← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 67

Sashe 23

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🅿️ 49__50
```Manzon Allah (SAW) ya ce''hakika Allah ba ya kallon surorinku da dukiyoyin ku amma sede abinda ya ke kallo shine zukatanku da ayyukanku''
Muslim ya rawaito shi``` .
Da sauri ya kalleta ya ce to tana ina ne?
Fulani tace tana gidanka na Maradi tare da kuyanginta da dogaran ta....
Quoi(what)?ya fada cikin wata irin voice. ...se kuma ya sassauta murya tunawa dayayi da fa Fulani yake magana ya danne bacin ranshi baki na karkarwa yace Momy wanne daga cikin gidan ?
Cike da nutsuwa ta kalle shi tace gidan ka dake unguwar ''sabon gari''wato babba gidanka ba....
Besan lokacin da ya waro ido ba yace haba Momy gidan nan fa na ginashi ne saboda sweetbaby.na ne sega hawaye shar2 kuma ai.....
Kafin ya karasa ta tare shi da fadin wai anya Murad kana cikin hankalin kuwa ?yo inba haka ba taya zaka gina gida akan wacce bata ma doron duniya ...
Rararafo wa yayi ya dora kanshi a cinyarta tare da dora hannushi dede zuciyarshi yace Momy har yanzu zuciya tace ta kasa yarda cewa sweetbaby na ta mutu a kullum gani nake kamar zata dawo gareni ko na ji ma kamar tana kusa dani.....
Fulani ta shafa kanshi tare da goge mishi hawaye tace kaci gaba dayi mata addu'a dan shi take bukata daga gareka bawai ka dorawa laifin wani akan wani ba.......
Bede ce komi ba se ajiar zuciya dayakeyi a jere ...
Can kuma kamar wanda aka ciza ya tashi ya zauna cuwat yace Momy dawama kikace kin bar wacan abar..?
Fulani ta gane sare amma seta mazge tace me wa kenan?
Cike da shagwaba yace ita fa !!
Fulani tana sonyin dariya amma ta danne tace idan baza ka fada min waba abar maganar tunda de ni ba yar modi bace bare nayi arwa......
Kamar zeyi kuka yace Maysam fa nake nufi......
Au wai da ita ....to tare da bayyinta take.........
Ya dan sauya fuska yace ina de fatan dogarai masu tsaron mata aka bata ?
Fulani kam se gimtse dariyar ta take tace ka taba ganin dogarai mata ne?
Yayi dan shiru can yace to wai ma miyasa bata dawo gida hutu ba?
Wanna karon fulani ji tayi kamar ta dokeshi a ranta tace ashe shi ya ma manta da sharadin shi ya bar baiwar Allah da wahala...
Tade daure tace to batayi ta daya ba ta biyu tazo...
Yayi fuskar tunani yace to mi alakar zowanta da ta biyu datayi..?
Fulani tace iii lale fa dole ka tambayya to sharadin daka ginda ya mata ne kan in bata yi ta daya ba to kada tazo hutunnnn..
Shi se yanzu ya tuna ya dan shafa kanshi yace aii hakane ashe........yace Momy bari na dan zaga gari.....
Tayi murmushi tace a dawo lfy .....
Har yakai kofar futa falon ya juyo yace kuma Momy dogarai nawane suke can din....
Fulani danta tsoratashi tace su goma kacal ne ....
Bashiri yace goma fa?
Tace to ko sunyi kadan ne a tura mata wasu?
Zuciya na tafarfasa yace Momy goma ai sunyi yawa ina laifin biyu ko daya ma....
Murmushi kawai tayi ta shige room dinta ganin inta biye mishi seya kashe mata aiki da tambayoyi..
Fita shima yayi rai a jagule se yaji baze ma iya fita yawon ba ....lambu ya tafi wai ko zeji dan sassauci amma ina inya tuna maza goma ke can tare da Maysam se yaji wani zut a zuciyarshi gaba daya ya saka kanshi a damuwa ya kasa sukuni wani bangare na zuciyar yace wai mi kake yi hakane?to wai ina ruwana in maza dari ke tare da ita tundade ba santa kake ba....wata zuciyar ta kitsa mishi ai ba wani damuwa bane kayi da ita kawaide kana kare martabar aurenka ne haka yayi ta saka da warwarar shi ...
Bayan sallar la'asr ya nemi izini ganin me martaba.....
Bayan an bashi izinin shiga ya shiga ya zauna fulani da Madina na kusa dashi sun sakashi tsaka da alama de wata magane ce suke wacce ta shafi shagulgulan gidan...
Bayan ya kwashi gaisuwa sekuma yayi shiru ganin haka Sarki yayi dariya yace da alama de akwai magana a bakin ka yarima MURAD me jiran gado...yayi y'ar dariya
Wannan furuci ba karamin ta dawa Madina hankali yayi ba ta kasa boye kishinta har seda fuskarta ta nuna wanda fulani kade ta lura da hakan bata ce komi ba se girdiza kai da tayi dan inda sabo ta saba.....
Shima yar dariyar yayi tare da dan sosa kai yace dama2 ina son zuwa Maradi ne yanzu se ya sadda kai.......
Me martaba sanin matar shi Maysam nacan ya sa be wani tambaye shi daliliba sede yace baza kayi hakurin gobe ba tunda yamma ta farayi..
Caraf ya ce ai jirgi zanbi ne.
Fulani bata san lokacin data dara ba
Madina kam fadi take kuyi ku gama na dan lokaci ne...kamaci sa'a a jirgi ne da a mota ne da cire maka burki ka mutu kowama ya huta
Sarki be sake cewa komi se addu'ar sauka lfy dayita jero mishi tareda sakon gaisuwa ga Maysam
Nan yayi musu sallama ya fice fulani ma addu'ar tayita mishi ..
Yana zuwa jirginsu ya daga se Maradi ...
.
A bangare Mubeeba kuwa dadi kasheta ne kawai beyi ma amma iya murna da nuna jin dadi tayi shi ..ita a yanzu hartaga ta zama matar yarima me jiran gado .....itada ummarta karansu suke ci ba babbaka waziri ma hankalin shi ya kwanta ganin yar shi ta ji sauki...
Muheeba kuwa tuni ta fara cusa kanta wajen Murad duk da yana korarta tare da yi muta wulankanci amma kamar bada ita yakeba a cewarta ta bashi time ne kan ya shigo hannu .....
.
Biyar da rabi ma acan tayi mishi ..yana sauka motoci suka zo daukarshi daya ke dogaran a sanar da su zuwanshi.direct gidan shi na sabon garin suka sauka...
Tunda suka shigo unguwar gabanshi ya fara fat2 ai suna sshigowa gidan ma gaba daya ya dan rikice da kyar ya seseta kanshi ya fito direct hanyar falon ya nufa ya na zuwa yayi knoking ....
Maysam dake zaune tana shan ace cream ga ta saka Tv gaba ...ga kuma biyu daga cikin kuyangi daya na matsa mata kafa dayar na bata labari me noshadantarwa da saka ban dariya.....
Jin knoking yasa tace waye ne...setaji ba amsa....
Aka sakeyi da har daya daga kuyangi zata bude Maysam tace a'a' bari na bude da kaina...
Da ace cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro ido tayi irin na kaga abun tsoron nan ...tace y..
Ina kaunar ku fans ina jin dadin yanda kuke bibiyar novel din Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa ...ina sonku irin totaly din nan
Muje zuwa
Fasma ce
Ahmed Gumel
Chapter 23 · 0% Book details