← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 99

Sashe 32

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace" ummi wallahi a koshe nake ban dade da cin abinci ba na fito , nagode sosai da kulawa Allah ya k'ara girma yayi gaba M.A na biye dashi a baya suna zantawa har bakin motarsa M. A yayi masa rakiya yashiga motarsa ya tafi shi kuma ya dawo part din ummi da niyyar cin kaniyar muwadda har zai haye bene sai yaji abi ya kirasa yana d'an juyo ahankali yasoma lokaci daya kuma yasoma jiyo kamshin turarenta mai tsuma zuciya da kashi jiki ya waiga hanyar step itace ke saukawa tana rausaya sai dai fuskarta a had'e tazo ta wuceshi ta zauna kusa da ummi ,abi ya numfasa yace "ni kuwa bunayya sai nake ganin abokinka nabeel yana dama dama da diyata ko dai shima yana son ayi yar gida ne?

M. A ya fad'ad'a murmushinsa yace "kai abi shi ya soma wannan dayen aikin ,bare ma bai ce ba ,sai dai idan ana so ayi masa tayinta ne, sai mamanta ta shirya masa toshi akai masa dan naga kmr tana yi dashi ,gbdy suka kwashe da dariya ban da muwadda dake aika masa da wani shegen kallo ,takowa yayi ahankali har inda take zaune yace "ke yarinya kallon wulakacin me kike min?
"tunda baki son tsofaffin samarinki ,baki son yaro irinmu, ai kya so nabeel tunda shi ya girmemin nesa ba kusa ba ....

ki hanzarta fad'awa mamanki ta tanadi gida da mota har ma da kujerar hajji matukar nabeel za'abawa ke saboda shi daman ya'yan manya irinki yake son aure ..
ummi tace "tafi can makwad'aitan banza ,baku kawo ba kuna neman abaku saboda mutuwar zuciya"no ummi ba haka bane yanzu zamani ya canza ririta maza akeyi fiyye da tunaninki "to banda diyata wallahi ta k'arasa mgnr tare da cewa ga abincinka can kan dining table amman bansani ba ko a d'akinka zakaci..

"anan zanci kai tsaye ya nufi table din cin abinci ya d'an ja kujera gabansa ya xauna sai daya bubbud'e yaga abincin da'aka shirya masa sannan yace " muwaddat taso ki xuba min abinci .

"baza'azo a zuba ba, kar Allah yasa kaci "da kuwa kin jawowa kanki matsala dani yarinya ,kin dai san hali...ummi tayi saurin cewa tasan hali me zaka mata ?

"No ummi babu ruwanki wannan tsakaninmu ne muddin batazo ba tasan abinda zamanta ko babyn mamanta?
sosai ta fahimci inda manufar zansa ya nufa ,kar yazo ya hanata bacci daren ,dan hk ta mike domin k'ok'arin isa inda yake ta tsaya tana tmbyrsa abinda za'a zuba masa ,ummi tace "wallahi muwaddat duk kece kike biye masa shi yasa ya rainaki banci haka yaushe .....
abi yace "uhmmm babu ruwanki tsakaninsu ne.

M.A ya nuna mata kalar abincin dayake so ta zuba masa yana duban fuskarta yana shafa saman kafarta da tafin kafarsa nan take jikinta ya kama rawa cikin sauri sauri ta zuba masa ta juya ,bai ce mata komai ganin har lokacin idanun ummi na kansu , yaja plet din abinci gabansa ya fara ci yaso kwarai yana cin abinci yana kallon kyakkyawa fuskarta amman yana d'agowa gefen dayafi tunanin zata zauna yaga wayam ta bar parl tun, daga lokacin bai sake d"aura kwayar idanunsa akanta ba har dare , cikin dare yayi k'ok'arin zuwa d'akinta koda yaje yaji kofar a kulle ....
Yana barin bakin kofar d'akinta bangarensa ya nufa duk yana jinsa wani iri iri yaso had'u daita ko dan ragewa kansa sha'awarta dake makale azuciyarsa, haka ya kwanta ya kunna wayarsa yana kallon nonuwanta yayinda hannuwansa duka ke kan joystick dinsa yana lumshe ido da kyar yassmu bacci yayi nasarar daukarsa cike da tunaninta.

********
washegari da misalin karfe takwas na dare byn ya gama duk wani shirinsa part ummi ya nufa domin ya sanar mata da damuwarsa akan muwaddat ,bakinsa d'auke da sallama yashiga k'aramin parlour'n ,ana ya iske abi zaune yana shan coffee yana sauraren labarai ,ummi na zaune a gabansa ,hannunta akan kafafunsa tana yi masa masaging ,atare suka amsa masa sallama cike da matsanancin farinciki, kullun idan suka kalli tillon d'an nasu sai su rasa abinda ke musu dadi ,tabbas ya'ya rahma ne ga rayuwar iyaye ,Allah dai yabamu masu albarka.
Shigowarsa bai sa ummi ta cire hannunta akan kafafun abi ba sai ma cigaba datayi da abinda take masa,shi kuma yana lumshe idanu..

Ahankali M.A ya k'araso ya zauna kusa da abi tmkr zai shige jikinsa cikin fara'a abi ya kai hannunsa ya shafa kansa yace "babana ya'akayi ne ?
M.A ya sune kai tare da Sosa keyarsa alamar jin kunyar ummi ,parlour'n ya d'an yi shiru ,can abi ya waigo ya dubesa sannan yace "bunayya kayi shiru ina fatan dai lafiya ko akwai abinda kake so ne ?
Ya jefa masa tmbyr duk da yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki ,M.A ya shafa fuskarsa sannan ya d'ago cikin yanayi na rud'ani yace dama..daman ina so ..sai kuma yayi shiru saboda idanun ummi dake kansa..

Murmushi abi yayi yace "relax my son kwantar da hankalinka ni mahaifinka ne ita kuma wannan mahaifiyarka ce ka saki jiki kayi mana magana muna sauraronka, wani irin numfashi yashiga fitarwa mai zafi saboda tunanin yadda ummi zata amshi mgnr agabansa ..

Abi ya sauke naunayen ajiyar zuciya sannan yace "hakika bunayya zaka aikatawa abi da umminka babban kuskure matukar ka boye musu damuwarka ,zanji babu dadi araina Amman babu komai kana iya tafiya idan baka shirya gaya mana mataslarka ba muryarsa a kasalance yace "abi daman magana nake son yi da ummi ..abi yayi shiru can ya numfasa yace "to shikenan bari na tashi na baku guri ya yunkura ya Mike tsaye yana murmushi ya bar musu d'akin .
byn fitarsa ummi tace "ina jinka meye matsalarka?
Natsuwa ya Nemo ya sanyawa zuciyarsa dama gangar jikinsa sannan ya fara mgn cikin murya tausayawa "ummi daman akan muwaddat ne ,wallahi ni dai har ga Allah ina sonta kuma da aure na fad'awa abi shine naga kema yakamata na fad'a miki ......
ummi tayi shiru kawai tana kallonsa cike da matsanancin mamaki can ta numfasa had'e da kiran sunansa Wanda wannan ne karon na farko tunda aka haifeshi bata ta'ba kiransa da Auwal ba, "auwal ni aganina Kamar kayi kankanta a batu na soyayya bare akai ga batu na aure ,yanxu fa kake 22 a duniya ,ba soyayya ce ta dace da kai ba ,karatu ne yafi dace da rayuwarka , muwaddat kuma da kake kwakwar so bazan baka ita ba saboda kayi mata kankanta a aure, bama haka ba, bana dai son nayi muku auren kuruciya ne daga kai har ita yara ne gara tasu wanda ya girmeta mai hankali ..

Ya dubi ummi kmr zaiyi mata kuka yace " ummi ki daina tunani haka ,nima mai hankali ne, duk abinda kike tunani na kuruciya bazanyi arayuwar aurenmu daita ba,"kai dai ka hakura kawai banason naci..
kansa ya sunkuyar kasa "bazan iya hakura daita ba ummi saboda ni kaina a halin yanzu nasan ba soyayya bace ta dace da rayuwata ba ,Amman bansan yadda akayi zuciyata ta farka wannan alamarin mai wuya misaltuwa ba ,zuciyata batayi shawara dani ba ummi da sam bazan kamu da soyayyar abinda nasan zai wahalar dani ba ,sai dai babu yadda zanyi na d'auki abun a matsayin wata jarabawa ce daga Allah, Dan girman Allah ummi ki amince ki yarda ki bani auren muwaddat ,ni ita kadai ce araina ita nake so ,duk rayuwar da babu ita to babu Auwal .....

"Ni dai ba zan yi wannan had'in ba, ka hakura ka cigaba da karantunka .. yana jin ta fad'i hk yasan ba yarda zatayi ba ,shi ya rasa dalilin dayasa batason aurensa da muwaddat ,Sam bai d'auki hujarta tacewar suna da kuruciya ba zuciyarsa tafi zargin wani abu daban .mikewa yayi ya bar parlour'n jikinsa a sanyaye, tabi bayansa da kallo har sai data daina ganinsa "shiru tayi byn fitarsa, saboda ta lura mgnrta ta haifar masa da damuwa "me yakamata tayi ?
"idan ita ta amince da aurensu ita muwaddat din fa?
" kwata kwata bata ga wata alamar tana son shi ba, illa shakuwar dake tsakaninsu mikewa tayi cikin sanyi jiki ta shiga bayi tana zance zuci . ...

*********

washegari tunda sanyi safiya direban alhji ishaq ya d'auki muwaddat a mota suka d'auki hanyar ilorin, tunda suka hau babban titi ibadan, ba abinda direba yake sai sharara gudu.

muwaddat ta kwanta abayan mota tana tunanin rayuwar dazatayi a garin ilori kafin ta dawo, hkn nan yau ta tsinci zuciyarta tana murna ganin mahaifiyarta da kannenta sa'banin lokunta baya da bata son zuwa saboda takurawarsu gareta akan abinda tafi tsana arayuwarta .

yayinda kuma wani bangare na zuciyarta yake cike da matsanancin kewar muhammed auwal dinta..
"amman duk da hakan tana dokin nesanta kanta daga gareshi ,sannan da d'okin ganin 'yan'uwanta taji dadin yadda ummi tace sai tayi watanin a can kafin ta dawo sam ranta bai 'baci da hukunci ummi ba , gara tayi nisa akan tacigaba da rayuwa tare da auwal yana tsuma zuciyar da tsumammiyar soyayyarsa da bata hango nasarar komai acikinta..

runse idanuwanta tayi "Allah sarki ko ya zai ji idan ya dawo ya iske bana nan?
ahankali zuciyarta tashiga hasko mata irin bori da haukan da zai yi, tayi murmushi kawai "my trouble auwal ....ta furta hkn tana bud'e idanunta.
Allah Allah ta dinga yi ta ganta a ilori wurin mahaifiyarta da 'yanuwanta ko zata ragewa zuciyarta damuwar datake ciki..

sun isa garin ilorin da misalin sha biyu da 'yan mintuna ,mai gadin gidan ne ya fara yi musu maraba yana ganin motar gidan alhaji ishaq, ya hamgame tafkeken get din gidan, direban ya danna hon tare da dannan hancin motar cikin harabar gidan.
direban nagama tsaida motar ,nan da nan sai ga yaran gidan suna ta fitowa da gudu zasu zo tarar auntynsu, eiman ce takaraso da gudunta tazo ta rungume muwaddat tare da fadin "tun daxu muke ta zuba ido ,muyi waya lagos abi yace tuni kun taho kuna hanya "

muwaddat tayi murmushi tace "muna hanya wallahi sai yanzu Allah ya yi isowar mu, ince dai dady yana gida?
"baya nan sun tafi kalgo da yaya al'aemeen da yaya akram da aunty faiza .
Chapter 32 · 0% Book details