← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 99

Sashe 99

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin ikon Allah koda ta karasa d'akin kwance ta sameshi akan doguwar kujera ,ya had'e hannayensa duka yayi pillow dashi idanunsa na kallon celling d'akin, yayi shiru da alamun har lokacin yana cikin jimamin mutuwar yaya akram ne, wanda itama har lokacin bata daina jin rad'adin rasa d'anuwata datayi ba.

tunda tashigo hankalinsa gabadaya ya koma kanta ya kafeta da tsumammun idanunshi yana kallonta cike da tashin hankali dan take zuciyarsa tashiga bugawa tana aiyano masa abubuwa da dama akan shigowarta .

tsayawa tayi tana dubansa kamar yadda yake kallonta, "ya zame mata dole ta karaso garesa tun kafin lokaci ya kure mata ta shiga uku, hakan yasa tacigaba da daga kafafunta ta k'arasa inda yake kwance wanda jin hkn ma bazai ta'ba yaye mata damuwar da fad'uwar gabar da take ciki ba, ahankali taga ya kawar da kansa gefe nan take jikinta ya kama rawa amman duk da hakan da yayi bai hanata isa garesa ba ,tana isa ta tsugunna a gabansa kawai tayi imani yana jin durkusonta amman ko juyowa da kanshi bai yi ya kalleta ba , kara daurewa tayi ta dafa gefen cinyar hannunsa tare da furta "bunayya "meye ki tafi ki kwanta kawai ... ya fad'a batare daya juyo ya kalleta ba dan zuwa lokacin zuciyarsa ta gama tabbatar masa da lafiya take wani abun ne daban ya shigo daita, a take a gurin sauran karfin gwiwar dake zuciyarta ya kare sai dai kawai hawaye taji sun tsiyayo akan kuncinta .
cikin karfin hali tace "bunaya jini.... "

"what ?
ya furta da karfi tare da mikewa zaune "me kika ce?
bata iya sake furta komai ba sai dai kife kanta datayi ajikin kujerar tasa masa kuka..

d'agota yayi tare da girgizata da karfi "ki fad'a min mana me naji kin fad'a yanzu?
"ina magana kinyi min shiru "jini da gaske kike kuwa?
"da gaske jini aiko ya saketa a gigice ,yayi shiru tareda dafe kanshi da hannayensa biyu...

tashi yayi ya fice daga d'akin hakan ba k'araminn tayar mata da hankali yayi ba, ta mike da niyyar binsa amman sai marata ta d'auka, dole tasa ta koma ta durkushe agurin saboda wani azababben ciwo da take ji, sai dai ta damu sosai da rashin ko in kula daya nuna mata , kusan minti goma sannan ta iya dan daddafawa ta mike tsaye amman duk da hk sai taji ta kasa d'aga kafafunta.

dole tasa ta koma ta zauna, zaman ma gagarata yayi sai gata ta zame kasa ta kwanta ita kanta bata san tsayin lokacin data d'auka tana birgima ciwon da tayi wa lakabi da ciwon mutuwa ba,acikin wannan halin taji shigowarsa ya d'auketa.

sam batayi tunanin bud'e idanunata ba saboda ita kanta ba zata iya d'aukar nauyin bud'esu ba, babu abinda bunayya bai yi mata ba, yaga ciwon ya daina haka jinin ya tsaya amman ko saukin ciwon bata daina ji ba..

dole ya d'auke zuwa wani hospital, ita dai tun daga nam bata sake jin komai ba ,sai kara motocin da suke wuce duk da idanuwanta arufe suke hkn bai hanata jiyo hayaniyar tashin muryayin mutane daban daban ba , bata tabbatar da inda take ba sai da taji tsinin allura ya rasa fatar hannunta sannan ta tabbatarwa kanta asibiti ya kawota kwana likitoci sukayi akanta da kyar aka samu jinin ya tsaya ..

********

tana bud'e idanunta babu abinda ya gane sai wani madaidaicin agogon bango dake tsaitin gadonta karfe uku daidai na rana ta gani batasan iya awani ko kwanakin datayi a kwance ba tasan dai tajima a hospital.

babu wanda yazo daga cikin dangi mumy sai ummi dake tare daita,Dan har lokacin haushin abinda aka yiwa al'ameen suke ji ,ganinsu duk yaudararsa akayi , Allah sarki ummi da ita ya zame mata dole itace ke faman zariya akanta , dady shima da abi duk sunzo,sai dai kallon fuskokinsu kadai zai sa ka fahimci suna cikin rad'adin rashin Yaya akram ..

kowa yazo sannu yake mata ita kuwa wani irin kunya ne yake dawainiya daita, shi kuwa uban cikin batasan yaushe rabonta dashi ba dan tun da farka bata sanya shi a cikin idanunta ba har bisa ga wannan lokacin, nan take ta fara tunani ina yake?

"koda fushi yake daita akan laifin da ba nata ba?
sai zuwa yamma can sai gashi yashigo hannunsa rike da lododi ya matso kusa daita sosai yayi mata sannu muryarsa can kasa kasa kmr mai tsoron yin magana .

cikin sanyi murya ta amsa masa "da sauki shiru ne ya biyo baya can ta katse shiru ta hanyar cewa "bunayya kayi hakuri dan Allah da furucina, bai ce mata komai ba ya d'aga kanta ya d'aura saman cinyoyinsa sannan ya sunkuyo ya sun baci kumatunta.

"ki daina bani hakuri dan Allah ,abinda nake so dake kiyi hkr mu rungume cikinmu , ba fa shege bane kamar yadda mukayi tunani tun farko ,a gabanki komai ya faru baa bayan idanunki ba ,ke din mamata ce ta sunnah ,yau ko cikin shege ne ai Kya rungumi kaddaramana dole,bare babu ko daya ..

"Ke da ya kamata ki zaki kara godewa allah lokacin da cikin ya bayyana , na tsaya tsayin daka akan lallai cikina ne , na jajirce akan nawa ne, ida nace bani nayi cikin ba fa yaya zakiji a lokacin ?
"kiyayyaki da cikin nan ko rashin son shi bashi zai sa idan allah yasa rayayye bane yaki zuwa duniya ba. nida muhammed auwal ina sonki da cikina, kuma a shirye nake da cin uban duk Wanda ya shegenta min shi da cewar bamu da aure .......

idan kuma har yanzu baki bukatar rayuwa dani ne idan kin haifa min cikina ki bani abinda kika haifa kowa yakama gabansa dan banga amfani tarayyata dake ba...
akwai mata dayawa da suke bukatata ,nace sai ke ,kinga sai nasamu daidai dani na aura na huta da salo, nayi nisa da rayuwaki dana d'ana watakilla ma bazaki sake sanya mu cikin duniyarki ba..
hawaye suka gangaro mata haka nan yau din nan take jin kaunar abinda ke cikinta ,wannan cikin shi zau kara ninkin soyayyarta a zuciyarta bunnayya, ta sani yana sonta soyaya mai tsanani da wuyar samuwa a wannan lokacin, zuwa yanxu yakamata ta rungume mijinta tinda iyayensu sun tabbatar mata da auren nasu..

cikin sanyi murya tace "shikenan na yarda na amince nima ina son abinda zan haifarmaka, yayi yar dariya tare da lakace mata hanci"abinda zaki haimana dai ni da ke ta d'an rufe idanunwanta alamun kunya, shigowar ummi yasa bunayya ya d'aga kanta dake kan cinyarsa ya d'aura akan pillow ,ya mike yana sosa gefen wuyansa wai shi kunya, wanda ita ya barwa kunya tunda gbdy ta kasa bud'e idanunta, sharewa ummi tayi ta nuna bata ga komai ba , ita dai Allah Allah take ta haife cikin tana jikinta ,ko suna baza'a yi ba ,zata aunasu gidansu suje can su karata , dan ba zata sake barin a sake auno mata wani cikin agidanta ba gara su tafi gidansu suje su karata..
kwanata uku aka sallamota suka dawo gida aka cigaba da karbar gaisuwa ...
******
Mutuwar akram ta doki kowa acikin dangi ,hankalin bunayya yaki kwanciya har lokacin ,zuciyarsa taki sabawa da mutuwa da rashin akram, tausayin rayuwar yaransa yake ji, ko yaya Polina zataji idan labarin mutuwarsa ta risketa?
"shi ba ma wannan ba, yaya zaiyi ya sanarwa iyayensu wannan labarin ?
"sannan yaya zai gano inda polina take ?
Yasan dai ko yaganta da wuya ta basu yaran ,Amman at least dai yasan inda jini yaya akram suke rayuwa ...

D'akin yashiga zagaye daga baya ya soma binciken kayan yaya akram ko zai ci karo da wani abu daya danganci Addresse din polina, Amman bai ga komai ba ahankali idanunsa ya sauka akan wayarsa dake yashe can gefe ya k'arasa ya d'auka yana dudubawa anan yaci karo da numbobinta har guda biyu ,yasoma kira number Kira daya ta d'auka kmr zatayi kuka cikin harshen tsadadden turancinta tace "hello my everything I have been calling your phone for five days, I hope you are doing fine?
runtse idanunsa bunayya yayi sosai, cike da tausayawa sannan yace mata "yana lafiya yayi wata yar karamar tafiya ne ,Amman shi dan'uwansa ne zaizo Spain kwanan nan ,a ina take ya bada sako akawo mata ita da yaranta ?
"tayi shiru da kmr bazata sake yin magana ba ,sai dai taga bai dace ba, tunda gashi da number'sa ya kirata idan bai da halaka dashi akram ba zai bar masa wayarsa ba ,muryarta a sanyaye tace "ya sunanta acikin 'yan'nuwansa ?
Kundinbala yayi yace "Muhammed Auwal aiko ta sauke naunayen ajiyar zuciya tace "bunyaya ...?

Da acikin faricikin yake tabbas da sai ya dara saboda yadda ta kira sunansa Amman sai ya ciza lips dinsa kawai yace "right that's my second name ,Dan haka tayi murmushin ta bashi full details dinta, ajiyar zuciya ya sauke sannan yashiga tambayarta yaranta da ainihin sunan da mahaifinsu yake kiransu dashi, nan ta sake sakankace tare da amincewa da lallai d'anuwan akram ne kuma na jini ..

*Sauran page 2 labarin muwa ya kare , muwaddat zai yi ending a 46 ,so kuyi min hakuri da page 44 , banason ganin complete muwaddat a waje yana yawo ,dan girman Allah kumin hakuri saboda nasan wasu daga cikinku zasuji babu Dadi aransu,Nima ba haka naso ba,sai dai Ina da dalilina nayin haka*

Mmn sudais ce
Chapter 99 · 0% Book details