← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 99

Sashe 68

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.....muwaddat bata farka ba sai wuraren la'asar ta farka bakinta d'auke da salati ,yayinda ummi da abi sun shigo d'akin yafi sau goma bata tashi ba, sai a karo na karshe ne da ummi tashigo ita kad'ai ta iske ta farka tana zaune ta rafka uban tagumi .
a Sanyaye ta gyara zamanta tana duban ummi da shanyayyun idanunta da suka kod'e saboda tsabar kukan da taci ,ahankali ummi ta matso kusa daita ta zauna had'e da riko tafin hannunta, take taji wani irin zafi ya ratsa tafin hannuta cikin tsarkewar murya tace " sunnu baby duk gajiyar hanyar ce haka,ko daman baki da lafiya ne ?

Da kyar ta iya bud'e baki cikin tsantsar jin kunyar ummi ta tsinci kanta da cewa "eh" yayinda gabad'aya ta kasa sakin jikinta daita tana jin kmr zata fahimci abinda ya faru ne a tsakaninta da bunayya .

ummi tayi shiru tana nazarinta na wani lokaci sannan tace "to shikenan ki tashi kiyi wanka kiyi sallah dan nasan yanzu haka ko sallar azahar bakiyi ba ko?
Ta d'aga mata kai ala'mun Eh .

gabad'aya jaruntar da tayi saura atattare daita, ta tattaro ta sanyawa gangar ajikinta da niyyar tashi da kuzari ,sai dai me tana gama ziro kafafunta daga Kan gadon ta ji
bazata iya d'aga kafafunta ba ,saboda wani irin tsami da ciwo da cinyoyinta suka d'auka, ,hatta gabobin jikinta jin su take tamkar an sassare mata su, take jikinta ya d'auki rawa .....

a matukar tsorace ummi ta matso gareta sosai tana binta da wani irin kallo, bakinta na rawa tace "ke lafiyarki kuwa, me ya samu kafafunki suke rawa haka ?

rud'ewa muwaddat tayi har tsayuwa ta nemi gagareta ta soma yin kasa tana lumshe idanuwanta , ummi tayi saurin tarota zuwa jikinta tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "me zan gani haka ni mukarama?
"hubbey ...hubbey !! ta shiga kiran abi da iyakacin karfinta, kmr an jeho shi ,ya banko kofar da karfi yashigo a matukar firgice yana tambayarta "lafiya?
"ina fa lafiya ta yani gani hubbey ,ta fad'a tana sake duban muwaddat dake k'ok'arin tsaitsaita tsayuwarta ta karfin tsiya jikinta na rawa ..
abi yace "me zan gani?

ummi ta kamo hannun muwaddat dake lummmmmm da idanuwanta tace "ke ki yi tafiya yaga yadda kika dawo ?
numfashi muwaddat ta janyo ahankali ta fesar tana lumshe idanu, kana bud'esu da kyar sannan ta soma ta kawa sannu ahankali da niyyar shiga bayi ..har ta gama shigewa bayi idanuwansu na kanta .

da sauri ummi ta juya ta dubi gefen da abi ke tsaye ,tana jujjuya masa hannu tare da marairaicewa "hubbey kaga yadda tafiyarta tayi ba?
"na gani menene ya samu tafiyartata?

jikin ummi na wani irin rawa ta janyo hannu abi sukayi hanyar fita daga d'akin ,kai tsaye d'akinsa ta nufa hankalinta a matukar tashe, idanunta sun cicciko da ruwan hawaye "wai hubbey meye haka ne?
abi ya fad'a shima hankalinsa a tashe.
"duk kin bi kin wani tayar da hankalinki ,ni fa gabad'aya ban fahimci komai ba.

ummi tace "bazaka fahimta ba tana kuka "wai meye hk ne hubbey nifa banason irin haka ,"ki fito ki fahimtar dani, idan wani abu ne ya sameta ,bawai ki dinga min irin haka ba,
ya fad'i yana kamota suka zauna abakin gado "ki fad'a min abinda kika gani ...ko na samu natsuwar zuciya ? muryarta na rawa tace "wallahi gani nayi kmr an ta'ba min yarinya ........
ta k'arasa mgn hawaye na gangarowa bisa kuncinta ...

"what..? "when?
"ban gane an ta'ba miki yarinya ba ?
"wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba an ta'ba min yarinya.. ....
abi yayi shiru yana kallon yadda take zubar da hawaye had'e da nazarinta, kana daga baya yace " haba mukarama ,haba mukarama wannan wace irin magana ce haka ?
"a tunanina irin tarbiyar da mukabawa baby ko kuda ne zai zama mutun ajikinta bazata ta'ba amincewa dashi ba bare ta bawa wani kanta, sannan ki dinga kyautata zatonki..
" hakika manzo Allah tsira da amincin Allah shi tabbata agareshi yace" *iyyakun wazzana, "kashedinku da zato, "fa inna zanna akzabul hadis," domin zato shine mafi karyar labari*
dan haka ki tsarkake zuciyarki ,ki sanya ikilasi acikinta ,sannan ki cire wannan zaton aranki, babu mamaki ko gajiyar hanya ce ,ta maidaita haka, tunda ki rigada kinsa yadda baby take , a duk sanda tayi tafiyar hanya irin hk ,a galabaice zaki ganta, sosai abi yashiga kwantar mata da hankali, har dai taji ta d'an samu natsuwar zuciya, tare da k'ok'arin kawar da abinda taji.

bangaren muwaddat kuwa cike zuciyarta take da matsanancin fargaba abayi, ban da tsinkewar zuciya babu abinda take ji ajikinta , jikin kofar bayin ta dawo ta jingina jikinta tana leken fuskar ummi, har sanda suka bar d'akin , ta sauke naunauyen ajiyar zuciya, jikinta na sake d'aukar rawa "ya Allah ka rufa min asiri...kada kasa ummi ta fahimci wani abu atare dani.. ..ya Allah ka taimakeni, ka taimakeni kada ta gano komai .....
cikin sanyi jiki ta had'a ruwan zafi tashiga gasa jikinta kmr yadda matar nan tayi mata d'azu da safe ,ta dad'e cikin ruwan zafin har sai da taji tsamin da gabobinta jikinta sukayi sun ragu sannan tayi brush da wanka ,had'e da d'auro alwala ta fito ta iske Muhammad auwal zaune a gefen gadon ya kwanta flat ,kafafuwansa duka a kasan tayis yana girgizasu , sannan yayi sama da rigar dake sanye ajikinsa har ana iya hango farar singlet din dake cikin rigar .

Kamar ta juya ta koma cikin bayin taji, sai kuma ta k'araso saboda tasan kota juya ta koma ciki ,hakan ba zai sa ya fita daga cikin d'akin ba, matukar ba shine yaga dama ba .
kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta daga garesa tana jin wani irin tuttukin bakinciki mara misaltuwa ,ta k'arasa ta tsaya gaban mirrow tana goge jikinta da towel tayi tamkar batasan da wani halitta a kwance agurin ba .
bata shafa komai ajikinta ba, illa kwalbar turaren data d'auka ta fesa a gabadaya ilahirin jikinta ,sannan ta nufi wardrobe dinta ta d'auko doguwar riga material wacce ta sha tsone work a iya ratsin brest dinta ta sanya .

Ta d'auki sallaya ta shimfid'a ta fuskanci gabas ta tada sallar azahar ,bayan ta idar , ta sake mikewa domin gabatar da la'asar d'an lokacinta tayi , duk yana nan kwance shima da ala'mun bashi da niyyar ce mata komai, cikin haka wayarsa ta d'auki k'ara ya bud'e idanunsa dake lumshe ,kana ya zaro wayar daga aljihun wandonsa ya d'auka yasoma amsa waya "shikenan okay i will try ..." shine kawai abinda kunnuwanta suka jiyo mata .

Bayan ta idar da sallah ,ta waigo ahankali inda yake kwance, nan taga wayam babu shi babu alamunsa, ta dad'e agurin zaune tana neman gafarar ubangijinta bisa abinda ta aikata a daren jiya tana kuka tana sake maimata , *allahumma anta rabbi laila a illa anta, khalaqatani wa'ana abduka, ana ala ahduka wa wahduka masta'atu auzubika min sharri ma'hsanahtu, abuhu laka bi nihmatika alaiya wa abuhu bi zanbi ,faga firli, fa inahu la yagfuruzzuba illa ant*

byn ta gama, mikewa tayi tsaye ahankali ta koma Kan gadonta ta jingina bayanta da pillow had'e da kallon ceiling d'akin still tana cikin fargaba,shigowar ummi yasa taji gabanta ya sake bada wani irin sautin bugawa, take yanayinta ya sauya, ta shiga kokuwa da numfashinta ,yayinda zuciyarta ta dinga dokawa tana tsalle tmkr zata fasa kirjinta tayo waje , ummi ta k'araso ta zauna kusa daita tana ta'ba gefen wuyanta , zuwa lokacin ba taji zafi kmr d'azu ba, dan hk ta sauke naunauyen ajiyar kana ta kira sunanta "muwaddat hakika d'azu naji matsananci tsoro ,har ma da faduwar gaba, nayi zato akanki wanda har yanzu hkn yaki barin zuciyata, sai dai wani bangare na zuciyata na karyata min hakan, sbd nasa ba zaki ta'ba aikata hkn gareni ba, duba ga yanayin tarbiyarki, "amman na rasa me yasa zuciyata tayi zargin wani abu attare dake, wanda ban ta'ba jin hkn ba sai yau....
" ko dan yanayin tafiyarki dana ga ta canza ne ban sani ba ...

da sauri ta had'eye abinda taji ya tsaya mata a makoshinta a tun shigowar ummi sannan ta yunkura ta sauko daga kan gadon tana takawa ahankali tace " ummi ki kwantar da hankalinki babu abinda ya samu tafiyata fa , kawai dai haka nima naji kafafuna sun rike d'azu , amman nafi tunanin zaman mota ne kalleni yanzu kigani ,ummi ki cire tunanin komai aranki domin bazan iya aikata hkn gareki ba ta k'arasa maganar cikin sheshekar kuka... .. ..

"numfashi ummi ta sauke tace "to shikenan bance min ki min kuka ba muje ki ci abinci , koma dai bari nasa baba mairo ta kawo miki nan ki ci Allah ya hutar da gajiya ,amman wallahi sai yanzu na d'an samu natsuwar zuciya, ta mike ta fice daga cikin d'akin zuciyarta na dokawa ,
ita kuma muwaddah ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya tana godewa Allah daya rufa mata asiri.
Chapter 68 · 0% Book details