← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 99

Sashe 46

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ilai kuwa abinda zuciyarsa ta kissima masa ne ke faruwa acikin d'akin muwaddat, domin kuwa fad'a ne sosai yashiga tsakanin Auwal da muwaddat ta inda yake shiga bata nan yake fita ba "Dan wulakanci da iskancin banza me ya kaiki d'akinsa ?
Kika bar ni ina kiran wayarki how many hours "wato kin fi damuwa dashi akaina, ke wai ma meye atsakaninki da shi ,?
"waye shi da bazaki d'auki wayata agabansa ba?
"Ni ina nan an tsareni ganina,gani wawa bansan abinda nakeyi ba ke kuma kina can kina shirme da katon banza , Dan haka gobe goben ki shirya zan zo na d'aukoki ki dawo gida zuciyata baza iya d'aukar nauyi nan ba, gara kina kusa dani daman nasan saiko ake son yiwa rayuwata shiyasa aka tsiro da zuwanki wannan hutun ..

"Kema dayake kinsa mugun nufin dake ranki shiyasa kika yi zamanki, bakya ko tunanin dawowa maza daman tun da wuri idan ma sonki yake kice masa kina da miji Dan wallahi babu mai auren ki matukar ina raye ya karasa mgnr yana furzar da iska ..
shiru tayi har yagama balainsa batace masa komai ba ...

Gashi kuma dai suna rike da wayar ,yadda bai yi yunkurin cewa daita komai ba haka zalika Itama bata ce masa komai ba, illa Kunar zuciyar da take, hakika Auwal yayi bala'in rainata wannan wulakanci ko iyayen da sukayi silar zuwanta duniya a yanzu basa mata fad'a irin haka ballanatana shi datake masa kallon kani gareta amman babu Wanda ya janyo wannan tozarcin kamar ita itace silar faruwar haka ta bashi abinda bai cancaci yagani ba ,banci haka tasan babu yadda zai dinga yi mata irin wannan matsefar kamar wani ubanta ..

Ganin tayi shiru taki cewa komai ta barshi shi kadai sai balai yake yi yasa yaja dogon tsaki har sai data yi saurin cire wayar a kunnenta ya fillingin da wayar akan gado batare daya kasheta ba ya sauko daga Kan gadon ya fito kai tsaye part din ummi ya wuce yana shiga ya isketa zaune ita kad'ai tana kallon labarai sallama yayi aciki sannan ya haye sama inda d'akin mahaifinsa yake ,tabi shi da kallo duk yadda akayi ransa a bace yake ",to waye ya bata masa rai ?
Ta tambayi kanta tana runtse ido ,kamar ta Mike ta bi bayansa sai kuma ta fasa tasan da matsalar data shafeta ce dole zai tsaya gareta Amman tunda ya nufi gurin mahaifinsa a sauka lafiya ...

A bakin kofar abi ya tsaya yana kwankwasa kofar abi dake cikin d'akin yana duba wasu mahimman takardun kasuwancinsa yace" waye ?
Muryarsa can cikin makoshi tamkar bai so ta fito tace ".ni ne "abi najin haka yasan kowaye Dan haka ya bashi umarnin shigowa ya tura kofar d'akin yashigo da sallama aciki ,abi ya d'ago ya dubesa yana nazarinsa kallo daya yayi masa yasan yana tattare da damuwa kuma duk abinda ya kawoshi a daidai wannan lokacin mai mahimmanci ne, Dan haka ya tattara takardun dake zube agabansa gefe ya nuna masa gurin zama "ka zauna fatan dai kana lafiya ?
Muryarsa tamkar Wanda zaiyi kuka Dan ma dai nmj duniya ne, kawai ya waske yace ",abi kana son nayi yawanci rai a duniya ?
Da sauri abi ya gyara zama yana girgiza masa kai ",kwarai kuwa Auwal meyasa zaka fadi irin maganar da tasanya gabana faduwa?
"Akan muwaddat ne abi ina sonta kuma da aure, wannan shine karo na karshe da zan furta hakan gareka ka aura min ita ka daina duba kankantar shekaruna, ni aure nake so a halin yanzu "abi ya numfasa yana cigabada dubansa yana nazarinsa tabbas yana hango gaskiyar abinda ya fad'a Amman ta yaya kamar Auwal zaa ace zaa aura masa muwaddat ?

Amman saboda ya kwantar da hankalin yaron yace "shikenan zan duba lamarin sai asan abun yi "zuwa yaushe kenan zaka nemeni kan mgnr, saboda ina son muce tare da ita ne?
"abi yabi shi da wani kallon mamaki kafin daga baya ya kira sunansa "bunayya kasamu natsuwa nace zanyi wani abu akai "bunyya ya ciza gefen lips dinsa kad'an yace "abi to kace ta dawo gida hakan nan nasan kun tura can ne saboda ni ,to wallahi idan bata dawo ba komai zai iya faruwa dani .
ya kamo hannunsa ya d'aura daidai saitin zuciyarsa "abi kaji bugun da zuciyata take ?
"Abi ya runtse ido saboda yaji yadda zuciyarsa ke bugu fastly "shikena zansa ta dawo gobe InshaAllahu zanyi waya da alhji Muhammud yanzu kaje ka kwanta kasamu natsuwa ..auwal ya Mike tsaye yana layi tamkar wani mashayi ya nufi hanyar fita..

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk .....

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 20

....Tun bayan fitar bunayya daga d'akin abi,abi ya kasa samun natsuwar zuciya a game da al'amarin tillon d'ansa,
" a zahirin gaskiya yana jin tamkar ya biye masa ne, yayi masa abinda ya bukata, amman lokacin daya tuna shekarunsa a duniya a halin yanzu sai yaga gabadaya lamarinsa na tattare da kuruciya da sharrin soyayyar farko ne , Wanda mafi akasari akan samun haka acikin wannan duniya .

soyayyar kuruciya mafi yawa matasa na tsintar kansu ciki wannan shaukin mai wuyar misaltuwa Wanda da wuya akai ga cimma burinta,
Dan haka ya ajiye maganarsa amatsayin yarinta da kuruciya ne kawai ke dawainiyya da d'an nasa ,bancin hk ta yaya kamar bunayya zai ce ayi masa aure a wannan lokacin
"auren ma da wace ta girmesa?
tattara zance yayi ya ajiyesa amazaunin wasan yara da kuruciya , ya cigaba da abinda ke gabansa .

Shi kuwa bunayya Ko daya dawo d'akinsa ya kasa samun sukuni, gabad'aya ya rasa abinda ke damunsa, zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, sai zariya yake acikin d'akin rike da kugunsa yayinda hannusa daya ke dafe da goshinsa ,gabad'aya hankalinsa baya gangar jikinsa, 'kwa'kwaluwarsa ke hasko masa wai ga muwaddat dinsa can tare da ala'meen tana masa murmushin nan nata da yafi so da kauna akan komai acikin duniyar nan ,take wani zazzafan kishi ya turnuke zuciyarsa dama gangar jikinsa, ahankali ya runtse idanunsa yana girgiza kai, kirjinsa na wani irin dokawa da sauri " Impossible ya furta a bayyane had'e da bud'e idanunsa ya cigaba da zagaye d'akin ..

"Anya kuwa zan iya d'aukar lokaci batare da na kai kaina gareta ba ?
Anya ba wani abu al'amen yake nufi dashi ba ?
"to wai ma me taje yi d'akinsa a daidai wannan lokacin?
"Ko ba'a gaya masa ba yasan ala'meen son muwaddat dinsa yake, tun da shi ba makaho bane ,dan idanuwansa sun fara hango masa mugun nufinsa akanta ..
Abinda yakamata kawai kaje ka d'aukota ka dawo daita gida shine kawai besty solution da kwanciyar hankalinka gareka ,zuciyarsa ta umarcesa da fad'ar Hakan ,take kuwa ya amince da shawarar zuciyarsa ,ya kudirci aniyar ko bai je gobe ba kamar yadda ya furta mata ba, to kuwa cikin satin sai ya dangana da ilori ,duk ma abinda zai faru sai dai ya faru amman sai ya d'auko abarsa kafarta kafarsa ya k'arasa maganar yana
fad'awa Kan makeken gadonsa da karfi ya kwanta ruf da ciki , yana furzar da iska mai zafi had'e da shafa sumar kansa ,sannan ya kai hannunsa ya janyo wayarsa shiru yayi sakamakon ganin har lokacin wayar tana kan layi ba'a tsinketa ba.

ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana duban screen din wayar sannan ya kai wayar kunnensa ,sautin muryar kukanta ya jiyo can kasa tamkar ta baby yana shiga cikin dodon kunnenshi, zuciyarsa ta cigaba da bugawar da take da karfin gaske, wani irin rad'ad'i ya dinga jin yana sauka akan tsokar dake makale da kirjinsa , runtse idanunsa yayi sosai had'e da Jan dogon tsaki sannan ya katse kiran gabadaya ya Mike ya shiga bathroom...

Muwaddat kuwa har lokacin tana zaune tana kukan bakinciki abinda bunayya yayi mata , kukan ma ba wai akaron kanta taso yinsa ba, ji tayi kawai hawaye na fita daga cikin kwarnin idanunta, tayiwa kanta alkwarin duk runtse babu abinda zai sake shiga tsakaninta dashi, idan mutuwa zatayi da soyayyarsa , sai dai sonsa ya kasheta ,amman babu ita babu shi har abada ko komawa tayi lagos bazata shiga tsabgarsa ba .
tana cikin wannan kukan mumy tashigo d'akin ganin har 11:00 na dare bata fito taci abinci ba .
Tana ganin shigowar mumy tasoma k'ok'arin had'iye kukanta had'e da share hawayenta da sauri ,yayinda ita kuma mumy tana ganin haka ta maida kofar da sauri ta rufe ta k'arasa shigowa d'akin tana kiran sunanta "muwaddat meke faruwa ?
" lafiyarki ?
"kukan me kike?
"Waye ya mutu ko waye bashi da lafiya ?
Tayi mata tambayar gabadaya ajere tana zama kusa daita.

kai kawai muwaddat tashiga girgiza mata al'amun babu komai "ke ki bud'e baki ki min magana, ba wai ki dinga karkad'awa mutane kai ba "me ya faru ,me yasameki ?

Muryata cike da kuka da in ina tace " ba..Babu komai fa" "babu komai zaki zauna kina kuka kamar wace aka aikowa sakon mutuwa, ki gaya min abinda ke damunki ?
Wasu sabbin hawayen suka sake gangaro wa bisa kuncinta , tasa bayan hannunta ta goge tana sake girgiza mata kai .
Hankalin mumy ya sake tashe matuka, tace "wato kina boye min Abu ko ?
Cikin rawar murya tace "Sam Sam ba haka bane mumy ,"kina boye min mana mumuy ta fad'i tana mai mikewa tsaye da sauri tayi hanyar fita domin kiran dady, muwaddat tayi saurin riko tafin hannuta "mumy karki yi fushi dani Dan Allah ,babu fa abinda ke damuna kawai dai ina cike da kewar ummina ne ........
ta tsinci kanta da fad'ar haka wasu siraren hawaye na gangaro mata .
Chapter 46 · 0% Book details