi yazo ya hanasu aiki kuma shima bayi yake ba da kyar suka lallabashi ya fita a cewarshi ze doko rigarshi ta likitoci dan baze iya barin wify shi itakade ba...

Yana fitowa ya shige office ya doko rigar..ze koma Mahmud da fulani na bashi hakuri kan yabari sauran docto suyi aikin su aman fafur yaki suna haka se kuwa ga Sarki ,M.Musa da kuma Dad suna shigowa asibitin suma .. Nan yaje ya rumgume sarki har da yar kallarshi kan wai su fulani sun hanashi shiga.... kallo daya sarkin yayi mishi ya ga baya cikin nutsuwarshi ..ko ya shiga ma ba wani abun ze iya ba dan duk ya wani gigice .....
sarki ya shiga bashi baki se suma su dad suka shiga zancen da kyar ya hakura de ya zauna zaman jira ..aman bini2 se ya lekata ...

Kaf dinsu babu wanda ya samu ya rumtsa kusan dukansu bisa sallaya suka raya daren suna me rokon Allah ya Tashi kafadarta .bama kamar Murad da M.Musa .ba Kai abu kamar wasa har gabbanin asuba Maysam nacin bakar wuya ..kuma likitocin sun tabatar da nakuda take dukda EDD inta saura two week.......

Wajejen hudu na asuba Murad ya saka farar rigarshi ya shiga dayake duk mata ne gyneco din yasa ya fara rena aikin su acewar shi basu san kan aikin su ba ... ....duk ta gala baita idon wanan shine. Shi kam ba karamar firgita yayi ba duk wata nutsuwarshi ya tattaro da sauri ya shiga dubata ..yaga da dan sauranta kafin ta haihun ..yanzuma..kawai yanke shawara yayi da 'a amata cs dan kada a rasasu su duka biyun dan daga ita har babyn su galabaita .......nan ya bada umarnin a kawo mishi form ya saka hannu kuma shida kanshi zeyi mata dan bayason a samu matsala..(ni kuwa nace dama kai da faninka ne ka tsaya sanya seda ta wahala haka🙄)

Maysam ta dan ji ysoro aman jin shine zeyi mata yasa taji sanyi a ranta.....

Su fulani ma sun tsorata bare da sukaji za'a iya rasa su duka biyun dan bata kai haihuwa ba tsokanota ne akayi kuma gashi Murad ne zeyi ba dan suna shanku be iya ba a'a sede ganin yanda ya bi ya damu ya susuce lokaci guda...

Ba' a dau lokaci ba aka shiryata aka shiga dakin operation din ..shi kadene namiji a ciki duk sauran mata ne ..ko Mahmud hanashi shigowa yayi dan tsabar kishin tsiya(kai Murad a rashin lfyr ma seka nuna kishin🙄).......

Ai kam cikin ikon Allah kamar wanda take jira a shiga har an doko alurar kashe zafi ..nakudar ta taso mata kadan2 ..nan Murad ya dakatar dasu . yana dubawa yaga contractions ne Dama shine kusa da ita ai kuwa wata damka tayi mishi tare da yin nishi akai2 cikin yarda Allah sega kan baby nan har yayi rabi aman mi ita kuma a lokaci ta fara lumshe ido karfinta ya qare.........

Cikin ikon Allah Cike da kwarewa Murad ya zaro shi ya doramata bisa cikin ya durkusa yayi sujudu shukur ..dede kuma lokacin aka fara asalatu dan asuba tayi..zagayo wa yayi yabata light kiss...ai kam yana dubawa yaga da namiji ne . ya so ace mace ce da yayi wa sweetbaby takwara to Amman wa ya isa yaja da ikon Allah haka namijin yayi niyyar bashi ..dan haka yashiga yin tasbihi da godiya ga Allah da sauke Maysam lafiya..lokaci guda wata mahaukaciyar kaunar yaron ta shige shi barema daya ga kamarshi daya da sweetbaby lokacin da'aka haifeta ..kaishi walahi seyace ma itace dan in ya leka ma kara lekawa yake wai kode mace ne dan shi gani yake bama kama ba ce ..a'a sweetbabyn ce ma gaba daya..nan ya shiga sakin murmushi tare da dariya kya3..bini2 se ya bata kiss itada baby ..ita abun ma kunya yake bata.. lokitocin ma sakin baki sukayi suna kallonshi ..

Duk wani gyara shiyayi kayanshi daga nurse za suyi se yace ya gode su bari..doctororin kam ikon Allah suke kallon dan su kansu ba wani barin suba yayi ba sukayi aikin su ...abin mamaki baby bashida komi ma'ana yana cikin koshin lafiya duk wani test yayi mishi aman she is very fine dan ..haka ya saka aka kai Maysam dakin hutu tare dayi mata Allurai ciki harda ta bacci shi kuma ya fito da jaririn a hannunshi direct wurin su fulani ya zo yana doka murmushi suma suna ganin shi suka taryoshi ...hum irin rashin ta idon Murad ko fulani yaki ya baiwashi ...wai acewarshi sweetbabyn shi ta dawo kuma babu me amsarta bare ya rabashi da ita ....

Mom tayi murmushi tace hala macece...

Yana kallon yaron yace a'a namiji ne aman walahi kamar shi daya sak da sweetbaby na ..duba ki gani ..se lokacin ya bude misu shi . .ai kam a tare suka dau kabbara da tasbihi ga ubangiji dan gaskiya kamar har ta bace

Murad yace walahi da macece da sweetbaby zanyiwa takwara kuma ma wani ikon Allah kinga rana guda lokaci guda aka haifosu ..dan shima wanan a kiran asalatu ya fado duniya kamar sweetbabyta itama .....gaban .Mom ne ya fadi nan zuciyarta ta kara tsanan ta bugawa har ta kasa hakura tace ka tabbata na mijine kuwa..
Yana murmushi ya bude musu suka gani ..kowa na wurin se barka suke mishi ..fulani ta tambaye ya Maysam din nan ya sanar musu tana dakin hutu..Mufeeda da Mariam baki har kunne se dadi suke ji suma sun zama uwaye wau...ai nan kowa ya fara rigay2 san amsarshi ..

Hum oga kam shafawa idonshi toka yayi keme2 ya ki bawa kowa .
Fulani cikin fada tace kasan baza mu shirya da kai ba inde har haka zakayi ko . haka lokacin da'aka haifi MUNIRA ka hana kowa ganinta bare daukanta ...to wannan karon kam bazan samaka ido ba..

Turo baki yake kamar karamin yaro shi adole anyi mishi fada aman still yaki basu shi...

Mahmud ya lallabashi da kyar dan har an fara kiran sallah asuba ...badan yaso ba ya bawa Fulani shi se waywayen yake ....

Suna dawowa direct ya nufi amsar danshi su fulani kam se kallon ikon Allah suke shi irin kunyar nan ma ta yan fari baya nuna wa....har sha biyu na safe ba'a fito da Maysam ba tana dakin hutu ya hana kowace nose shiga inba shiba ...fulani ganin har sha biyu yasa tace ni Murad ina dauther nane ko zamu iya ganin ta ..

Babu kunya yace Momy ta gaji dayawa fa shiyasa na mata allurar bacci ...kawai inta tashi zan muku magana se ku ganta .

Ai kuwa fulani ta shiga fada ai so ba hauka bane dazaka hanumu shiga ganinta ...

A memakon ya barsu sema yayi kasa da murya yana fadin Momy kiyi a hankali kada ta farka da yake kusa da dakin suke........

Su fulani kam koma gida sukayi dan kimtsa tunda de yaki bari su ganta..

Mahmud ya ce wai ni ya zancen birtday ne ko an fasa ne..

Wata dariya Murad yayi yace wani birtday ai ni yau wife ta cike mun birtday dina tunda ta haifo mun sankacecen yaro ai kuwa kaga birtday ya qare...sede ko na dagashi har ranar sunan yaron ..tunda shima kaga ranar haihuwar mu daya dashi.. Se a hada

Mahmud yace to ya kake ganin za'ayi da waccar azulumar ne...

Dan danan fuskarshi ta sauya ya dena dan murmushi ma dayake yace walahi badan Dady yace na bari ze dau mataki ba da ni kade basan irin hukunci dazanyi mata. .ai ita so tayi ta kashemun mata da babyna to kuwa walahi ina me tabbatar maka dana rasa daya daga cikin su ita ma da ta bisu ...dan hukuci sak na addinin misulinci za'ayi mata. ..yanda ta kashe da gangan to itama jininta ya halasta..

Nan suka ci gaba da hirar su wanda kusan duk akan Maysam ne da babyn

Dad da Mom kuwa tunda suka koma gidan hankalinsu ya kasa kwanciya gaba daya son yaron ya shige su bare da suka ga tsananin kamar shi da sweetbabyn su...dan ita Mom taso ma taga matar Murad din nan data haifi me kama da diyarta ...

Bayan sallar azahar Murad ya shiga dakin da Maysam take da babyn a hannu...aka koyi sa'a ta tashi sede da gani bacin be ishe ta ba...ganin shi yasa ta sakar mishi da murmushi ...

Matsowa yayi ya kwatar mata da babyn kusa da ita .ta kurawa yaron ido .. doko mata brush yayi bayan ta gama ya hado mata tea me kauri tasha dan dama ya tanadi kayanshi a dakin jiran farkawarta kawai yake .wani irin farin ciki su ji su duka sunma kasa furta komi kawai sun zurawa babyn ido .....
Can Murad ya rankafo ya sumbaceta a goshi yace na gode my lovely Maysam kin gama min komi kin haifamin yaro me kama da sweetbaby ..sede ince Allah ya saka miki da mafifici alheri. Allah ya biyaki da aljannarsa ma daukakiya ....

Ita kanta maysam din wani sanyi dadi take ji yana shigarta bare inta ga baby wai fa itama yanzu uwa ce...se kuma hawaye shar2 ya fara zarya a kumatun ta . .

Hankalin Murad ya tashi ya shiga tambayar menene ?ina yake miki ciwo.?duk yabi ya rude .
Shafa fuskarshi tayi da hannuta tace ina kukan rashin mahaifa nane ,?ina tunanin wani irin laifi nayi masu da ta barni ne?a yanda naji wahar haihuwa yanda take bana tsammani ko shege ka haifa zaka iya jefar dashi........

To fa gaba daya kan Murad ya kulle ya shiga duniyar tunani tomi Maysam tke nufi ne.....

Ganin hka yasa Maysam fadin am sorry babyna yau birtday dinka kaga ko happy birtday banyi maka ba...

Kara rankofowa yayi yace wani happy birtday bayan baban happy da kika mun har da gift din dakika bani..

Cike da mamaki take kallonshi tace ni yaushe na baka,..
Chapter 63 · 0% Book details