← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 99

Sashe 21

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana barin gurin ya maida idanunsa akan mahaifinsa "abi ya furta muryarsa can kasa kmr mai koyan magana "ya'akayi ne bunayya, kana bukatar wani abu ne?
"ko abincin ne bai yi maka ba?
"uhmm komai yayi ai ummina daban take acikin matan africa gurin girki she's perfect abi yayi murmushin jin dadi an yabi masoyiyarsa.

"abi ina son muyi wata mgn mai mahimmanci da kai wanda ya shafi bangaren rayuwata "to ka gama breakfast din mana sai muyi "no abi bazan iya sakawa cikina komai ba matukar ban amayar da abinda ke cikin raina ba"

abi ya numfasa yana gyara zamansa "to ina sauraronka "M. A yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara "abi ya tsareshi da idanu "ina sauraronka ka fad'a min damuwarka duk da bana tunanin wata damuwa ce mai tsanani "gsky abi nima a tunani bawata damuwa bace matukar za'a fahimceni daman dai aure nake so nayi acikin lokacin nan, idan ma da hali ina son kafin na koma hada Master's dina nayi ,na wuce tare da *matata* ......

abi yayi shiru yana kallonsa tare da sake maida hankalinsa gbdya akansa "aure nake son nayi acikin lokacin nan,idan da halima ina son na wuce da matata ya maimata hkn a kasan zuciyarsa yana cigaba da kallonsa .
M. A ya d'an yi murmushin a kunyace yace "Allah da gaske abi ina son nayi aure naga ya'yana tun ina da karancin shekaru, shiyasa na dawo adaidai wannan lokacin kaga yanzu na had'a digirina na farko ina da karancin shekaru ,ina son kafin nayi join din master inyi aurena na huta ....

ajiyar zuciya abi ya sauke da karfin gaske yana dubansa wanda zuwa lokacin muwaddat ta dawo parlour'n ta isa inda M. A yake ta d'auki remut ta koma mazauninta adaidai wannan lokacin abi yace "duk naji bayaninka amman nafi son ka kammala karatunka gabadaya sannan aure, yanzu ma da kake maganar aure kasamu wace kake so ne ko dai kawai auren zakayi?

ya d'an yatsina fuska "ni dai dad'y ka amince min ina da wacce nake so ayanxu hk muna tare da ita muwaddat tayi saurin d'agowa tana kallonsa a matukar tsorace kafin ahankali tasoma girgiza masa kai ala'mun kar yayi mata hk..

"wace anan din?
"nan dai daga ni sai kai sai kuma auntynka muwaddat ,ko acikin 'yan aiki kaga wace kake so ne?
yayi murmushi kawai yana nuna muwaddat da bakinsa a tsoroce abi ya waigo gefen da take zaune , take tashiga girgiza masa kai "Allah abi wasa yake maka ...

abi yayi dry "kai bby manya meye na saurin tsorata hk "abi ba tsoro bane ta yaya ma zaice ni yake so nifa auntynsa ce "wannan kuma gsky ne bunayya kayi saurin ido dayawa ,nasan da wasa kake yi ,idan ma gaske ne kabari ka kammala karatunka alabashi sai kayi auren...

nan take abi ya shashantar da zance ya maida maganar shirme" ina M. A ina aure a yanxu duka guda nawa yake da zai takalo aure ..?

wata hirar suka shiga yi yayinda shi kuma ya rasa abinda zaice yayi tagumi kawai yana dubansu " tunanin mafuta yashiga yi, yasan tunda mahaifinsa ya shashantar da maganarsa ko umminsa taji itama hk zatayi dan ra'ayinsu daya..
yunkura yayi ya mike tsaye zai bar parlour'n batare da yaci abinci ba "abi ya kirasa bunayya ya ba kayi breakfast ba?

kasa cewa komai yayi ya tsura musu ido kawai can kuma ya juya ransa a 'bace ,abi yashiga kiran sunansa amman sam yaki juyowa cikin haka ummi tashigo parlour'n da sallama tayi wani irin azababben kyau sai kamshi ke tashi ajikinta "abi ya amsa yana kafeta da idanunsa kyawunta na nan har lokacin kamaninta bai canza ba sai dan manyanta datayi amman dayake ma'abociyar kwaliyace bamaza'a ce itace ta haifi M. A ba d'an kiba kad'an tafi muwaddat "hubbey lfy naji kana kiran bunayya cikin d'aga muryar da ban saba jinka dashi ba lafiya ?

saurin waskewa abi yayi ta hanyar cewa "babu komai hira muke da muwaddat kunnenki ne dai yaji yo miki hk"
tayi murmushi "to hirar me kuke yi?.

"daman shawara muke yi da bby akan zanyi miki kishiya, wai ita tagaji da zama da aunty daya acikin gidan nan ummi tace uhmm "ka dai fad'i gsky babu ruwan bby idan ma dai auren kake so kayi ka daina kameme tun yanzu gara ma ka fito fili ka fad'a mana idan ka hango wata ne..

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVE AND EVER~

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 10

....Cikin dry abi yace "o ,kishi kumallon mata yanzu har cikinki ya duri ruwa ,shi yasa ma yar fara'ar da kika shigo daita ta d'auke ,kin wani tamke fuska daga jin zance kishiya "

"cikin dariya ummi tace "Allah sarki su kishi manya ,dadin abun ban ta 'bata fad'a akan zance kishiya ba ,kuma ni ko kishiyar za'a min me zai tada min hankali ?
"tazo ga gurin zama nan ni wallahi har na gaji da zancenta kullun, ayita kawai mu huta..

"Ai kuwa Ki sha kuruminki wannan karon zan bugi kirji na k'aro aure sa'ar baby suyi zamansu lfy ko baby ?

sai lokacin muwaddah ta saka baki "Dan Allah abi ka daina zance kishiya nan kar ka fad'awar da ummina gaba ,kasan dai yanzu ba kowace ke da imani ba, kowace k'ok'ari take idan tashigo tayi iko ,mu kuwa babu matar da zata shigo gidanmu tayi mana iko aciki..

"Abi yace shikenan tun da kin bi bayan uwarki wato ke ma ba kya son na k'ara aure kin fi son uwarki ta zauna babu kishiya ko ?

"Uhmm abi ba haka bane ,gani nayi da kunya yanzu ace zaka k'ara aure.."kin ci gidanku ke da kunyar ,ba sai na bari sai na aurar dake da bunayya ba ,sannan sai na auro sabuwar amaryata mai kalar 'yan birni ,in zaki zo sai kice wa mijinki zanje gidanmu ana bikin babana ..

Suka fashe da dry gabadayansu muwaddah tace "Dan Allah abi karkace zaka yi aure ,wallahi in ka auro budurwa gori za'a dinga yi mana nida bunayya ,ace babanmu ya auro k'aramar yarinya..

"To ai ni din ma bawani tsufa nayi ba, Dana aske yar furfurar nan zakiga 'yammata na rububina, suka sake kyalkyalewa da dry muwaddat na dry tace ,"kai abi wata yarinya ce a yanxu zata yarda ta auri tsoho in ba mara wayo ba ,ta k'arasa mgnr tana sake bushewa da dry .

ummi tace" in kai yarka ta hanaka auren yara ,kai tsofafi sazo neman aure gurinka ,abi yace "kmr ya ya ?
"Oh baka da labarin abokinka alhj jabril yana son muwaddat "
abi yayi 'yar dariya ana wata ga wata kenan ga auwal ga abokinsa ,Amman zahiri cewa yayi "shikenan nazama Surukin tsoho a she har gaytumai ke kawowa diyata Hari...

Muwaddat ta turo baki cike da shagwaba kmr zatayi kuka "Dan Allah abi ka bari ,kuma karkacewa ummi komai ,ni dai wallahi babu ruwana me zanci da wannan tsohon "

"me yasame shi shikenan sai muyi musaya Dan nima na gano iri a gidansa, kun ga kuwa ta kwana gidan sauki saboda shi bai da yawon surutu daman kince kin fi son auren nmj mai shiru shiru , yana zuwa zan sheida masa na bashi ..

Muwaddat ta shagwa'be fuska ummi tace "zancen wasa ya wuce bazan laminci ka rikita min 'ya ba shima abokin naka tuni nayi masa Burki na zuwan da yayi kwanakin ban mishi ta dadi ba ,tunda na gane yana son baby nace "masa kar ma ya fara domin yasan bazan iya basa bby ba, Dan ba baby ba ko wace ta girme mata gareni yayi mata tsufa ballanatana ita yarinya.

ina gaya masa sai ya kama driya har da cewa haba ummi ya zaki min hk km, ke din da nake sa rai zaki goyi bayan abun, nace "yaje can ya nemi umminsa ni bazan zama surukar tsofafi ba ..

Abi ya fashe da dry Amman dai gsky kinji kunya tun da kika tsaya kina sai'nsa da suruki "ai abokinka shi yayi babbar abun kunya banda budurwa zuciya ina shi ina muwaddat ?" har da zai bud'e baki yace yana sonta ko an gaya masa neman kai muke yi daita ..

"Yarinyata idan ta kammala karatunta sai ta zaba ta durje tukunna yara matasa masu sabon jini bashi ba ,ko kai ina tunanin ya girmeka kullun yana cikin kankare fuska Dan kar tsufansa ya bayyana ,abinda bai sani ba gyara fuska daban tsufa da ban ..

Abi yayi dry "to ai diyar taki ce ta cika farin jini dayawa yanzu ma wani case din muka gama ana da bunayya wai..... muwaddat tayi saurin cewa "Dan Allah abi kar kace komai "ki barshi yace ,duk masu sonki sa gama shiermensu diyata ta mai rabo ce ....

Aransa yace Allah yasa rabon Auwal ce Dan haka kawai yaji al'amarin ya kwanta masa, bai sani ba ko dan yadda auwal din yake acikin zuciyarsa ne, shi kansa zai so yayi auren wuri domin yaga 'yan jikokinsa tunda shi kad'ai Allah ya nufesa da samun , ,Amman karatunsa na bukatar natsuwa da ajiye hankali guri daya, yanzu yana yin aure hankalinsa dole ya rabu gida biyu duk ma ba haka guda nawa bunayya yake ....?

Hira ta kwance atsakaninsu wani lokacin muwaddat tabi bayan ummi ,wani sain tabi bayan abi , sosai sukayi hirarsu data zame musu jiki a duk sanda suka had'e, rayuwarsu abun sha'awa, duk wannan hirar da'ake hankalin muwaddat ya rabu gida biyu ,wani bangare na zuciyarta na gurin M. A daya bar parlour'n cikin fushi ,wani kuma na gurin hirarsu abi , Dan Sam batason abi yayi su'butar Baki ya gayawa ummi abinda ake ciki , tunda tasan itama ba wani amincewa zatayi da abun ba .
Cikin haka abi ya Mike yace zaije ya kwanta ya d'an huta ,yaso kwarai ummi ta biyosa ko d'an tausa tayi masa Amman yaga ta sharesa tacigaba da kallon tashar zeeyword dan haka ya kama gabansa yana tsokanarta.
Chapter 21 · 0% Book details