← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 99

Sashe 44

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

....yana jin ta kashe wayar gabad'aya ,ya zame ahankali ya kwanata dafe da marasa dake masa zugin sha'awa ,cikin wani irin shauki yasoma juyi akan katifarsa tare da runtse tsumammun idanunsa da suka gama canza kala tsabar jarabar dake cinsa.

kusan awa daya ya d'auka kwance batare da bacci yayi nasarar d'aukarsa ba, illa juyi daya keta faman yi rike da mara, da kyar yasamu ya yunkura ya sauko daga kan bed yashiga bathroom yayi wanka ya fito ya sake kwantawa yana rawar sanyi ,dan jin yayi tmkr wanka da yayi ma sake k'ara masa wani sabon sha'awa yayi, ranar dai kwana yayi yana watsawa jikinsa ruwa ko zai rage jin abinda yake ji,gbdy yayi week, jikinsa yasoma sakewa, numfashinsa yasoma barazanar d'aukewa dole tasa ya sake mikewa yayiwa kansa allurar kwantar da sha'awa sannan ya d'an ji dama ajikinsa har bacci yayi nasarar d'aukesa .

**********

yau tsawon kwanaki uku kenan ala'meen bai sanya muwaddat acikin kwayar idanunsa ba tunda safe kafin ya tafi aiki ,zai so ganinta amman hakan bata samuwa , idan kuma ya dawo shima baya ganinta saboda wasu lokutan da yamma tana kitchen ,ko a parlour sun daina haduwa ,lokacin da yake zuwa parlour ita kuma tana d'akinta makale da wuyar bunayya, dan haka ko yana son ganinta babu dama ,to idan kuma ya aika kiranta yace daita me ?
shi Gabadaya ma yanayinta firgitashi yake da zarar ya ganta yanxu ne gabansa zai kama faduwa ,sai daya kwashe kwanaki wajen biyar bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba, yanzu daya sauko cikin shirin zuwa office yake tambayar eiman "wai me yasa yayarku yanxu bata zaman parlour'n, ko bacci take da wuri?

"Babu wani bacci, kawai dai tana gama cin abinci sai ta shige daki kamar mai yin bacci ,nan kuwa hirarsu suke ita da yaya Auwal a waya ..
Ya d'an zaro idanu kad'an cikin kad'uwa,acikin zuciyarsa yace hirar suke da Auwal ?
"Kwarai kuwa yaya ala'meen, ai sau tare idan kaji tana waya to dashi ne wani lokacin har da dariya zakaji tana yi ,wannan zantuttukan nata yasa ya fahimci ba a zuciyarsa yayi maganar ba azahiri yayita "ai sai ma ka ga yadda suke ji da junansu,, cikinsu duk Wanda bai ji muryar Dan ......
A matukar fusace ya buga mata tsawa "dan Allah malam ban tambayeki duk wad'an nan bazanye surutan ba ,tambaya daya na miki sai wani zuba kikeyi kmr ruwa ,ke kam mijinki nada aiki yana gama fad'ar haka ya juya afusace..

Tabi bayansa da kallo tana ta'be baki "maseefaffen kawai ,ince Kaine ka tambayeni ,ni kuma yazama lazin na fayyace maka komai, idan ma surutu ne ubanwa ya koya min ?
Dubeshi sukai sukai da wuya kamar lagwani ..
ta karasa maganar tana kwashewa da mugun dariya ..
"Yayan kike zagi ,da yiwa dariya haka ?
Taji muryar ihsan daga bayanta "tayi murmushin "ke munafukarsa to ni ba zaginsa nayi ba ...

"To me kikayi idan ba zaginsa kikayi ba?
"Nafa ji duk abinda kika fad'a Dubaishi sukai sukai da wuyansa kamar.. ai da sauri eiman ta matso gaban ihsan ta rufe mata baki "haba yar'uwa so kike yaji ya markad'a min duka ?

ihsan ta cire hannuta a saman bakinta "ai wallahi gara ya lallasaki saboda baki da kunya "to kiyi hakuri yar gaban goshin d'anta na daina ...

A ranar bayan sallar magariba hisham ya ziyarci ala'meen suna samansa suna tautaunawa hisham yace "ni kuwa ina bakuwar gidanku muwaddat madam fa ta dameni da maganarta ..

Al'amen yayi murmushin takaici yana yatsina fuska "ai nima da muke gida daya ba ganinta nake yi ba ...

"Malam cewa zakayi baka so ganinta ba ."wallahi idan dai har zaka yarda yau kwanana biyar kenan ban sata a idona ba ,nima hakan na damu daita Wanda bansan dalili ba gabadaya tunaninta yaki barin zuciyata ta huta ..

Hisham ya buga masa harara "banason maganar banza so dai kawai kake kace min ka fara sonta cikin murmushi ala'meen yace" kusan haka ne ni ban ta'ba tunanin wata yarinya a zuciyata ba sai wannan karon daren jiya fa har kasa bacci nayi amman duk da haka bakaji yadda nake jin tsoron shiga harkarta ba domin na gane take takenta tana da wulakanci..
hisham ya numfasa had'e da cewa
"Abokina ka cire zance wulakanci ai ko tana yi nasan bazata iya yi maka ba ,abinda nake so dai kai, in dai da gaske kana sonta,to kabita a sannu ku saba daga nan sai ka fara nuna mata soyayya, ka tabbata kafin ta koma garinsu ka dasa soyayyarka a cikin zuciyarta ,ala'meen ya sauke naunayen ajiyar zuciya tare da cewa "shikenan sai dai akwai wata matsala fa "
"Ta me kenan ?
"Akwai yaron gidan da'ake rokonta a can,in takaice maka shakuwar dake tsakaninsu tayi yawa , ni sai nake ganin kamar soyayya suke ,duba da yadda zasu d'auki tsawon lokaci a waya suna hira ,kuma idan kaga dariyata ko maganarta da shine, wannan abun na matukar d'aga min hankali fiyye da tunaninka "

"Zancenka zai iya kasancewa gaskiya zai kuma kasamcewa hasashe ne kawai saboda shakuwa babu abinda baya sawa ,sai dai ai last time danazo ai na gansa, ko bawani yaro fari dogo mara kiba mai doguwar fuska da saje mai shegen miskilanci ba ?
"Shine d'an iskan yaro da bai ganin kowa da mutunci in takaice maka har ya gama kwanakinsa a gidan nan kallo arziki ban ishesa ba balle gaisuwa yaro k'arami ya d'auki girman kan tsiya ya d'aurawa kansa, kodan yaga ubansa wani ne oho ?

"Hakan ma zai iya zama sila amman ni yanzu abinda nake so da kai tunda abun yazo hk, ka samu goggonka ka tuntu'beta, kafin kasoma bayyanawa ita yarinyar soyayyarka, idan akwai wani abu a tsakaninsu sai ka janye ,karka soma bayyana mata soyayyarka ace an rigaka kaga kai babu yadda zakayi tunda wata kusan tafi wata "ala'meen yace 'shikenan zan yi haka amman ni sai naga yaron kmr zai wa muwaddat kad'an a batu na soyayya, sai dai idan saurin ido zai yi..

"Kai dai ba wannan bace damuwarka domin kasan namiji baya kad'an a soyayya ko aure idan tana son shi sai kaga anyi musu aure, an jisu shiru ,kafin wani lokaci ya tirka mata ciki. ala'meen yayi saurin runtse idanunsa saboda d'acin kalmar yana daga masa hannu "ya isheka malam ka daina hasasho wannan rayuwar tsakaninsu, kwakwaluwarka ta hasko maka ni ne zan aureta har ma na dirka mata ciki hisham yasa dariya yana nunasa "wallahi ala'meen baka da mutunci yanzu dai kiri kiri ka'ajeye latifa a gefe "ai kama sheida ne ban ta'ba sonta ba kawai darajar Goggo hajara ne , bazan iya cewa mahaifiyarta banasonta ba ,saboda amintakan dake tsakaninsu amman ni Sam Sam ban ta'ba jin ina son latifa araina ba, "shikena yanzu yaya kenan za'a yi, ni gashi madam tace na karbar mata number muwaddat..

Cikin rawar jiki ala'meen yace bari na kiraka maka faiza sai ta sada ka da ita ,ya fiddo wayarsa ya kirata tana d'auka yace" ki turo min muwaddat da ihsan yanzu ina son ganinsu ...

Hisham ya dubeshi "ni da ka hado da eiman na sha dariya ,tare da cewa abokina ni fa ina son ihsan gara kasani ,tun yanzu ina riko tunda kayi min kwacen babbar to zan koma Kan karamar ..cikin Dariya ala'meen yace "kai tafi can babban banza yar kawar tawa danake ji daita zan d'auka na baka alhalin kafin aureta yazo , zakama mata tsufa, Dan bana jin nan da shekara Goma za'a aurar da ihsan saboda akidar son boko da dady yake da ,idan kaji yadda dady yake zuzuta sai sunyi boko sosai sai kayi mamaki ..

"Okay a she dai zaku aurar daita din komai dadewar ,ai na d'auka sai dai ku dinga jikata kuna sha ,sukayi dariya a daidai lokacin da ihsan ta shigo parlour'n had'e da sallama tana gama shigowa eiman ma ta kunno kai da sallama ta d'an kalli hisham tana fara'a ,tace "eye yaya hisham dinmu lallai kana jin dadi har wata kiba da kasuba ka fara ajiyewa, abun yabasu dariya gabadaya al'ameen ya had'e rai yana duban ihsan "ke wace kizo min da wannan shirmamma.. "wallahi yaya bansan ta biyoni ba kawai nima yanzu na ganta "

eiman tace "a'a karkaga laifinta yayanmu batasani ba ,na biyota dan kar ayi ban dani Dan tunda naji ka kira aunty faiza nasan tasamu ne ,sannan ta juya ta kalli hisham had'e da shagwa'be fuska tace yaya hisham "wai tambayar danayi maka akwai shirme aciki ?

"Rabu dashi mun fi kusa ni dake kinsa bata baci atsakaninmu, yanzu manta da wannan yayan naki yaushe zan zo in kai ki kiyiwa minal yini ?
Chapter 44 · 0% Book details