← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 99

Sashe 51

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama tashigo gidan Tana yatsina fuska Inna ta dubeta Tana yi mata sannu "kin gaji ko Daman ziyara haka yake dole ki gaji baki saba ba "wallahi Inna duk na gaji garin nan naku akwai Rana "Inna tayi murmushi in go nan tayi mata dakuwa ,"Allah yasa dai kema garin naku ne Kuma inshallau acikin garin Zaki karasa rayuwarki "Kai Inna ina zan iya rayuwa anan ,ku dai daya zamemu ku dole kuyita fama, mu ma dinga zuwan muku ziyara ta k'arasa maganar Tana shigewa d'aki dayake Bata fahimci inda zance Inna ya nufa ba ....

Daddare ala'meen yashigo gidan yasa mu Inna Tana zaune akan tabarma yayinda muwaddat ke kwance akan gadon Tana rike da waya da dukkanin alamun chatting take, bayan sun gaisa da Inna ya waigo inda take kwance ya Kira sunanta..muwaddat

Ta yatsina fuska sannan tace na'am '"ki shirya gobe da wuri saboda fitar asuba zamuyi "to kawai tace Masa atakaice Tana juya Masa baya ..

Inna tayi kasa da muryarta can ta yadda muwaddat bazata jiyota ba "wai yana ga Kamar kana jin tsoron yarinyar, ka fad'a mata abinda ke ranka mana Kar fa wani yayi maka shigar sauri, duk da dai tunda tazo Banga Wanda ya kirata ba, ko ita takira ba ,bayan iyayenta "girgiza Kai yayi "ba yanzu ba tukunan Inna "
"ya dai tabbata dai tsoron nata kake ji?
"to kusan haka ne Inna duk lokacin Dana yunkuro zan fad'a mata sai fargaba ta hanani .."ina ganinka jarumi a she kaima lusarina ne bansani ba.... "yanzu meye abun fargaba da jin rsoro anan?
" to Bari ni na sanar da iyayen nata "a'a Inna karki yi sauri yanke hukunci haka ,kinsa fa gaugawa daga sheidan ne, ki Bari mubi komai ahankali ke dai kiyi min addua kawai "to shikenan Allah yasa rabonka ce ,yace "ammen suka shiga wata hira har sanda goma ta buga yayi mata sallama da zai wuce ya k'arasa inda take kwance idanunta a lumshe suke ala'mun tayi bacci ya Dade tsaye akanta Yana dubanta Yana jin sanyi aransa sannan daga baya yasa Kai ya fice ....

*********
Washegari tun safe suka d'auki hanyar komawa ilori d'auke da tsaraba kauye iri iri danginsu daddawa kuka da gasashen kifi sai Kuma dankalin hausa Wanda yazamoto abinda aka fi nomawa kenan agarin kalgo ....
Agajiye suka k'araso ilori saboda mugun gudun dayayi akan titi ....
Suna shigowa harabar gidan idanunta ya sauka akan muhammed auwal zaune akan motarsa Yana fuskantar kofar tafkeken get din gidan yana ganinsu tare cikin motar yayi wata irin zabura ya duro ya tsaya yana kallon motar zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu.

Ta tsura masa ido har sanda ya tsaya jikin motarsa ya harde hannayensa duka a saman kirjinsa tamkar wani babban mutun ,ahankali ta cigaba kallonsa kirjinta na wani irin mahaukacin bugu lokaci daya hankalinta yayi mugu mugun tashi ,kallo daya zaka mata kasan cewar ba cikin natsuwarta take ba ,tana cikin zallar tsoro da abinda idanunta suka ci karo dashi ne, sam batayi tunanin ganinsa a daidai wannan lokacin ba, ba ita ba hatta ala'meen ya d'an samu buguwar zuciya da irin kallon kaskanci dayake aiko musu dashi .

Gaban bunayya ya dinga faduwa ya kura mata tsumammun idanunsa yana kallonta sam ya kasa d'auke idanunsa akanta yana duban abun tamkar a mafarki ,yayi bala'in mamakin ganinta tare da ala'meen, ya fara taku ahankali zai zo gurinta sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi akan gara dai ya cigaba da tsayuwarsa a inda yake zai fi masa alkhairi ,idan ma ya k'arasa inda yake yace mata me ?

Dan haka ya koma da baya ya jingina bayansa da jikin motarsa ya cigaba da kallonta ,Kallonsa take yi itama cike da matsanancin tsoro sannan a matukar kidime tun daga kasa har sama kirjinta na bugawa, zuciyarta kuwa kamar zata fito daga cikin kirjinta .
Gabadaya halitar jikinta babu inda bai amsa ba .
Da kyar tasamu ta yunkura ta zata fito daga cikin motar dan tuni ala'meen yayi parking taji sautin muryarsa a kasalance "koma ki zauna tukunna......

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 21

....a matukar firgice ta juyo suka had'a ido dashi ya lumshe mata idanunsa batare daya ce mata komai ba yayinda ita kuma ta dinga dubansa cike da mamaki ," ita yake bawa umarnin ko wata daban ?yadda yayi mugun tsareta da idanuwansa yana kallon cikin kwayar idanunta yasa gabanta yashiga fad'uwa ,tana cigaba da kallonsa cike da tsantsar mamaki "kina mamakin abinda na fad'a ne ?
Ta lumshe idanunta kawai "kar kiyi mamaki ,ki zauna ban baki umarnin fita ba "umarni ta furta ahankali tana kallonsa, yace "Eh akwai batu da nake son mu tautauna dake masu mahimmanci sai data yatsina fuska sannan tace "amman ai kaga yanzu muka dawo daga tafiya ka bari idan na huta ,dan gaskiya ni ..na gaji ,tana gama fad'ar haka ta fito daga cikin motar..
Tunda ta fito kirjinta ke luguden bugu saboda idanuwan muhammed Auwal da take jin suna yawo a gbdy ilahirin jikinta, niyyarta da zarar ta fito daga cikin motar ko kallon inda yake bazatayi ba zata shige cikin gidan ne kai tsaye , amman sai gashi tsumammun idanunsa sun sa ta kasa aiwatar da hakan, ta d'an tsaya Jim kad'an tana kallonsa sannan tayi gaba ta nufi hanyar shiga cikin gidan.

"ayshatul muwaddat "ta tsaya cak kirjinta na bugawa da matsanancin karfi, wanda yasa take kuma jikinta yashiga rawa jin ya sake kiran sunanta yasa ta waigo ta kalleshi " tsayuwar jiran dawowarki nake anan amman shine zaki wuce ki barni tsaye ?

Da kyar ta bud'e bakinta tace "me zan zo nayi maka ?
"kasan dai san wacce kake jira amman ba ni ba ..

a matukar harzuke yace "dole ki fad'a min haka mana tunda kinsamu Wanda yafini matsayi agurinki ,wanda kike so tunda ni dama ba sona kike yi ba ,dole zaki fad'a min maganganun da kika ga dama ,ta runtse idanunta zuciyarta na cigaba da dokawa kana ta bud'esu ahankali tamkar zatayi kuka tace " waye yace maka ina son yaya ala'meen?
" wallahi ni banasonsa, babu wannan atsakaninmu dashi kaine dai kake ganin haka "in har da gaske baki sonsa ki zo wajena yanzu ya ware mata hannuwansa duka biyu daga inda yake jingine da motarsa ,tayi tsaye ta kasa domin jikinta na bata ala'meen su yake kallo, bazata iya wannan kasadar ba agabansa.

"tabbas hasashena ya tabbata kina son shi kamar yadda yake sonki tunda har kika kasa isowa gareni agabansa ?
"Kina son ki kasheni ko ?
tayi saurin girgiza masa kai,
"kina so mana "zo ki kasheni kawai ki huta tunda baki sona...
"ni ..ni fa bance maka ina son ala'meen ba "me zai hana kizo gareni tunda kinsa ni mai sonki ne da kaunarki yayi shiru tare da mayar da jikinsa ya kwantar da jikin mota .."kizo gareni wannan kawai zai tabbatar min da bakya son shi ..

ahankali ta dinga tafiya har tazo daidai kusa dashi amman sai ta kasa k'arasawa jikinsa ta kura masa ido tana kallon fuskarsa Wanda idanunsa ke lumshe yana mayar da numfashi ahankali ,nan take taji sonshi ya dawo mata sabo fil kyawun fuskarsa ya bayyana sosai babu macen da zata ga Auwal bataji tana matsanancin son shi ba, komai nashi daban ne da sauran maza har yau bataci karo da mutumin daya tattara komai irin nasa ba, nan take taji gashin dake kwance a fatar jikinta duk sun Mike tsaye ta tambayi kanta shin Auwal ya dace daita sannan ya cancaci ta so shi kmr yadda takeyi a yanzu ko kuwa ? Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewar shine mutumin daya dace da rayuwarki, Auwal ne kad'ai acikin jininki bazaki iya daina son shi ba saboda da soyayyarsa aka halicceki ,shine mutumin daya cancaci kiyi rayuwa dashi maimakon ta isa garesa sai ta kasa ta tsugunna kasa .
jin shirun yayi yawa yasa ya bud'e idanunsa ya saukesu akanta ta kalleshi , yadda suke dazu har lokacin ma haka suke batasan lokacin data kai hannuta tasoma shafa zarara yatsun kafafunsa masu fitar da sheki na musamman ba ,sannan kwance kowani yatsansa yake da gashi, sai alokacin shima ya bud'e idanunsa yace "Baki San ala'meen ni kike so ...?

Ta d'ago kanta yasa hannuwansa ya dagota ta Mike tsaye adaidai wannan lokacin da tuni ala'meen ya fito daga cikin motar ya shige cikin gida Dan zuciyarsa bazata iya cigaba da kallon takaicin da suke ba ..
hannuwansa duka Auwal yasa ya tallabo kumatunta "did you love me now ?
Maimakon ta masa masa sai kawai taji hawaye masu sanyi sun zubo a kumatunta tare da ajiyar zuciya, ta mayar da fuskarta ta kwantar ajikin hannunsa "zaki aureni yanzu ?

"Bazan iya ba Auwal "don't say that muwaddat "auren irina bawar ne gareki, bakowace mace take samun damar mallakar auren yaro irina ba ,yasa d'an yatsa yana wasa da hawayen dake zuba a fuskarta, tasa hannunta ta d'auke hannunsa ahankali taji ya janyota sosai ya had'eta da jikinsa ya rungumeta tsam ya kwantar da kanta a daidai saitin zuciyarsa dake faman aikin bugawa "ki saurari yadda zuciyata take bugawa akanki ,ina sonki muwaddat wallahi bansan yadda zanyi da soyayyarki ba ,ba kasada nayi ba hakan nan Allah ya jarabeni da soyayyarki karki barni ki aureni plz....ya k'arasa maganar yana sake rurukunkume kmr wand ake shirin kwace ita.

gabad'aya kasusuwan jikinta suka amsa saboda irin rungumar da yayi mata, dan hk babu shiri tasoma K'okarin zare jikinta daga shi bugu da k'ari ta lura yasoma fita haiyacinsa gashi a harabar gida suke, akowani lokaci mutanen gidan zasu iya fitowa uwa uba ga ala'meen na dubansu .
Chapter 51 · 0% Book details