Sashe 39
Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gasky aunty bazan iya ba kawai ki taso idan kika ki kmr kin wulakanta dady ne muwaddat ta yarda da shawarar kanwarta ta tashi ,ta sauya kaya jikinta ta shirya tsaf ta fito cikin wani had'adden material mai maseefar tsada kayan sunyi mugun kama jikinta tayi kyau sosai kana kallonta kasan yar Hutu ce ba'a kashe kudi a banza ba hatta jaka da takalmi kace domin kayan aka kerasu ta d'an yafa Gyalenta ,kana ta fito parlour'n dady ya dubeta yana driya "kai yar gidan daddy wannan irin kwaliyar haka kar fa ki gigita mutane gari gashi babanki bai tashi miki aure ba .
Ta dan yi murmushi saboda wasan da dady yake mata ala'meen kuwa idanunsa kyam akanta yana son yaga yadda zatayi magana zata ce mishi su fita ko kuwa Jan aji ba zai bari tayi mishi magana ba ,koda yake ta cancaci fiyye da hakan yacigaba da kallonta saboda kwaliyarta ta burgeshi, shiyasa sam ya kasa d'auke idanunsa akanta ,lokuta dayawa mace mai yanga tana burgeshi amman baya son Jan aji yayi yawa kuma bai fiyye shiri da shagababbiya ba ,yana daya daga cikin abinda yasa yake gwasale eiman shagwabatar tayi yawa kmr itace auta idan tana wasu abubuwan ko sabir k'aramin kaninsu baya abinda take yi .
tun muwaddat na yarinya yasanta da shagwa'ba saboda gata da yayi mata yawa ,Yasan dole ne ta zama sangartacciya domin gata mugun abu ne kuma gata guba ne agurin wasu ya'ya Dan bakowanne Dan gata yake samun ingantacciyar tarbiya ba ,tun sanin dayayiwa muwaddat tana yarinya har yau da wannan fuskar yake kallonta ,shi yasa lokaci datazo yayi kmr bai Santa ba domin bayason yashiga harkokinta bare yasha haushi, amman d'an zaman datayi yanzu a gidan ya kula kmr tana da kamun kai ,domin yanayin halayenta suna burgeshi bata da son hayaniya kuma bata da yawon surutu sannan akwai natsuwa ,illarta girman kai da Jan aji, gashi shi yanzu zuciyarsa ta kamu da matsanancin soyayyarta....
Muwaddat tayi zamanta da Jakarta a hannunta shi kuma yaki yace mata tashi su tafi, sai dady yace "ku tafi mana tunda kin shirya ,zaman me Kuke?
Ala'meen ne ya fara mikewa batare idanunsa na akanta ba yace "ki sameni a mota bata amsa ba ta Mike tabi bayansa ,Kafin ta k'arasa gindin mota shi har yashiga ya zauna ,tasa hannu jikin motar tana kokarin budewa sai taji shi gam a kulle , bazata iya ce masa ya bud'e Mata ba ,kawai sai ta matsa ta bud'e gidan baya ta shiga ta zauna ala'meen ya d'an waigo kawai ya kalleta baice komai ba ,yayi zaton ko ta kasa bud'e gidan gaba zatace a bud'e mata ,Amman sai yaga ta kame a gidan baya ,a zuciyarsa yace lallai ma wannan yarinyar direba zata maidani ko me?
Ya dai daure ya tada motar suka tafi suna hawa titi ya fara sharara gudu ban da kidan zamani ba abinda ke tashi acikin motar ,glass din motar ya saita gefenta domin yasamu damar kallonta adaidai wannan lokacin wayarta tayi k'ara ta d'auka tana magana da abi Sai wani magana take cikin shagwa'ba.
Alameen ya natsu sosai ahankali take magana Amman ya fahimci da Wanda take waya ,har wani lallaminta t
yake "haba yar gidan dady menene abun fushi kuma ?
"Cikin zumbura baki tace "to abi bayan kaine yau baka tasheni a bacci ba shiyasa har na makara banyi sallah da wuri ba yace "kiyi hakuri abinda yasa tun asuba Dana shiga massalaci ban fito ba sai da gari ya waye sosai shiyasa ban bugo na tasheki daga bacci ba, na yi zaton idan umminki ta tashi zata tasheki Amman kibari in Allah ya yarda zan cigaba da tashinki da asuba ince dai idan na ta dake kiyi sallah kina min addua kullun ?
A marairace tace " haba abi ina maka mana taya daman za'ayi in yi sallah ban wa babana addua ba "yauwa yar diyata nasan zaki min ina fatan kina jin dadin zaman ilorin?
"Abi babu laifi garin akwai dadi "da fatan hajara bata takura miki don nasanta da zafi akan yaro "dady wannan karon bata matsa min ba da yake tasan halinka Dana ummi "to fatan dai baki da damuwar komai "wallahi abi babu wata damuwa,sai dai gaskiya ni abi ina son na dawo "ki k'ara zama tukunna har yanzu da sauran lokaci kafin ki koma makarata ki dai dinga duba litattafanki saboda kinsa da kun koma zango karshe zaki shiga kuma zamanki anan zaki fi samun nasuwa saboda takurawar bunayya .
"Shikenan abi tunda kace haka na amince zan zauna Amman nayi kewarku ban da bunayya ,abi yayi murmushi "mu ma muyi kewarki ,bunayya daman wani kewarsa kikayi bayan kuna tare duk kwanakin nan ince yau kwanansa uku da dawowa, nan da sati biyu masu zuwa zai koma London take gabanta ya fad'i yashiga dukan uku suna hira da abi cikin nishadi shi kuwa ala'meen tukinsa yake Amman hankalinsa na gurinta sai lokacin ya gano yawon amsa wayoyinta datake yi ashe ba wayoyin samari bane da iyayenta take ko da wancan miskililin yaron da baya ganin mutunci mutane shi Sam yaron baya burgeshi ..
Satar kallonta yacigaba dayi wato Dan tsananin gata har tashinta suke daga bacci ,bayan daren da suke rabawa suna waya ita dasu .
Bai rage gudu ba sai da suka shiga ciki wata unguwa sannan ya rage gudu ya karya kwana yashiga cikin layin a kofar wani madaidacin gida yayi parking ya bud'e murfin mota ya fito ya Dan jira ko zai ga ta fito daga cikin motar Amman sai ya lura bata da niyyar fitowa wata wayar ma take amsawa sai ya tuna ashe bai gaya mata cikin gidan zasu shiga ba ,sai daya bari tagama wayar sannan ya bud'e mata murfin motar "bisimillah ki fito muje ki gaida matar abokina ya tsira mata idanu ko zatace wani abu batayi magana ba ta zuro kafafunta ta fito daga cikin motar suka jira suka shiga cikin gidan .
minal ce ta fara tararsu da faraa ta kaisu parlour'n ta tana fad'in "kai alameen sai yanzu tun dazu ake jiranka Amman ka shanya min miji ,yayita kokarin nemanka a waya bai sameka ba .
"Al'amen yace ku ya femin madam wallahi wani Dan uzuri ne ya tsaidani, ya fad'a yayinda yake kokarin zama a daya daga cikin kujerun kushin din parlour'n ya d'an dubi muwaddat sannan ya cewa minal "madam gafa bakuwa na kawo miki .
Itama ta dubi muwaddat cike da faraa yayinda ta nuna mata wurin zama da murnarta da komai ta karbeta sai kace tasanta muwaddat taji dadi sosai da irin tarbar da minal din tayi mata ,suka gaisa a mutunce ta fara tsokanar al'ameen in ce sabon kamu akayi shiyasa tutar latifa ta fara dusashewa ?
Cikin murmushi yace "no wannan kanwatace a lagos take ta d'an zo mana Hutu ne ina angon naki ?
"Yana ciki gajiya yayi da jiranka shiyasa ya shiga ya Dan kwanta bari na tasoshi .
Tana shirin shiga sai gashi ya fito daga bedroom dinsu ganin ala'meen tare da muwaddat ya sashi washe Baki da yake ya taba ganinta sau biyu dayaje gidansu cikin fara'a yace "a she ba kai kad'ai bane ,cewa zakayi yau muna da babbar bakuwa ya fad'a yana kallon muwaddat.
Ta dan kirkiro murmushi dole kana ta gaida shi minal kuwa sai rawar jiki take tana nan nan da muwaddat kafin kace me duk ta zagayesu da abubuwan motsa baki al'maen Yasan ba lallai bane muwaddat taci abubuwan da aka kawo mata Dan haka yayi hanzarin cika cup da ruwan lemu ya tura mata gabanta ,abun mamaki sai yaga ta d'auka tasha suna ta hira minal sai tsoma muwaddat take cikin maganar dole sai da muwaddat ta saki jiki tashiga cikin hirar ,ta dinga saka baki jifa jifa, ala'meen zuba mata ido yayi saboda lura dayayi yadda yarinya ta iya lafazin iya magana cikin natsuwa tare da kwantar da murya da gogewar harshe hakan ya tabbatar mishi da tasan abinda take ,ala'meen ya dubi minal sannan yace "madan Dan Allah zan barta anan saboda inda zamu da oganki idan mun dawo zan kaita taga gari kmr yadda dady ya bukata minal tace "babu damuwa ya Mike ya kada mukullin motar dake rike a hannunsa tare da watsa idanunsa akan muwaddat Amman ita Sam bata kallesa ba asalima hankinta na can gurin turawa M. A sako .
Yace "ayshatul muwaddat ki zauna anan kafin muje mu dawo muryarsa ta ratsa cikin dodon kunnenta da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido saboda yadda yakira complete name dinta ya razana zuciyarta domin tun tasowarta babu Wanda ke kiranta da wannan sunan bayan Auwal dinta sai yanzu dayayi mata ,da muwaddat akasanta kuma dashi kowa ke kiranta, ita kanta mantawa take da sunanta na gasky saboda ba'a kiranta dashi sakamakon sunan uwarsu ummi ne daita, suna girmama sunan babu abinda yabata mamaki kmr yadda ala'meen yayi amfani da sunan gurin kiranta ..
Ahankali ta gyada masa kai kawai Amman batayi masa magana ba, har ya fice daga parlour'n suna hira da minal saki fuska da fara'ar da minal ta nuna mata ya burgeta da kuma kyakkyawan tarba da rawan jikin datayi daita yasa taji tana son minal .
Minal dai yar wani fitaccen d'an siyasa ne anan garin ilorin ba'a Jima da yin bukinsu da Hisham ba Wanda ya kasance babban aboki agurin ala'meen tare suka kare karatu a Rasha har yanzu minal karatu take ,ayanzu haka tana karatunta a jamiar ilorin, hira ce ta balle tsakanin muwaddat da minal tamkar sun dade da sanin juna muwaddat ta saki jiki sosai har kowa ya labartawa kowa tarihin rayuwarsa.
Anan muwaddat ta wuni cur a gidan minal sai kusan yamma sannan ala'meen suka dawo daga unguwar da suka tafi suna cikin mota akan hanyarsu ta dawowa ala'meen yace bari in kira yarinyar nan ince mata gamu nan zuwa zan d'an zaga daita yawo sai mu koma gida .