← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 99

Sashe 49

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

soyayyar kuruciya mafi yawa matasa na tsintar kansu ciki wannan shaukin mai wuyar misaltuwa Wanda da wuya akai ga cimma burinta,
Dan haka ya ajiye maganarsa amatsayin yarinta da kuruciya ne kawai ke dawainiyya da d'an nasa ,bancin hk ta yaya kamar bunayya zai ce ayi masa aure a wannan lokacin
"auren ma da wace ta girmesa?
tattara zance yayi ya ajiyesa amazaunin wasan yara da kuruciya , ya cigaba da abinda ke gabansa .

Shi kuwa bunayya Ko daya dawo d'akinsa ya kasa samun sukuni, gabad'aya ya rasa abinda ke damunsa, zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, sai zariya yake acikin d'akin rike da kugunsa yayinda hannusa daya ke dafe da goshinsa ,gabad'aya hankalinsa baya gangar jikinsa, 'kwa'kwaluwarsa ke hasko masa wai ga muwaddat dinsa can tare da ala'meen tana masa murmushin nan nata da yafi so da kauna akan komai acikin duniyar nan ,take wani zazzafan kishi ya turnuke zuciyarsa dama gangar jikinsa, ahankali ya runtse idanunsa yana girgiza kai, kirjinsa na wani irin dokawa da sauri " Impossible ya furta a bayyane had'e da bud'e idanunsa ya cigaba da zagaye d'akin ..

"Anya kuwa zan iya d'aukar lokaci batare da na kai kaina gareta ba ?
Anya ba wani abu al'amen yake nufi dashi ba ?
"to wai ma me taje yi d'akinsa a daidai wannan lokacin?
"Ko ba'a gaya masa ba yasan ala'meen son muwaddat dinsa yake, tun da shi ba makaho bane ,dan idanuwansa sun fara hango masa mugun nufinsa akanta ..
Abinda yakamata kawai kaje ka d'aukota ka dawo daita gida shine kawai besty solution da kwanciyar hankalinka gareka ,zuciyarsa ta umarcesa da fad'ar Hakan ,take kuwa ya amince da shawarar zuciyarsa ,ya kudirci aniyar ko bai je gobe ba kamar yadda ya furta mata ba, to kuwa cikin satin sai ya dangana da ilori ,duk ma abinda zai faru sai dai ya faru amman sai ya d'auko abarsa kafarta kafarsa ya k'arasa maganar yana
fad'awa Kan makeken gadonsa da karfi ya kwanta ruf da ciki , yana furzar da iska mai zafi had'e da shafa sumar kansa ,sannan ya kai hannunsa ya janyo wayarsa shiru yayi sakamakon ganin har lokacin wayar tana kan layi ba'a tsinketa ba.

ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana duban screen din wayar sannan ya kai wayar kunnensa ,sautin muryar kukanta ya jiyo can kasa tamkar ta baby yana shiga cikin dodon kunnenshi, zuciyarsa ta cigaba da bugawar da take da karfin gaske, wani irin rad'ad'i ya dinga jin yana sauka akan tsokar dake makale da kirjinsa , runtse idanunsa yayi sosai had'e da Jan dogon tsaki sannan ya katse kiran gabadaya ya Mike ya shiga bathroom...

Muwaddat kuwa har lokacin tana zaune tana kukan bakinciki abinda bunayya yayi mata , kukan ma ba wai akaron kanta taso yinsa ba, ji tayi kawai hawaye na fita daga cikin kwarnin idanunta, tayiwa kanta alkwarin duk runtse babu abinda zai sake shiga tsakaninta dashi, idan mutuwa zatayi da soyayyarsa , sai dai sonsa ya kasheta ,amman babu ita babu shi har abada ko komawa tayi lagos bazata shiga tsabgarsa ba .
tana cikin wannan kukan mumy tashigo d'akin ganin har 11:00 na dare bata fito taci abinci ba .
Tana ganin shigowar mumy tasoma k'ok'arin had'iye kukanta had'e da share hawayenta da sauri ,yayinda ita kuma mumy tana ganin haka ta maida kofar da sauri ta rufe ta k'arasa shigowa d'akin tana kiran sunanta "muwaddat meke faruwa ?
" lafiyarki ?
"kukan me kike?
"Waye ya mutu ko waye bashi da lafiya ?
Tayi mata tambayar gabadaya ajere tana zama kusa daita.

kai kawai muwaddat tashiga girgiza mata al'amun babu komai "ke ki bud'e baki ki min magana, ba wai ki dinga karkad'awa mutane kai ba "me ya faru ,me yasameki ?

Muryata cike da kuka da in ina tace " ba..Babu komai fa" "babu komai zaki zauna kina kuka kamar wace aka aikowa sakon mutuwa, ki gaya min abinda ke damunki ?
Wasu sabbin hawayen suka sake gangaro wa bisa kuncinta , tasa bayan hannunta ta goge tana sake girgiza mata kai .
Hankalin mumy ya sake tashe matuka, tace "wato kina boye min Abu ko ?
Cikin rawar murya tace "Sam Sam ba haka bane mumy ,"kina boye min mana mumuy ta fad'i tana mai mikewa tsaye da sauri tayi hanyar fita domin kiran dady, muwaddat tayi saurin riko tafin hannuta "mumy karki yi fushi dani Dan Allah ,babu fa abinda ke damuna kawai dai ina cike da kewar ummina ne ........
ta tsinci kanta da fad'ar haka wasu siraren hawaye na gangaro mata .

Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke sannan ta koma ta zauna tana dubanta had'e da nazarinta "har ga Allah ta yarda da maganar diyarta, saboda tasan yadda shakuwar dake tsakaninsu da uwarta tafi karfin haka ,domin kuwa daya baya iya d'aukan dogon lokaci batare daya ba ,yanzu haka kullun garin Allah ya waye akalla basuyi waya ba sai sun yi sau Goma hatta bacci suke tashinta wani lokacin ko abinci zata ci sai takirata tana cin suna waya haka zalika abi ,Yayinda komai akayi ta bangaren kowanensu ,yanxu ne zasu bugawa juna suna cike da tsantsar farinciki suna labartawa juna "
Ahankali mumy ta bud'e bakinta "to kuma shine zaki zauna kina kuka?
" idan kin gaji da zama damu kamata yayi kiyiwa umminki magana tasa azo a tafi dake .. .. ba wai ki zauna a d'aki kina kuka irin hk ba "
Amman yanzu ki bari zuwa wani sati sai ki koma, saboda ina son kije kalgo ki ga inna kafin ki koma, ki d'an yi kwana biyu agurinta ,dan koda yaushe idan munje sai tayi maganarki ,Dan haka zan saka ala'meen ya kaici gobe tunda weekend ce sai kiyi musu kwana biyu "zuwa lahadi ko manday sai ku dawo, ki soma shiri komawa
Muryarta a matukar raunane tace "to mumy "

Mumy tace "Muje ki ci abinci Sam baki son cin abinci muwaddat, shiyasa gashi nan kullun jikin naki babu laka bare kuzari ,muwaddat ta Mike tsaye jikinta a matukar sanyaye tayi gaba tasoma tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki , mumy ta bi d'akin da kallo sannan ta kai hannunta Kan wayarta dake yashe Akan gadon ta d'auka tana duddubawa, babu abinda ta gani duk number's din yan gidansu ne Dana kawayenta , sai number guda daya data ga an rubuta (man ) muwaddat...mumy ta kira sunanta. ...
ta D'an tsaya tare da juyowa ta tsaya tana duban mumy "waye kuma man ?
"Tayi shiru can tace " d'an makarantarmu ne "meye tsakaninki dashi ?
"Babu komai momy "to ki goge lambarsa bana bukatar ganinta cikin wayarki ,sannan ki dinga kiyayewa ,Allah kuma ya kiyaye mana ku a duk inda zaku sanya kafafunku .

Muryarta ahankali tace ameen ta amshi wayar ta goge number man har ma data Auwal gabad'aya sannan ta sake juyawa ta cigaba da tafiya mumy ta biyo bayanta ,
Mumy na fita ta kira ala'meen a waya ta sheida masa abinda take so ayi a gobe idan Allah yasa suna raye ta kirasa Dan ya kwana da shirinsa ,yace mata "babu damuwa Allah ya kaimu.
Tun daren al'ameen ya shirya kayansa set biyu kacal ya d'auka sai kayan Pajams dinsa haka ma muwaddat mumy ce ta shirya mata kayanta cikin yar k'aramar akwati ..

Washegari tunda sanyi safiya suka d'auki hanya zuwa kalgo, gudu kawai al'ameen yake sharara akan titi batare daya juyo ya kalli inda muwaddat take ba ,haka zalika itama bata kalli inda yake ba idanunta naga kallon titi ne, domin haushinsa take ji acikin zuciyarta, ganinta duk shine silar damuwarta silar da yasa ran bunayya ya 'baci har suka samu sa'bani dashi , Dan da kace bai aiko kiranta ba alokacin da duk hakan bata kasance ba ..
Tun yana dauriya har dai yasoma janta da hira tana amsa masa tana yatsina fuska amman ya dakewa zuciyarsa ya cigaba da janta Dan dai ta saki ranta sannan yana bukatar tafiyar tayi masa dadi gashi ga rabin rayuwarsa ,tafiya ce mai nisa tsakanin ilorin da kalgo sannan suka iso ..
suna shigowa kauye ya rage gudu
Adaidai wani madaidaicin gida yayi parking din motarsa ya fito yana Mika had'e da salati ,kusan minti goma ta fito tana kallon yanayin garin ,yana nan dai tamkar yadda ta sani acan baya sai 'yan canje canje kad'an da taga garin ya samu na cigaba ,ciki kuwa har da gidan kakarta ,Kafin kace me tuni kofar gidan sun cika da kananun yaran unguwar da almajirai suna kallonsu had'e da zagaye motar .

Daya daga cikin yaran ya k'araso gurin ala'meen yana washe baki "yaya ala'meen sannu da zuwa "yauwa musa sannu ya kake ya gida ?
ala'meen ya fad'i hk yana zagayo ya bud'e boot ya d'auki akwatin kayanta,musa yayi sauri ya amsa had'e da shiga cikin gidan inna .
Ya waigo ya dubeta tana kallon yaran dake zagaye suna wasa da tsalle tsalle "Muje ko ,nasan kin gaji dayawa "ba tace masa komai ba ta nufi hanyar cikin gidan tun
daga farkon shigowarta gidan tasan ba iyayenta kad'ai rayuwa ta sauyawa ba har da kakarta , koina tsaf tsaf sannan a tsaftace malale da tayis har cikin tsakar gidan bakinta d'auke da sallama tasanyo kanta ta k'arasa shigowa, inna dake tsaye jiran shigowarta tun shigowar Musa ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tana murnar ganin jikarta, "marhabun lale da mutanen iko da ilorin "muwaddat ta saki murmushi me tattare da gajiya sannan ta k'arasa ta rungume inna ajikinta "inna mun sameku lafiya ?
"Lafiya kalau ya hanya ?
Bata amsa ba ta saki inna tana dubanta "mu shiga daga ciki sannu kun kwaso gajiya "babban ango maraba sannu ,kun sha hanya "sai yanzu kika ganni tun dazu nake ta faman bud'e makoshi ina rattafa sallama amman kikayi min banza "yi hakuri mai gidan asaliyyan, ni na isa in shareka ai ko zan yi shariya sai dai in share wancan mai wuyan kamar lagwani , amman ba kai ba ,suka saka dariya ita dai muwaddat tayi gaba tashiga d'akin da inna ta nuna mata .
Chapter 49 · 0% Book details