← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 99

Sashe 88

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"lallai yaran zamanin yanzu sai dai abarsu kawai ......
har lokacin abi ya kasa cire mamakin wannan a'lamarin acikin zuciyarsa ,wai muhammed auwal d'ansa d'an shekara 22 ne yayi muwaddat ciki, to a ina akayi wannan cikin....... ?
kwalkwaluwarsa tashiga caji da tunanin inda akayi ciki suna cikin gidan batare da sun sani ba.

Bunayya ya mike tsaye ahankali ya isa gaban ummi ya durkusa bisa gwiwowinsa yace "dan Allah ummi karkice zaki cire cikin nan wallahil azim ciki na ne ajikin muwaddat, kuma ina son kayana .....
tassss !tasssss!! tassss!!! Kake jin ta d'auke shi da wasu gigitattun maruka har guda uku ajere tana haki "ka min Shiru .... d'an iskan yaro mara d'a'a idan ka sake furta wannan kalmar agabana sai na tsi....

" kul...... ....abi yayi saurin katseta ta hanyar fad'ar haka , "baki ta'ba masa mummunar furuci ba a tsawon rayuwarsa kin dai ga abinda ya faru yanzu .....

"baki ta'ba furta wata kalmar banza garesa ba kinga aika aikan da ya aikatamana , hakuri zamu taru muyi gabad'aya tunda haka kaddarar tazo mana, amman batu na tsinewa ko zagi duk bai taso ba.
"Irin abinda nake hangowa kennan agareki mukarama kika mutsutsuke idanunki kika biyewa son zuciyarki yanzu wa gari ya waya ?
"Tabbass idan bunayya na da laifi namu laifin ya zarta nasa "
"Yaran nan suna son junansu sosai fiyye da tunaninki ,amman kika ce Sam ba haka muwaddat bata son shi yanzu ai Kinga karshen kiyayya tun da ga sakamakon nan ta haifar ,tun tuni na zubda makaman yakina akan lamarin sabida ba'a jayayya akan irin wannan lamari 'a'a bunayya yaro ne bazan bashi diyata ba this and that ya k'arasa maganar yana furzar da iska tare da buga abun kujera yana zabgawa bunayya wani irin mugun kallo .....

Bunayya wanda idanunsa suka rikid'e sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki ya mike ya nufi gurin abi ,"abi kayi hakuri dan Allah karka karawa ummina damuwa akan wanda take ciki "yi min shiru wa ya jawo ?
"Ai suk wanda ya sai rariya yasan zatayi zuba "Kai Kuma da yake ..sai yayi kawai yana sake furzar da iska mai zafi ...

"Kuyi hakuri amnan tun tasowata nake son muwaddat Kuma da aure ,na cire kawaici da kunyarku amatsayinku na iyayena na bayyana muku abinda ke raina da burina amman kuka ki ,ni dai dan girman Allah ku bar min ci.....

Wani sabon mari yaji daga bayansa wanda yasa take ya had'iye abinda zai furta "shine akace ka mata ciki dan iska ?
"Nasani muwaddat ba zata ta'ba aikata hakan ba wallahi sai dai idan tursasa kayi .
"kayi Mata dole dan kawai kaga karshena ko bunayya ?

" Nasan kayi haka ne dan ka kuntata min amman sai numfashinta ya d'auke sakamakon hakin d'aya rufeta tayi kasa luuuuuuu zata Fad'i, bunayya yayi saurin tarota jikinsa Yana jijigata ,take hankalin abi da muwaddat ya sake tashi suka yo kanta atare suna Kiran sunanta muwaddat na kuka ta durkusa kusa da ummi ta kamo hannuta hawaye na bin kuncinta ...

"ummi..!ummin....!!"ya rabbi dan girman Allah ummi karki mutu ki barmu a duniyar Nan ,idan wani Abu ya sameki a dalilin abinda na aikata bazan ta'ba ya fewa kaina ........
Abi yasoma k'ok'arin amsarta daga hannunsa amman furrrrrr bunayya yaki sai Kiran sunanta yake cikin tsananin tashin hankalin .

Cike da matsanancin tashin hankali abi yace "wa. water ..... wani irin zabura muwaddat tayi ta nufi hanyar inda firdge din abi yake, ta bud'e ta d'auko ruwa mai tsanyi tun kafin ta k'araso ta soma k'ok'arin bud'e robar ruwan tana gama k'arasowa ta shiga tsiyayawa ummi tana wani irin kuka ..

gabad'aya sun gigice sun rud'e sun fita haiyacinsu kallo d'aya zakayi musu kasan cewa suna cikin tsananin damuwa , duniya da abinda ke cikinta sun taro sun cakud'e musu guri d'aya , barin muwaddat da ke jin rayuwata ita da babu duk d'aya ,addua kawai take a halin da take ciki Allah ya d'auki ranta a lokacin ta huta ,da kyar numfashin ummi ya dawo gangar jikinta.

tayi atishawa tare da sauke naunayen ajiyar zuciya Jikinta na wani irin rawa take suka shiga rigerigen yi mata sannu suna sauke numfashi "sorry ummina dan Allah karki tsine min bisa kuskurena ......

ummi ta bud'e idanuwanta da kyar hawaye na tsiyaya daga kwarnin idunta tashiga kallonsu d'aya bayan d'aya tana girgiza Kai kana ta runtse idanunta gam tana jin yadda dukkanin su ke jero mata sannu amman banda bakinciki babu abinda ke dawainiya daita da zuciyarta "me zatayi da wani sunnunsu "an rigada an cuceta an cuci rayuwar diyarta.. bunayya take kallo ta kawar da kanta tana hawaye su bunayya da muwaddat suma kuka suke har wannan lokacin .

Ahanksli bakinta ya shiga motsi al'amun tana son yin magana tana salati ..
hakan ya sake gigitasu suka sake matsowa gareta , abi da bunayya suka yi saurin kasa kunnuwansu daidai bakinta dan jin abinda zata farta .......sai Kuma tayi shiru .

Yayinda da komai nata yayi sanyi ,lokacin ne muwaddat ta tsilla ihu a hankali bunayya ya sake kafe ummi da idanunwansa ,yaga idanun ummi sun sake rufewa haka nan bata motsi bare numfashi ,cikin hanzari bunayya ya tashi da sauri Yana duban ummi dake Kwance ,can Kuma ya koma Jikinta ya rungumeta yayinda Kansa ke kan kirjinta abi da muwaddat tuni kuka ya gama cin karfinta .....

Cikin lokacin kankani bunayya ya burkice Yana shafa fuskar ummi yana magana "ummina duniyata hakika bani da tamkarki ,bani da mai Sona kamarki karki min haka ummi karki had'iye zuciya ki tafi ki barni ....ki taimaki tilon d'anki bashi da kowa daga Allah sai ke ,karki min haka ..

"Abi kace ta tashi wallahi na hakura da cikin ...,a ciresa matukar ummina zata samu kwanciyar hankali ,wallahi a zim na hakura ,"ya sake kamkameta "ummi ..!ummi !!!wallahi na hakura ki tashi "Ina son ki ummina fiyye da abi ,da muwaddat duk duniya kace mutun ta farko da nake kauna .......

*Manage plz idona kaina, Kai koina ma ciwo yake min😭😭😭😭😭😭 Ina fatan zaku min addua*

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 38

.....cikin wani irin birgicewa da matsanancin tashin hankalin bunayya ya soma magana cikin sambatu "abi tashi ...taimaka ....
Ka taimakawa rayuwata abi, mu kai ummi hospital ,abi bana son na rasa ummi nah ,wallahi Ina sonta bana son na rasata ,kuskure ne abinda nayi bazan sake ba ,wallahi nayi nadama jikinsa na kyarma yake wannan sambatun "ummi ki tashi dan Allah karki min haka ...
"Karki tafi ki bar muhammed auwal dinki ...
"Idan kika tafi duniya zata masa zafi .....
"Hakika ummi baki cancacin haka daga garemu ba ..

Abi dake rike da hannun ummi gam cikin nasa jikinsa ya sake d'aukar wani kyarma yana zubda hawaye masu ciwo da rad'ad'i ... .....

Hawayen da yasan sunfi kowani hawaye ciwo da rad'ad'i arayuwarsa
,domin kuwa zuwa lokacin ya rigada ya gama sadaukarwa kansa cewar ummi ta rigasu gidan gasky ,dan haka ahankali bakinsa ke furta kalmar" Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un ...
"Shikenan mukarama kin tafi kin barni .......

Jin haka yasa hankalin bunayya da muwaddat sake kololuwar tashi, a matukar firgice bunayya ke bin abi da wani irin kallo 'kwal'kwaluwasa na juyawa ....
can ya zabura ya mike tsaye ya soma magana cikin d'aga murya "abi me kake cewa haka ?
"Kana nufin ummin tawa ce ta rasu ko me ?
"Impostible abi, ka..ka daina furta haka ga ummi nah " "ta Yaya ummi nah zata mutu yanzu?

"Ummi ba zata mutu yanzu ba ,lokacin mutuwar ummi nah bai yi ba ,kwata kwata ma babu mutuwa acikin idanuwanta,idan ba zaka taimakamin mu kaita hospital bane kawai nasani ...."Ni..ni sai na kaita .........
ya k'arashe maganar yana k'ok'arin kwace ummi daga hannun abi ..

Yayinda muwaddat ta kasa motsi daga inda take ,ta dawo tamkar mutun mutumin a durkushe tana duban gangar jikin ummi da bai motsi ,koda bata san mutuwa ba tasan tabbasss ummi ta tafi........

Wani irin fad'uwa gabanta yayi da mugun karfi, take wani Abu ya tsarka mata tun daga kirjinta zuwa kasan mararta ....
Cike da tashin hankali bunayya yasoma k'ok'arin ciccibar gangar jikin ummi hawayensa na diga bisa fuskarta, abi yayi karfin halin tallafota jikinsa , shima hawaye yake, hakika wannan abu da ciwo yake ,yasan mutuwa tana kan kowani bawa da yayi eimani da Allah ,amman sam bai ta'ba expecting mukaramarsa zata tafi ta barshi a daidai wannan lokacin ba, ban da kalmar Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un babu abinda yake furtawa har suka fito daga bangaren abi ,nan ne fa binta mai aiki ta fahimci akwai damuwar dake faruwa acikin gidan ganin abi da bunayya suna tara tara da ummi .
Jikinta na rawa ta k'arasa garesu tana tambayarsu "lafiya alhaji meke faruwa da hjy ?
"Me ke damunta ?
Daga abi har bunayya babu Wanda yayi k'ok'arin bata amsa, illa k'ok'arin nufar hanyar fita da suke cikin tsananin tashin hankali..

Ita kuwa muwaddat da kyar ta soma k'ok'arin Mikewa tsaye bisa kafafunta ,ai ko gama Mikewa batayi ba, tayi kasa luuuuuu tare da sakin wata razananniyar k'ara ta fad'i kasa sumammiya wannan k'arar data yi ne yayi sanadiyar da binta ta nufi hanyar parlour'n cikin matsanancin tashin hankalin tana zuwa ta risketa cikin matsanancin hali take jikinta na rawa tana sallalami ta janyo sauran ruwan da aka yiwa ummi amfani dashi tashiga tsiyaya mata tana Kiran sunanta ....
Chapter 88 · 0% Book details