← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 99

Sashe 36

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**********
da misalin karfe takwas na dare yana zaune a parlour'n yaya akram sanye cikin wasu haddun fararen kayan bacci ,riga da gajeren wando iya cinyarsa ya lankwashe kafarsa daya ,yayinda dayar kafarsa ke mike yana karkad'ata ahankali ahankali, system ne agabansa yana duba sakonin yayinda sauran yaran da suka shigo d'akin tare tuni sun koma bangaren mumy ,ita kad'ai ce ta kasa ta tsare taki barin parlour'n, tun sanda tashigo take kallon TV ta kasa yi masa magana saboda fargaba, domin kallon fuskarsa kad'ai ya isa ya saukarwa mutun da kasalar kasa furta komai garesa , yayinda a zahirin km kacokan hankalinta da natsuwarta suna kansa ne tana lura da duk wani motsinsa..

wayarsa dake gefensa ta d'auki k'ara sautin mai dadi ,faiza dake zaune a gefensa ta kai hanuta ta d'auka ta mika masa,yaki d'agowa ya karbi wayar a hannunta har sai da wayar ta tsinke wani kiran ya sake shigowa sannan ya mika mata hannu batare daya kalli inda take ba, yana amsar wayar ya tsura screen din wayar ido yana kallo, sunan abokinsa nabeel ya gani yana yawo akan screen din wayar, sai daya numfasa kana ya manna wayar a kunnensa batare daya ce masa komai ba.

bangaren nabeel kuwa yana jin ya d'auka yace "ya'akayi ne friend nazo gida ban sa meka ba ina ka shiga ne?
M. A ya furzar da iska daga bakinsa yace "wallahi bana nan ina ilori, but cikin satin nan zan dawo,ahankali suka shiga hira atakaice, sannan sukayi sallama ya katse kiran ya ajiye wayar ya cigaba da abinda yake..

Cike da sanyi jiki faiza ta matso kusa dashi zata fara damunsa da shirmenta na banza ya d'ago kansa da sauri suka had'a ido, yadda bai d'auke idanunshi cikin nata ba haka itama ta kafeshi da manya idanunta farare tas ,dan ita fara ce sol kalarsa, alama yayi mata da ido da ta bar gurin.

amman faiza ta kasa aiwatar da umarninsa saboda wani irin zazzafan soyayyarsa dake fixgarta ahankali ta lumshe idanunta tana jin wani iri sabon kaunarsa na sake shigarta cikin sananin damuwa tace " dan Allah yaya ka barni a kusa da kai mana, zamana tare da kai yana k'ara min karfin gwiwa da yaye min damuwar da nake ciki ,ina sonka yaya ,ba tun yanzu ba kasan da haka ,ina sonka tun bansan ciwon kaina ba ,kayiwa Allah ka duba lamarina nima ,ka daina nuna min kiyayya irin haka kasancewata mace ,ina da rauni bazan iya juriar wannan tsanar daga gareka ba ,a duk sanda kake min kallon tsana ina jin tamkar na kashe kaina ne .. ta karasa mgnr
Idanunta suka ciciko da ruwan hawaye, "kasani ba laifina bane , nima tsintar kaina nayi cikin tafkin kaunarka Wanda nake jin bazan iya rayuwa babu kai ba ,na sha gaya maka yadda nake jin sonka a zuciyata ....

"ba sai kin tunatar dani soyayyarki ba ya katseta ta hanyar fad'a mata hk ,yacigaba da mgn a tsanake yana kawar da fuskarsa " ina son kisan wani abu faiza,sam ba kya cikin zuciyata da duniyata gabadaya.. asalima ni yayarki muwaddat nake mutuwar so ba ke ba ,dan haka wannan yazamo karonki na karshe da zaki zo min da wannan banzar maganar, dan bazan iya auren duk macen data fara furta kalmar tana sona ba, wannan tsarina ne ba kuma zan sauke shi ba, bare akan ke da bana sonki ...

Muryarta a matukar raunane tace
"Nasani ,nasan baka sona amman kayi la'akari da wasu abubuwa nima ina da ....
A matukar tsawace ya katseta ta hanyar furta "short up there karki tozarta kanki abanza dan bazaki ta'ba samuna arayuwarki ba, and get out of this room now
,bana son sake jin komai daga bakinki , bana son sake d'aura idanuna akanki ......
babu musu ta mike sum sum ta fice daga d'akin tana jan tsaki .
kai tsaye tana shiga part din mumy d'akin muwaddat ta nufa tana shiga ta zauna kusa daita tana share hawaye.. muwaddat ta waigo da sauri tana dubanta hankalinta a tashe "lafiya faiza me ,yasameki kike kuka .. ?
Girgiza mata kai kawai faiza tayi tana ganin duk duniya babu mai sa'a kmrta tunda yaya bunayya ya furta ita yake son.. yin duniya muwaddat tayi daita ta fad'a damuwarta amman faiza taki jikinta na rawa ta mike zata bar d'akin
faiza tayi saurin riko hannuta "ina kuma zaki aunty ?
"babu fa abinda ke damuna " wai da mumy zan kira"
faiza ta girgiza mata kai "karki kirata dan Allah mumy zata matsa min ni kuma ban san abinda zance mata yana damuna ba,"yanzu faiza har akwai abinda zaki iya boye mana?
"duk duniya fa mu yafi dacewa mu san damuwarki amman tunda hk kikace babu komai ta nufi bayi ta barta zaune..

***********

abun mamaki tunda al'ameen ya d'aura idanunsa akan muwaddat ya rasa samun kwanciyar hankali duk inda muwaddat take yana gurin yana barkwanci da kannenta Wanda kusan wannan abun nayiwa muwaddah dadi, dan duk mai son kannenta tana sonshi uwa uba yadda yake girmama iyayenta tare da mutuntasu .

Tsaye take a kitchen tana taya masu aiki ayyukan girki bisa umarnin mahaifiyarta ,domin ta koya, dan taga alamun bawani girki ta iya ba,ranta bai so shiga kitchen din ba, amman da yake tana shakar mahaifiyarta babu mutsu ta ware ta shiga cikinsu tana koyan nau'ikan abinci ,wani lokacin in ta takarkare tana girki har dariya abun yake bawa hjy hajara, domin ganin bata saba ba ,dady ma da kansa yake lekawa kitchen dan yaci dariya ko yaya yaga tayi aiki sai yace "ta taho ta huta wai tagaji bazai bari ta wahala ba ,dan yar amana ce, aiko haka za'a tasata gaba da dariya ,shi kuwa al'amen bai San tana shiga kitchen ba sai ranar da safe yashiga neman ruwan zafi sai yaganta acikin kitchen tana suyar dankali ,yan aiki guda biyu na zagaye daita azumi na fere dankali yayinda ita kuma tabawa take yayyankawa dadaffen dankali tana mikawa muwaddat tana tsomawa cikin kwai tana soyawa ,abun yayi matukar bawa ala'meen mamaki domin da gani yasan muwaddat yar gata ce ta karshe ,babu yadda za'a yi asa irinta wannan aikin wahalar a gidansu yana shiga kitchen duk ma'aikatan suka gaisheshi sannan itama ta gaishe dashi daga nan ta d'auke kanta ta cigaba da aikin da take ,dan daga inda take tsaye tana hango Auwal daya zauna rashe rashe kmr wani babban mutun yana kallonta ,tun zuwanta gidan babu abinda ke had'ata da al'amen ,ban da gaisuwa asalima ko surutu yake da yaran gidan bata tsoma musu baki ciki ,ballanatana yanzu da Auwal yayi kaka gida ya kasa ya tsare wani lokacin har mamakin karfin halinsa take yadda yake da maseefar miskilanci da girman kai da Jan aji matukar bada ita yake tare ba bazaka ta'ba jin motsin bakinsa ba,shiyasa tunda yazo gidan babu yaron da ke shiga shirginsa..

ko jiya da ana kallo a main parlour'n din gidan su Iman da faiza suna surutu har ma da al'ameen "ya buga musu tsawa tare da cewa gabadayanku in ba ku rufe min baki ba nida ku ne masu shegen surutun tsiya ,take sukayi tsit dayake suna maseefar tsoronsa saboda tsare gida da kamewa lokacin da momy ta kawo masa abinci ya amsa ya mika mata yace" ta kai masa shima ya Mike zai koma part din yaya akram .

Iman ce tayi karfin halin kyalkyalewa da dariya saboda ganin yadda yaci magani kmr bai ta'ba dariya ba, tace "haba yaya bunayya wai me yasa sai kayita wani cin magani kmr wani zaki , ka saki ranka kawai mu caskare kmr yadda yaya al'ameen yake yi damu .
Yayi mata banza ya nufi hanyar waje, ta cigaba da magana tana jansa da wasa irin na abokan wasa, "kai kamshin abincin nan fa ya doki hancina dayawa yaya in biyoku muci tare ?

Ya juyo da sauri "karki ki kuskura in ba so kike in wurgoki daga matattakalar bene ba '"yana fita daga parlour'n suka kaure da ihu ,yayinda faiza tabi bayansa da wani irin kallo da batasan manufar hkn ba..

ajiyar zuciya ta sauke tana sakar masa murmushi daga inda yake zaune yana aiko mata da harara, tasan duk dan yaga al'ameen ne cikin kitchen din, ta sakar masa hararar wasa itama ta dubi yaya alameen tace " am yaya kana bukatar wani abu ne ?daddar muryarta ce ta ratsa cikin kunnen ala'meen da sauri ya jiyo suka dubi juna amman sai tayi saurin d'auke idanunta saboda wani irin uwar hararar da bunayya ya banka mata yana gargadinta da idanunsa .

Al'ameen ya zuba mata ido sosai saboda maganarta tazo masa a bazata shi duk yadda yake expecting jin zazzakar muryata yanzu dayaji sai yaji ya zarta haka, saboda bawata doguwar magana suke yi ba shiyasa har lokacin bai gama tantace muryarta ba, shi dai yasan tunda yaji yana sonta yasan an jarabi rayuwarsa ..
Cikin rawar murya yace "am daman ruwan zafi nake so Kofi daya muwaddat ta d'an juyo ta dubi M.A tana sakar masa laulausar murmushinta mai kashe zuciya sannan tace "okay bari a dafa maka , ta kai ganinta ga flask ta jijiga "akwai ma acikin flask bari ma na tsiyayo maka .

Girgiza mata kai kawai yayi yana murmushin jin dadin "bar shi kawai kanwata cigaban da aikinki nagode sosai da kulawa na tsiyaya kar na tsaidake.

Tun da yace haka bata sake cewa komai ba ,al'ameen ya tsiyayo ruwan zafi kad'an ya fita daga kitchen ita kuma tacigaba da aikinta ,daga inda take tsaye tana iya jiyo yadda M.A ke sakin tsaki babu kaukautawa ..

Tasowa yayi ya isa bakin kofar kitchen din ya tsaya yana kallonta kmr zai cinyeta ,wannan shine ranar na farko daya doshi inda hanyar kitchen yake a iya tasowarsa ,ya cigaba da tsayuwa shiru yana agurin kallonta fuskarsa a d'aure batare dayayi yunkurin yi mata mgn ba,gabadaya sai taga ya sake mata kwarjini .....

Tsawon minti goma yaga tana yarfe hannunta tare da hura wani bangaren data ji digar mai , take ya lura da konewa tayi ,yasa take hura gurin idanunsa ya zaro kad"an yana cizan gefen lips dinsa kana yace "ba dai konewa kikayi ba garin neman suna ?
Chapter 36 · 0% Book details