← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 99

Sashe 69

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kan gado ta fad'a tana mai runtse idanunta saboda azabar zafi , dauriya kawai tayi ta tsaya bisa kafafunta agaban ummi dan kawai ta kawar da zargin ummi akanta, dan tasan muddin bata daidaita yanayinta ba, ba k'aramin aikin ummi bane tayi asibiti daita domin duba lafiyarta ,
kafafunta ta mike ahankali kana ta janyo wayarta domin kiran 'yan gidansu, dan tunda ta shigo gidan batayi tunanin nemansu ba ,sai yanzu da taji abinda ummi tace , bayan mumy ta d'auki wayar suka gaisa tayi mata ya gajiyar hanya had'e da cewa "ai tun d'azu nake neman layinki ban samu ba"
muwaddat ta numfasa kana tace "wallahi mumy wayar ce a kashe tun bayan da muka dawo .
bayan sun gama gaisawa da mumy ,ta mikawa kanneta waya ,haka suka yita gaisawa d'aya bayan d'aya , eiman ce ta amshi wayar daga karshe tace "big sister ......,ina nan nayi tabaje, babu matsi balle takura ,sai dai duk da haka nayi kewarki sosai ,amman dan Allah next time idan zaki sake zuwa mana hutu ,dan girman Allah karku zo tare da yaya bunayya ,wallahi ya cika matsi da takura mutane, ga shegen miskilancin tsiya ,har ma gara naki miskilanci akan......
"ke dan Allah malama ban son shirme.... ta katseta ta hanyar fad'ar hk, ni da kike Allah Allah mu rabu, shine yanxu dan gulma da munafurci zaki ce wai kinyi kewata "kai aunty muwaddat kefa matsalata dake kenan har yanzu bakije Ghana ba,da wasa fa nake miki "ai kuwa bazan ta'ba zuwa ba ,kinga sai anjima ta katse kiran ....

tun bayan da muwaddat ta gama waya da yan gidansu ta tsakuri abincin da baba mairo ta kawo mata sama sama ,tayi kwanciyarta a d'aki har dare taki fitowa sai nan mairo mai aiki ta sake biyota da abinci .

bangaren bunayya kuwa bai sake shigowa d'akin ba, dan haka ta samu damar sakewa sosai ,tana tunanin abinda ya dace da rayuwarta ,domin nemawar kanta mafuta dangane da halakarta da bunayya ,dan kasancewarsu tare guri daya ,babu abinda zai sake haifarwa facce dagula mata lisafi,tare da d'aga mata hankali ,haka dai tayita juyi akan gadonta tana tunani , har lokacin hoton abinda ya faru tsakaninsu yaki 'bace wa acikin kwalkwaluwarta ,sai da lokacin sallah magrib tayi sannan ta yunkura ta Mike ta sake shiga bayi ..

************

washegari tana zaune a inda ta idar da sallar azahar yashigo ,ko ba'a fad'a mata ba tasan shine yashigo d'akin, juyowa tayi a sukwane suka yi 4 eyes dashi, tsaye sanye ciki wasu had'd'un bakaken kanana kaya ,riga t shirt da wandon baki iya gwiwa, idanu suka tsurawa junansu tamkar ranar suka fara ganin juna , take zuciyoyinsu ya sake dilmiya cikin tafkin kaunar juna , hk nan ta tsinci kanta cikin sabon tafkin kaunarsa shima kusan yana jin irin abinda take ji ajikinta ,sosai tayi nisa cikin kallonsa, laulausar tafin hannunsa da taji akan kafad'arta ne yasa ya dawo daita daga duniyar data Lula, kusa daita ya matso sosai yana kallon fuskarta, lumshe idanunta tayi ahankali saboda bazata iya jurar kallonsa ba ,kusan minti goma yana durkushe a gabanta yana kallon fuskarta, cike da matsanancin so ya kira sunanta cikin sanyayiyar muryarsa mai shiga jiki " "muwaddat dina ...
Tana jinsa taki motsawa ya kamo hannuta ya Mikar daita tsaye ,ba tayi masa mutsu ba ta Mike ya soma tafiya daita har suka k'araso bakin gado ya zaunar daita, d'an k'aramin ajiyar zuciya ta sauke tana bud'e shanyayyun idanunta ahankali while zuciyarta na dokawa ,idanunta ta lumshe tare da bud'e su fess akan fuskarsa , suka sake had'a ido ,take suka shiga wani yanayi Wanda hkn yasa suka tsurawa kwayar idanunsu ido suna kallon juna, gabad'aya ya gama karantartar halin da take ciki, har lokacin tana cikin tsananin tsoro da fargaba ne.
Haka nan shima ya tsinci kanshi cikin damuwa sosai saboda yanayin da take ciki "muwaddat dina.....ya sake kiran sunanta
ta sake kallonsa tana kawar da idanunta batare data amsa ba ,ya kamo fuskarta da hannuwansa duka ya had'e fuskokinsu guri daya tare da sanya kwayar idanunsa cikin nata yana kallonta, har bai son d'auke idanunsa cikin nata "am really sorry my muwaddat i really sorry for what I did .... bazan gaji da baki hakuri akan abinda ya faru a tsakaninmu ba .

ta sake kawar da kanta gefe idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "kiyi hkr ki daina kukan nan, sannan kice kin hakura plz shine kawai kwanciyar hankalina....

muryarta na rawa tace "ba..babu komai ya wuce , had'e da sake kawar da fuskarta ta sunkuyar da kanta kasa, "to me ye kuma abun sunkuyar da kai bayan kince babu komai ,dan Allah ki saki jikinki kinji aunty nah.......
ta d'ago da sauri tana dubansa cike da matsanancin mamaki ,sbd wannan shine karo na farko daya furta hk gareta ,wani irin kallon yake mata kai tsaye batare daya sake ce mata komai ba ,babu zato taji ya janyota tare da sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam yana furzar da numfashi, yana jin kmr su tabbata a haka ,ahankali ta soma k'okarin fixge jikinta ,amman ta kasa sbd irin kalar rungumar da yayi mata ,babu yadda zatayi ta raba jikinta dana shi, tsawon minti goma suna haka suna sauke numfashi ,tana cigaba da mutsu mutsun raba jikinta dana shi,saboda yanzu wani irin mahaukacin tsoronsa take ji ,dan ya shata mamakinsa da bazata ta'ba mancewa ba har karshen rayuwarta .....
cigaba da mutsu mutsu tayi wanda hkn yasa ya barta ba dan yaso ba .

saukowa yayi gabadaya daga saman gadon ya tsaya bisa kafafunsa "ni zan koma d'akina ki saki jikinki plz ,babu abinda zai faru sannan rashin kusantar inda ummi take zai sa tashiga damuwa sosai, ko yanxu da zan shigo naji suna maganar da abi ,wai tunda muka dawo ta rasa gane kanki ko parlour'n baki sake fitowa ba ,ki taimakeni ki saki ranki da zuciyarki plz karki bari ta fahimci komai ya fad'i hk yana had'e hannuwansa guri daya, shiru tayi tare da kafe shi da idanunta..

gbdy ta rasa ma abinda zatace masa ..
"dan Allah nace "muyarta sanyaye tace "naji amman kai ma zan roki wata alfarma agurinka, ka daina shigo min d'aki kai tsaye ,ko nuna ka damu dani akan idanunsu ,kai bama hk ba, ni.. ni. na yanke duk wata halakata da kai har karshen rayuwata , ka tsaya matsayinka na tsaya nawa, banason kusancina da kai ......

"shine kawai alfamar ?
Ta d'aga masa kai "shikenan angama yana gama fad'ar haka ya juya yasoma k'ok'arin barin d'akin tana kallonsa ya fice zucuyarta na wani irin harbawa ...

***********
bayan sati biyu da faruwar hk atsakaninsu, muwaddah ta warke sumul ta dawo normal saboda idanun ummi dake kanta amman sam bata cikin kuzari da walwalarta,tare da farinciki tmkr yadda take ada , tana dai fitowa ayi hirar barkwanci daita da sauransu kmr dai yadda suka saba dan duk kar ummi ta fahimci tana tare da damuwa, cikin satin ta koma makaranta.

shi kuwa bunayya ya d'auke mata wuta kmr yadda ta bukata, ya daina shiga tsabgata da shishige mata, ya daina nuna kulawarsa gareta tsakaninsa daita ido ne ,wannan sharewar da ummi ta fahimci suna yiwa juna yayiwa mata , sannan hankalinta ya kwanta tare da d'aukar ko ya watsar da kudirinsa akanta ne akan muwaddah ,bunayya kuwa hakurinsa ya gaza yasoma bibiyar d'akinta cikin dare ,kullun sai sun sha dambe bala'i dashi akan sai ya kusanceta, ko kuma ta fito ta sanarwa iyayensu, cewar itama tana son shi, ta nuna musu tana bukatashi ,bashi kad'ai yake bukatarta ba.

*********

zaune take a gefen gado ta rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta, abu daya tasani har lokacin tana jinsa ajikinta, musamman yanzu datake sake hango tsananin soyayyarta acikin kwayar idanunsa,sai dai duk wannan bai sa ta amincewa zuciyarta ba, zata rusa soyayyar zuwa kiyaya tunda iyayen goyonta basu bukatar wata halaka atsakaninsu,, ta koma ta kwanta lamo tana sauke numfashi sama sama, har bacci barowa yasoma fixgarta.
Chapter 69 · 0% Book details