← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 99

Sashe 90

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar take takawa ta fito tana layi hakan yasa ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta "muwaddat Ina zaki cikin wannan hali ?
Ta juya ahankali domin fad'a Masa bakar magana jiri ya kwasheta tayi kasa zata fad'i cikin rud'ewa ya kamota jikinsa ya d'auke cak dan ganin jini a bin kafafunta , part dinsa yayi daita , da kyar ya samu jinin daya soma bin cinyoyinta ya tsaya amman ya Sha wuya sosai, yanzu wani irin son cikin ne ya dawo masa sabo fil ....
Allurar bacci yayi mata domin tasamu natsuwar zuciya, amman ta burkice masa tana zuba masa ruwan bala'i ..

Duk yadda yayi k'ok'arin ya shawo kanta ta fahimceshi amman abin yafi karfinsa, sai faman had'ashi da Allah take ya rabata da ciki ,gabad'aya ya sake shiga rudu ..

yana kallonta ta fice daga bangarensa shima ya biyo bayanta anan suka ci karo da idanun baba mai gadi kallo daya yayi masu ya kawar da kansa yana Allah wadai da masu hali irin su "da al'amun uwarsu bata da lafiya, amman hakan bai saka sun hakura da juna ba, wannan wace irin maseefa ce haka?
yayi maganar a kasan ransa " ko yake zuwa yanzu ya daina ganin laifin su sakacin iyayensu ne ..

Binta bunayya ya shiga yi har ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya sabata a kafad'arsa yayi d'akinta daita ,ya kwantar yana mata sannu , sannan ya koma cikin part dinsa, har kusan magariba yana d'akinsa kwance bai tashi ba tunani Kashi da Kashi ke dawainiyya dashi, jifa jifa ya kan Kiran abi ya tambayi yanayin jikin ummi ,sannan haka ya dinga zariya tsakanin part dinsa zuwa na ummi domin duba lafiyar muwaddat..

Karfe biyun dare muwaddat ta farka daga baccin daya d'auke ta ,yana zaune akusa daita ya zuba mata ido, hannushi cikin nata jin motsin datayi ne yasa ya gane ta farka da sauri ya mike yana Kiran sunanta muwaddat, sai ma ta rufe idanunta wasu zafafa hawaye na zubo Mata babu irin maganar da bai mata ba amman ta shareshi band'aki ya shiga ya had'a mata ruwan mai d'an dumi zuwa yayi zai d'auketa duk da Jikinta babu kwari sai data fixge tana zabga masa uwar harara "bana son jin hannunka ajikina na tsaneka ka rabu dani ..
Kuka ne yaci karfinta, jin kukan nan yake har cikin zuciyarsa ya kasa ce mata komai "

Can kusan minti goma yace "plz muwaddat kina bukatar kulawa da taimakona a daidai wannan lokacin ..

"Banason ko wani iri taimako ne daga gareka ka barni na mutu na huta da wannan bakinci ," komawa tayi tayi kwanciyarta, har kusan asuba yana fama daita tana jin Fitarsa matsalaci ....

Koda ya dawo ma kusa daita ya tsaya ,ban da hawaye babu abinda idanuwanta ke zubarwa cikin sanyayyiyar muryarsa yace "Dan Allah muwaddat na rokeki ki bar kukan nan haka kada yayi miki illa "
"Yaya kuke son nayi, gaki tashin hankali gurinki ,ga matsalar ummi ,Ina bukatar kowane daga ciknku arayuwata ,bana son ba rasaki "kiyi hakuri muwaddat ki d'auka kaddararmu ce tazo haka ...
Gefe ta juyar da kanta "ka rabani cikin Nan ni banaso .......

Shiru yayi kawai had'e da kafeta da tsumammun idanunsa ,yau tazo Masa da abubuwa dayawa tashin hankali da rudani , gabad'aya duniya ta cakud'e mashi waje d'aya ba ta bangarenta ba, bata bangaren umminsa ba ,bai ta'ba sanin haka tashin hankali irin wannan daya ke ciki yake da ciwo ba , "ya zai yi da kaddara data afka masa?
" d'an da zai fara samu a duniya shine yazo ta wannan hanyar ...."

Cike da muryar kuka tace "dan Allah ka rabani da cikin tun kafin ummi ta dawo ,na had'aka da Allah ka ci ....

"Dan Allah dan annabi malama ya isheki "

"enough muwadda "
" Wai ma me kika d'auke ni ne ?
"Mahaukaci ko me ?

"Nasan na aikata zina dake na tsawon lokaci har ga sakamakon nan ajikinki ,amman wallahil azim bazan iya zubar da wannan ciki ba ....
"Bazan iya d'aukar wannan zunubin ba ...
"bazan iya kashe kiyashi ba ,bare gudan jini ...... I can't muwaddat Yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuuuuuuu cikin tashin hankali...

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 40

....shiru ne ya ratsa gidan tun sanda su ummi suka baro parlour'n , abi dake zaune akan kujera mai zaman mutun d'aya ya rafka uban tagumi, gabad'aya abun duniya ya dameshi ,ya kasa tashi daga zaunen da yake, mafuta kawai yake nema da tunanin wanda zai tautauna matsalarsa dashi akan bakon lamarin daya samesu .

a qalla ya kusan minti talatin zaune agurin yana tunanin mafuta , mutun na farko da zuciyarsa ta bashi umarnin ya nema ,shine d'an'uwansa umar ,batare da 'bata lokaci ba, abi ya mike cikin hanzari ya nufi d'akinsa yasoma neman layinsa .

Bugu d'aya biyu uncle umar ya d'auki wayar bakinsa d'auke da sallama byn sun gaisa ne abi ya shiga sanar masa abinda dake faruwa a gidansa , take zuciyar uncle umar ta tsaya na wunci gadi , a tsaye uncle umar yake amman bai san sanda ya Kai zaune rike da wayar ba tsabar firgici da tashin hankali , har gumi na karyo masa tsabar rud'anin da buguwar zuciyar d'aya tsinci kansa alokaci ,d'aya byn d'aya yake sauraron bayanan abi "abinda ya gudar musu kenan tun farko shiyasa ya d'auke bunayya zuwa wata uwa duniya da sunan karatu ,amnan duk da haka basu tsira ba ...
"Wannan wace irin maseefar rayuwa ce haka ?
"Wasu irin yara ne haka da nacin tsiya ?
ya yiwa kansa tambayar
yana mai dafe gaban gashinsa, Yana sake tuno abubuwan da idanunsa suka ci karo dashi a wancan lokacin ,abi bai boye masa komai ba tun daga farko har kan maganar zuwan iyayen al'ameen da ummi ta tilastashi akan lallai sai ya amshi kayan aurensu, "ni duk cikin lamarin babu abinda ke bani mamaki kmr yadda alhji Mahmud yayi min bakan da zance kmr bai san abinda ake ciki ba ,kwata kwata yayi min shiru da batun auren al'ameen da muwaddat , haka zalika nasan dole yana da masaniyya akan zuwan iyayen yaron amman har yanzu bai ce min komai ba ....

"umar bazan boye maka ba naji haushin wannan shirun da alhj muhmud yayi min ,saboda nasan babu yadda za'ayi ace bai san komai dake tafiya ba ,duk nayi iya tunanina ban gano ta inda ake irin haka ba, ta yaya ma za'a ce...
"Kayi hakuri yaya ,uncle umar ya katse shi ta hanyar fad'ar hk "kayi mashi uziri , ka daina ganin laifinsa, shima wata killa yana jin yadda kake ji din ne azuciyarsa ,shiyasa bai maka maganar ba ,tunda Kai ma akaidance yakamata ka nemeshi akan batun zuwan iyayen yaron Koda shi bai neme ka ba ,yanzu dai ka fara tuntubarshi da zance muji mai zaice ... ..

haka suka cigaba da tautaunawa da Kuma yadda za'a bullowa a'lamarin ,inda uncle umar yace "masa zai shigo kasar da zarar ya kammala da ayyukan gabansa , zai zo ayi komai akan idanunsa ....

Yau tsawon kwanaki uku kenan da faruwa al'amarin , gabad'aya ahlin gidan basu cikin kwanciyar hankali duk wanda ka d'aura idanunka akansa katuwar ramar zaka gani a bayyane ajikinsa , al'ameen kuwa ya Kira layin muwaddat har ya gaji wayar bata shiga ,ai kuwa hankalinsa yayi kololuwar tashi ,sai daya Kira ummi ne take ce masa wayar ce tasamu matsala amman tana gurin mai gyara, sannan ya d'an samu natsuwar zuciya, da hakan nan ya tsinci kansa da jin cewar akwai damuwa ga wani mummunar fad'uwar gaba da yake fama dashi ..

******
muwaddat durkushe agaban ummi , har lokacin ta kasa saida hawayenta, kamar ummi itama hawayen yaki tsayuwa a idanunta, muryarta cike da kuka tace "ummi ki taimakeni ki taimaki rayuwata ki zubar min da cikin nan wallahi bazan iya haihuwarsa ba ......

ummi ta numfasa tana sauke naunayen ajiyar zuciya tace "kinsa da haka kika biyewa kaninki kuka aikata abinda kuka aikata, "a shekaranjiya zuciyata cike take fal da son zubar da cikin jikinki amman ahalin yanzu ba zan iya ba.
" ban ta'ba cire ciki arayuwata ba a tun sanda na soma aiki ba kuma zan soma daga kanki ba ,haka zakiyi hakuri ki haife abinda ke cikinki , sakamakonki kenan da zaki girba akan biyewa son zuciyarki , ni yanzu yadda zan fuskanci d'anuwana da wanna batun ne yafi damuna ,ta k'arasa mgnr tana matso ruwan hawaye daga idanunta, nayi danasani nayi nadama mara iyaka arayuwata ,da wani ido zan dube d'anuwana na fad'a masa wannan abun kunyar .. ?
Cike da sanyi jiki muwaddat ta mike ta nufi d'akinta tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya .

*******
Bunayya yayi k'ok'arin ya fahimtar da muwaddah wasu abubuwa a game da cikinsa dake jikinta dan baya bukatar rasa shi ,domin kuwa shine karfin gwiwarsa a halin yanzu,amman taki bashi wannan damar ,sai dai kallo d'aya zaka mata ka tabbatar da bata cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankali, duk ta fige acikin kwanaki had'u kacal saboda damuwar data d'aurawa kanta ..
Chapter 90 · 0% Book details