Sashe 28
Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana isa a harabar asibinti yayi parking yana k'ok'arin fitowa daga cikin tsaleliyar motarsa sukayi kicibis da kausar sanye cikin uniform ,ahankali ya fito daga cikin motar yasoma tafiya cikin takunsa na d'aukar hankali, ta tsura bayansa ido tana kallonsa tana jin ina ma yazamo mallakinta ,jikinsa ne yabashi kallonsa take dan haka ya waiwayo shima yana dubanta sai dai nashi kallon da gani na tsantsar tsana ne tattare da takaicin kallon datake masa ,yaja tsaki ya girgiza kai kawai ya wuce saboda arayuwarsa ya tsani irin wannan kallon da mata ke masa ,kusan minti goma tayi a dan kare agurin tana kallon bayansa ...
Tun daya shiga emergency hankalinsa ya tashi matuka sakamakon kukan da tarar da wasu matune nayi , Allah Allah yake ya isa office din ummi yaga halin datake ciki a daidai bakin kofar shiga office dinta suka had'u ta riko hannunta cikin azama ta nufi d'akin tiyata dashi bai ce komai illa binta dayake ahankali har suka shigo d'akin dake cike da manyan likitoci ..
Suna ganinsu suka ja baya suna duban yaron da ake tunanin shi zai duba mara lafiya .
abinda ya gigita ummi har yasa ta kirasa cikin tashin hankali ,shi sam bai d'aga masa hankali ba, saboda inda sabo ya rigada ya saba ganin irin irinsu agurin practical ,wata k'aramar yarinya ce kwance akan gadon marasa lafiya a d'akin tiyata wacce shekarun haihuwanta bazasu wuce shahud'u ba a duniya , tana fidda numfashi sama sama ranta hannun Allah, sai dai gabad'aya fuskarta tayi damage,sakamakon 'yan ta'ada da suka kawowa mahaifinta ta hanyar kawo masa hari ,saboda ba'ason ya zarce kujerarsa ta d'an majalisar jahar dayake kai , sukayi rashin sa'a basu samesa a gidan ba ,wannan bakincikin yasa sukayi tillon diyarsa fad'e sannan suka watsa mata acid a fuska .
ahankali M. A yake kallon yarinyar yana girigiza kai , yana sake mamakin wannan tashin hankali da maseefar son siyasa irin ta mutanen nigeria,akan siyasa babu abinda bazasu iya yi ba, ya tausayawa yarinyar sosai ,batare da bata lokaci ba ya bukaci kayan aiki yana cigaba da dubanta tare da tunani ta inda zai fara ,cikin rawar jiki ummi take bada sauran likitocin umarni ,cikin kankanin lokaci M.A yashiga taimakawa yarinya cikin gaugawa, yayinda manya likutocin dake aiki a asibintin suka zagayeshi suna taimaka masa , ban da ummi wacce tuni ta fice daga d'akin din dan ta kasa tsayuwa saboda yadda fuskar yarinya yayi dan nama fuskarta har yasoma zagwanye.. ..
sosai M. A yashiga k'ok'ari akan yarinyar, domin taimakawa rayuwarta, sai dai duk wannan aikin da yake zuciyarsa na bugawa saboda wannan shine karo na farko da zai yi aikin daya danganci haka.
bashi ya fito daga d'akin tiyata ba sai gurin shida na yammacin rana, inda har lokacin iyayen yarinya sun kasa tsaye sun kasa zaune sai zariya suke suna rusa kuka,ta gabansu yazo ya wuce, kai tsaye gida ya wuce saboda ya gaji dayawa,yana zuwa gida bathroom yashiga ya sakarwa kansa shower ya gama ya d'auro alwala ya fito ya tada sallah ,byn yayi sallah yaso ya kwanta saboda wani irin bacci yake ji amman sanin da yayi bacci a daidai wannan lokacin bashi da kyau ,yasa ya koma parlour'nsa ya kwanta flat akan kujerar kushin me zaman mutun uku ya d'auki remut ya kunna TV ya janyo wayarsa ya kira cikin gida a kawo masa coffee ..
***********
ranar bacci M. A yayi sosai can gurin asuba wayarsa ce ta tashesa daga bacci kiran gaugauwa daga asibintin ummi yana d'auka "yace muhsin ya'akayi? Muhsin daya daga cikin likitocin dake aiki ne asibitin, yace
"daman yarinyar da akayi wa sugyren din ce fa har yanxu bata motsa ba, M.A yasa hannu ya d'auki agogonsa yana duba lokaci ,yace" okay nan da awa daya idan bata motsa ba ka bari nasani "okay...
Muhsin bai kira ba sai byn awa ya sake tabbatar masa fa yarinyar har lokacin bata farka ba ,bashiri ya mike ya shirya ya bar gidan xuwa asibiti ,akan hanyarsa ta zuwa asibiti ya kira ummi yake fad'a abinda ya faru tace"nima yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kira Allah dai ya bada sa'a yasa ayi nasara aiki "ameen ummi ..
......muwaddah kuwa tunda taji wayarsa da ummi hankalinta yayi matukar tashe saboda ummi ta bata labarin abinda ya faru jiya ,jikinta yayi mugu mugun sanyi dan batason ya samu matsala da aikinsa, gabad'aya a sanyaye ta dinga abubuwanta, ganin haka yasa ummi tashiga rarrashinta tana bata baki akan tayi hakuri" cikin kwanakin nan zata shirya mata tafiyarta zuwa ilori , dan a tunaninta kodan saboda haka ne yasa tayi sanyi taki sakin jikinta .
shi kuwa auwal tunda ya isa asibitin bai samu zama ba,sai kai kawo yake ,har sai da yarinya ta farfad'o tukunan hankalinsa ya kwanta ,batare da 'bata lokaci ba ya kira ummi a waya ya sanar mata, murna tayi sosai had'e da jiro masa addua , tun safe hankalinta bai kwanta ba sai yanzu daya kirata .
byn sun gama waya ta dubi muwaddat dake zaune tana kallon zeeyword.
" muwaddat ta kira sunanta cikin farinciki" "na'am ummi ta amsa tana dubanta "kinji bunayya ya samu nasara akan aikin nan "
murmushi tayi cikin sakin fuska saboda har ga Allah taji dadi sosai ,ahankali ta motsa labbanta tace"Allah yasa yafi haka "amen inji cewar ummi muwaddat tacigaba "ai jikina ya bani tabbas zai yi nasara saboda bunayya nada matukar kwazo .
"Haka ne Amman da fari naji tsoro sosai saboda karonsa na farko kenan "haka ne Allah dai ya taimaka.
Ummi tace "ameen tare da cewa yauwa bari na aikeki gidan alhj nuhu ki kaiwa hjy kubura wad'an nan atamfofin da kamfala,ai duk kalolin da kika d'auka sun miki ko?
"sun yi min ummi, sai dai ni kamfalar nafi so wallahi, ina jin kmr na had'esu duka na dinka dogayen riguna dasu, dan babu wace kalarta batayi min kyau ba "
"Allah shalelen umminta da abi ..?
Muwaddat tayi murmushin tace "da gaske nake "to ai shikenan bari abarsu kawai ki sha kwaliyarki dan nafi son kullun nayita ganin ki tsaf tsaf ,sai ki maida mata da atamfofin .
muwaddat ta mike ta amshi farar ledar dake rike a hannun ummi "tana lekawa ,"ummi naga ke baki d'auki kamfalar ba?
ummi tace nifa bawani damuna tayi ba, nafi ga atamfar dai.
muwaddat ta cire kamfalolin ta ajiye akan kujera, ta kama hanyar fita "karki dade kije yanzu ki dawo kafin abi ya dawo, kai kawai ta daga mata ta k'arasa ficewa.
kai tsaye inda ummi ta aike ta nufa,tana shiga gidan, da mijin hjy kubura tasoma cin karo a harabar gidan yana zaune rike da jarida daily trust, gabansa k'aramin tebur ne mai d'auke da tattaciyar ruwan inibi da ruwa ,sai ritsetsen tubinsa mai kama dana yan giya.
sallamarta yasa ya bar abinda yake ya d'ago ahankali yana kallota ,har ta iso daf dashi bai d'auke idanunshi daga gareta ba, ta bude baki da kyar ta gaishe shi "ina yini ?
da sauri yace lafiya lau muwaddat yammata ya gida da hutun makarata ?
"lafiya lau ta bashi amsa atakaice tana tafiya batare da ta sake kallon inda yake ba. shi kuma yabi bayanta da kallo cikin rausayar da kai, shi dai muwaddat tana matukar burgeshi duk sanda ya ganta sai yaji wani abu ya tsarga masa ,yana son tukararta amman babu fuskar da zai bayyana mata abinda ke cikin ransa, ahankali ta k'arasa cikin gidan inda ta iske hjy kubura zaune tana kallon tashar arewa 24 ta gaisheta tare da mikawa mata afamfofi tace "gashi inji ummi tace na kawo , hjy kubura ta amsa tana murmushin jin dadi ganin duk an kwashe rabin kayan ,muwaddat ta juya abunta tasoma kokarin barin parlour'n ,hjy kubura ta ajiye laidar a gefe tace "ki gayawa ummintaki zuwa anjima idan na natsa zan kirata..muwaddat tace
"to ,tacigaba da tafiyarta.
inda tabar alhj nuhu zaune a nan ta dawo ta iske shi yana kallon kofar shiga cikin gidan ,bata ko kalli inda yake ba saboda tsarguwa datayi dashi, dan sam batason yawon kallo arayuwarta koda ta juya baya tana takawa ahankali jikinta na bata idanunsa akanta suke,shi kuwa ahji nuhu ido ya tsurawa bayanta tare da sauke ajiyar zuciya yana lasar lips dinsa da tuni suka fara bushewa ,da sauri ya mike daga zaune dayake ya biyota, wanda lokacin tuni har muwaddat ta kai kofar get din gidansu , ya tsaida ita cikin tsarkewar muryar yana kiran sunanta "muwaddat muwaddat!! ....
taja ta tsaya tana juyowa ahankali tare da tsare gira da had'e fuska sosai "tace menene?
sai da gaban alhaji nuhu ya buga saboda firgicin daya ziyarcesa ,duk da yadda zuciyarsa ke bugawa hkn bai hanashi k'arasowa inda take tsaye ba, ya d'an lumshe idanunsa yana fad'ad'a fuskarsa "uhm ammm muwaddat daman ina son na d'an miki wani bayani ne gsky akan wani lamari mai girma dake zuciyata , wato muwaddat na dan jima ina son bayyana miki sirrin dake raina akanki "
tayi shiru tana sauraronsa har sanda ya numfasa sannan yacigaba "muwaddat azahirin gsky idan kin kalli cikin kwayar idanuna zaki iya fahimtar inda zancena ya dosa tayi saurin katsesa " ni ban fahimci komai akan zancenka ba "ya gyara tsayuwa yana rungume hannuwansa akirji ga kuma ritsetsen cikinsa "eh to daman dai na dad'e ina sonki kuma aurenki nake son yi idan kin amince"
idanunta ta rausaya cikin nasa dariya na neman kufce mata a yadda take kallonsa da ritsetsen tunbinsa, da jajayen kwalala idanuwansa kmr na agolan nafawa, hancinsa a zube kmr faranti yasa dryar ta k'arasa kwacewa dry tana rufe bakin da hannuwanta .