← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 99

Sashe 40

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya fiddo wayarsa da niyyar zai kirata sai kuma ya tuna bashi da number ta ,yayi tsaki ya maida wayar aljihunnsa hisham ya dube sa yace "Anya manage babu wani abu tsakaninka da yarinyar nan?
Ala'meen ya Dan hararesa yace ",me kagani ?
"Ni Kan haka nan naji zuciyata na zargin akwai wani abu koma ince akwai soyayya mai karfi tsakaninku "kai rufa min asiri ai wannan ba irin tamu bace "saboda me kace haka ala'meen byn akwai zumunci mai karfi tsakaninmu ?
"nasan babu yadda za'a yi ka furtawa iyayenta kana sonta suki baka ,sannan ka daina ganin tafi larfinka..

Ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske "duk ba haka bane yarinyar ce yar shagwa'ba kai kanka kasan bana shiri da yan shagwa'ba ya fad'i hk yana waskewa ,zuciyarsa na dokawa ,domin a yanzu ma dayake maganarta wasu wurare a kirjinsa sake bud'ewa sukayi soyayyarta na kara nikaya aciki .

Hisham yace "Amman ni kuwa yarinyar batayi min kalar shagwababbiya ba..
"Eh to wani lokacin ni kaina ina mamakin yadda take magana a natse Amman shagababbiya ce gurin daka ganta ,iyayen goyonta sun sangartata ainun kar mutun yaje yasaka kansa cikin tasko."ai kuma ba daga nan take ba bakowa gata yake lalatawa ba ,akwai wasu ya'yan gatan da zaka gansu da tarbiya da kamun kai idan dai kana sonta na bada goyon baya dari bisa dari Dan gaskiya yarinyar tayi da kace aurena bai Jima ba Dana k'ara ta biyu daita idan kai baka da ra'ayinta ..

"Dan iska to yaya zakayi da minal ?
"Yaya kuwa zanyi daita Karka fa manta nmj nake inda daidai da auren mata hudu "to kuma duk Dubin matan dake garin nan basu yi maka ba sai bakuwar gidanmu ,hisham cikin dariya yace" ita naga ta min kasan nafi son auren yayan Hutu shiyasa nake sha'awar in tara matan Hutu agidana nayi ta hutawa dasu "to kuwa kwalelenka anan ,wannan tafi karfinka "ta yaya kake tunanin tafi karfina? Ince abun ba kokuwa bane ya k'arasa mgnr yana kwashewa da dariya "
alameen yace "ka hakura kawai Dan ba baka zamuyi ba "idan Baku bani ita ba zaku jikata ku sha ne ?
"No no saurayi dai zamu bawa danye sharab Wanda ba'a cirewa yanar kaciya ba domin yarinyar bata dace da auren nmj mai mata ba "

Hisham yayita dariya har da rike ciki "kai nafa San inda zamceka ya dosa Amman kake son yin wani kwana kwana kai kace min hasashena gaskiya ne ...
Wallahi duk wani kauksucenka Nasan kana son yarinyar nan so kuma mai girma ,tun zuwana gidan na nasan za'a rina, a duk ruwan idonka da wuya ace baka sota ba ,ba zanga laifinka ba domin kuwa yarinyar akwai ruwan kyau Amman karka manta kmr a kunnen latifa domin ni zan fara bata labari za'a yi yar gida cikin murmushi alameen yace "sai kabari dai sai na fad'a da bakina sai kaje ka sanar mata dayake mamatace "to meye maraban dambe da fad'a ?
Alamen yace" zage zage sukayi dariya hisham yace "tunda uwar lafita ta rigada tace Tabaka ai tamkar tazama matarka ce fatiha ce kawai da za'a shafa ba .
Alameen yace " kai ni rabani da zanceta ba ita nakeyi ba yanzu " sai ta muwaddat ba ,ai nasan za'a rina tunda kai ba mutumin kirki bane.."ni wallahi tausayi yarinyar take bani itama hjy mantawa tayi da halinka shiyasa ta nanika maka yarinyar ..
Suna ta hira har suka iso gidan suna shiga parlour'n suka iskesu suna hira ,muwaddat kishigid'e Akan kujera kanta ko d'ankwali babu ana iya karewa dogon gashinta kallo Wanda ya sha gyara yagaji ,sai kyalli yake,da alamar hirar tayi mata dadi domin hankalinta baya kan komai sai tautaunawar da suke ita da minal Dan haka bata lura da shigowarsu ba sai da hisham yayi magana tana waigowa taga duk ita suke kallo ..

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......wannan shine.

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 17

....da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zamanta ,basu daina kallonta ba hakan ya ankarar daita a she fa kanta babu d'ankwali sai lokacin tayi hanzarin d'auka ta d"aura gaskiya irin gyaran da muwaddat takewa gashinta ba namiji ba hatta mace 'yaruwarta zai iya burgeta bare nmj .

Hisham ya d'an juyo ya kalli abokinsa ya lura shima ita yake kallo minal ce ta katsesu ta hanyar yi musu sannu da zuwa sai da kowa ya zauna sannan muwaddat ma tayi musu sannu al'ameen ya amsa idanunsa akanta yace "yau dai kun sha hira ,tun sanda suka shigo muwaddat bata sake yin magana ba saboda tsarguwa datayi da irin kallon da al'ameen ke binta dashi haka minal ta fahimci muwaddat batason yin magana agaban al'ameen da tunda suka shigo ta kasa sakewa hisham ne ma yake d'an janta da magana amman Sam taki saka bakinta acikin surutun da suke .

Al'ameen ya Mike da kanshi ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko lemo mai sanyi ya zauna yana sha, sai da ya gama sannan ya sake dubanta "mu tafi ko kar muyi dare ,batayi magana ba sai kawai mikewa datayi ta lalubi Jakarta ta rataya minal ta dubi al'ameen "gaskiya banso dawowarku da wuri ba domin hirar da muke bamu gama ba "to ko zama zanyi ku karasa ?

"Kai ma kasan bakuwa bazata iya sakewa a gabanku ba ,gashi daga shigowarku ta d'auke wuta ko magana bata iya yi ..

Muwaddat dai gaba tayi abunta har gaban mota suka yi musu rakiya minal tayita rokon muwaddat akan ta dinga zuwar mata hira muwaddat tace "bazan iya miki alkwari ba amman idan nasamu lokacin da kuma mai kawoni zan dinga zuwa ...

Hisham ya d'an kalli inda Al'ameen yake yana.dariya domin jin abinda muwaddat tace shi kuwa al'ameen shiru yayi kmr bai ji ba d'an Jan ajinta yasoma bashi haushi ya bud'e mota yashiga ya juyo ya d'n zubawa muwaddat ido domin yaga inda zata shiga amman sai yaga hisham yana k'ok'arin bud'e mata gidan gaba shiru yayi bai yi magana ba sai data shiga ta zauna sukayi sallama dasu minal har ya tadda motar sun fara tafiya sannan yace "na d'auka direban zaki sake meidani irin na d'azu"haba dai ta yaya zan maida kai diteba"eh mana gashi nan da zamu zo kin wani kwanta abaya ina janki tayi shiru ,da yaga bazata yi mishi magana ba sai cewa yayi "halan nayi miki kama da direbanki ne da d'azu ki wani rashi rashi abaya ?

"Ba kayi kama ba, tabashi amsa a agajerce dayake bata fiyye son doguwar magana kamarsa ba ,sukayi shiru gabad'aya can kuma ya sake janta da wata hirar da alamun muryata yake son ji, kallonta yayi tare da cewa "amman fa nayi mamakin yadda kuka dade kuna hira da minal musamman yadda kike ba ma'abociyar son magana ba ,"kasan ita magana zuwa take bawai ayita zuba kmr ruwa ba yace "ko ?
"Tace kwarai kuwa tun daga nan basu sake magana ba har suka iso wani katafarin mail na sai da kayan makulashe yayi parking din motarsa acikin harabar wajen sai daya bud"e ya fito kana ya zagaya ya bud'e mata yace "bismillah fito mu shiga ko, ta d'an yatsina fuska kmr kar ta fito sai kuma taga hakan bai dace ba ko babu komai d'an'uwanta ne yakamata ta nuna kulawarta.

ta fito tana yatsina fuska saboda kai tsaye gida taso taje ta kira bunayya dan tun safe take expecting kiransa amman ko miss call dinsa bata gani ba .
Duk yadda taki son jerawa dashi sai daya saita kafad'unsu suka jera suka nufi kofar shiga mail din suna gota wasu matasa da suke tsaye kusa da kofar shiga mail din ,dayan ya zunguri sauran da suke tare yana yi musu nuni da muwaddat.

"kai kai kai had'uwa ji wata hadaddiyar zalziyya suka kalleta gabad'aya, dayan yace "gaskiya da ba dan wancan gayen da suke tare ba, da sai na d'an latsa ko zan yi sa'ar ta sairareni ,daya daga cikinsu yace "kai tafi can kana ganin yarinya wata muguwar yar hutu amman har kake zaton zata iya sauraronka ..

"Ai ba'a anan take ba ,su irin wad'an nan yammata da suke furgitamu in akayi sa'a sunfi saukin kai in Allah ya doraka akansu ,babu wuya sai kaga kun daidaita "kai dan Allah karya ne ba dai irin wannan kalar ba wannan ko acikin yayan talakawa ta fito bazata saurareka ba bare kana ganinta kaga masu gidan Rana kaga mace na takun kasaita, ko gwal din dake wuyanta ya isa ya sayi motarka .

Suka kyalkyale da dariya yayinda duk maganar nan da sukeyi acikin kunnen al'ameen amman baya zaton muwaddat taji su ,saboda ita tarigashi shiga ciki, da sauri ya k'arasa ya sameta suka jera tare "ki shiga ciki sosai ki duba abinda kike bukata kai kawai ta gyada masa sannan ta fara zagayawa tana bada baya, wasu samari suka shiga dubanta suna magana kasa kasa "kai Anwar dubi yarinyar dake gabanka kaga wata halitta da kyan diri mai d'aukar hankali ,cikin hanzari wanda aka kira da Anwar ya d'aga kai yana duban muwaddat" kai gsky cikar nan ta hadu da yawa Allah yayi halitta a wannan guri ,ina ma ina ma ..saif yace ina ma me ?

"Ina ma yarinta ce gsky Dana more rayuwar duniya ",to ai yanzu baka makara ba kana iya latsawa ,ko zan maka sallama daita ne
ai baasan inda rana zata fadi ba?
" ,lallai kuwa ka kawo shawara dan gaskiya ina sonta ,ya kake ganin zamu bullowa abun .

Jira zamuyi sai tagama tsiyayarta ta kai idan za'a yi mata bill sai kayi sauri ka biya mata,kaga daga nan nasan zata maka godiya kaga mu km mun samu hanyar gaisawa daita ko ba haka ba ?
Chapter 40 · 0% Book details