← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 99

Sashe 45

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kafin ta sake cewa wani abu al'amen ya Mike ya korata waje da gudu ta arta tana dariya har da rike ciki ya kalli ihsan yana huci ",ina muwaddat ?
"Tana d'akinta yayi shiru na wasu sakwani sannan yace me takeyi ?
"Gaskiya ban dai sani ba amman bari na duba, ta juya ta fita da sauri ta sauka kasa d'akin muwaddat ta nufa bata sameta aciki ba sai kawai ta nufi parlour'n dady tana ganinta tace "aunty muwaddat wai inji yaya ala'meen kizo ku gaisa da yaya hisham muwaddat ta d'an bata rai "Anya kuwa ni yace miki "kwarai kuwa ke yake nufi muwaddat tayi shiru kmr bazataje ba sai hjy hajara ta galla mata harara ba shiri ta Mike, ita ba gaisawa da hisham bane bata so kawai d'akin ala'meen din ne bata son shiga d'an tunda tazo bata ta'ba yin hanyar bangarensa ba ,amman yau dayake babu yadda ta iya da ranta haka nan ta nufi hanyar tana yin sallama ta yaye labulen parlour'n tashiga..zazzakar muryarta ta doki kunnen ala'meen yadda muryarta ta ratsa jikinsa ko daga bacci ya tashi muryar bazata bace masa ba ,gabadaya suka had'a baki suka amsa sallamar datayi kafin ta gama shigowa kamshin turarenta duk yagama shige musu hanci gabadaya hatta parlour'n ma ya gauraya da kamshinta ,ala'meen dake kishinged'e ya d'an lumahe idanunsa ahankali kana ya bud'esu akanta suka d'an kalli juna kafin daga baya ta kawar da fuskarta hisham na nuna mata gurin zama ta gaishesa sannan ta zauna cikin fara'a kad'an bazakace itace take zagewa da Auwal su raba dare suna zuba surutu ba ,da kyar ta sake bud'e bakinta tacewa hisham" ya gida da madam ?

"madam tana nan lafiya tace a gaisheku suka d'an yi shiru batare da sake cewa komai ba kusan second biyu hisham yace "malama muwaddat me yasa kika da wuyar gani gashi baki son mutane ?
Yanzu da ba Dan na tura a kiraki ba har na tafi bazamu gaisa ba kenan? Murmushin gefen baki tayi "kaga kuma ganina ba wahala garesa ba amman ga Wanda bai kama kansa ba zai wuya ya gani sannan batun rashin son mutane, ni mutane masu shegen surutu ne banaso..

"Al'amen ya jefa mata wani irin kallon da shi kansa bai San yayi hakan ba ,nan Dana ta tamke fuska tana sake kawar da kanta gefe hisham ya cigaba.
hisham yace "shikenan na fahimceki "minal tace ki d'aure ki sake kawo mata ziyara acikin zuciyarta tace "ita idan ta matsu tana son ganina why not tazo ,amman a zahirance cewa tayi InshaAllahu zanje "Kamar yaushe kike ganin zakije ?

Ta yatsina fuska had'e da cewa" babu rana gaskiya amman ina da niyyar zuwa ,sai lokacin ala'meen yayi karfin halin cewa karka yarda da zanceta makaryaciya ce da sauri ta kallesa cike da matsanancin mamakin tare da tsaresa da fararen idanunta "yaushe wannan ya fara atsakaninsu da har zaice mata makaryaciya? kalmar datafi tsana kenan a rayuwarta sai gashi a karon banza a kirata dashi, hisham yayi saurin cewar karyar me tayi maka ?

"Ranar da mukaje gidanka muna dawowa gida sai naji tana bada labarin karya wai taga gidan sarkin garin nan taga gidan gwana kai har gidan zoo tace munje ....
sukayi Dariya hisham yace "ina laifi data kareka.
"ta dai kare kanta dai nasan tayi haka ne Dan kar gaba a sake tursasata fita..

Muwaddat ta d'an Mike tsaye saboda shirmensu ya fara cika mata kunne dole daman tasan hisham zai kasance kmr ala'meen gurin zuba tmkr ruwa ,tunda sai hali yazo daya abota kan zo daya ..hishsm yace "ya kuma kika tashi ana hira ?
"Ni zan koma ciki idan kaje ka mika min gaisuwata gurin madam"

Ala'meen ya fahimci shi take son ta gujewa saboda kallon dayake mata hisham yace "amm madam fa tabani sako a amsar mata number wayarki a she Ranan nan har kuka rabu baku amshi number juna ba muwaddat tace "mantawa muka yi saboda hira ta d'auke mana hankali anan take ta gaya masa number ya shigar dashi cikin wayarsa yace "baki gaya min sauran lambobinki ba dan naji ance layuka uku gareki cikin yatsina fuska tace "ka manta da sauran tunda za'a iya samuna Akan wannan layin ,hisham yace "haba muwaddat ina ganin ko mutun yana rowar number baya yiwa kawarsa ba ,duk yadda yayi muwaddat ta tsare gida ta hanna sauran number's dinta Wanda tabashi din ma ta karamar wayarta ce datake amsa kira Wanda abi ya tsiya mata ,wai saboda koda cajin babbar wayar ya kare, Dan bayason yakirata bai sameta ba ..

shi kuwa hisham Dan dai yajata da hira sai cewa yayi "ke din da nake son ki zama surukata sai gashi kun kulla kawance da daman ..

Da sauri tace wace irin suruka kuma ?
"Au baki da labarin ina rikon ihsan ko?
Cikin dariya tace "da dai faiza kace me yuwa na Dan tsaya maka tunda ita ihsan ai uban gidanta na hannun damanka ne ..

Hisham ya jiyo ga ala'meen dayazamanto tamkar sauna a zaune yana kallonta ",kai maigidana kaji abinda surukata ta fad'a....

Ala'meen yayi murmushi yace ",ai ina ganin ko ita surukar taka a halin yanzu bata isa aure ba bare aje ga faiza ko ihsan, hisham yace "haba babban yaya karka raina min hankali mana kawai saboda ba'ason bani kanwa sai kuma ace yaya ma bata isa aure ba ,kina jinsa dai big sister ya fad'a tare da kallon muwaddat.

Ta d'an kawar da fuskarta gefe "eh to abinda ya fad'a gaskiya ne, sai kaje kayita jiran lokacin idan kaji zaka iya "kenan idan na fahimci ki kenan kin goya masa baya akan maganar sa na cewa kema baki isa aure ba ballanata kanwarki?

Ta sake had'e rai "wannan ai maganarku ce ni dai na tafi ka gaida gida tana shirin fita daga parlour'n sai ga eiman ta biyota da wayoyinta big sister an damemu da kiran wayarki muna cikin kallo an hanamu jin gari ya Auwal yakira wasu ma duk sun kira ni dai nace musu kina d'akin yaya ..........

Cikin matsanancin jin haushi muwaddat tace ",to d'an me zaki biyoni da waya d'akin mutane ,ko ance miki dadewa zanyi ,Muje gani nan saukowa eiman na shirin fita aka sake bugowa ta juyo da sauri "to ga Auwal nan ya sake kiranki .

Cikin tsawa tace dan rashin da'a kai tsaye kike kiran sunansa bako rusunawa ?
Bata amshi wayar daga hannunta ba har kiran ya sake katsewa "oya maza ki koma da wayar idan na sauko zan kirasa ..

"Ni gaskiya ki amshi wayar a hannu , ni yanzu meye laifina bayan agabansa bazan kira sunansa kai tsaye ba "ki ma yi kiga yadda zai yi kaca kaca da namanki Dan kinsan shi baya d'aukar shirme ..

eiman ta marairace" murya big sister Dan girman Allah ki taimaki rayuwata ki amsa kinga na rigada na d'auka da farko ,kinsan Halinsa zai d'auka ban kawo miki bane ...

Gabad'aya daga muwaddat din har eiman a tsorace suke ita eiman najin tsoron kar idan yazo yaci ubanta, Dan bai mantuwa, sannan bai yafiya duk dadewar Abu zai hukuntaka akansa, sai dai idan yagadamar Kyaleka, ita kuma muwaddat rashin sanin abinda zata fad'a masa idan ta ashi wayar take, cikin haka ya sake kira "kin gani ko big sister ya sake Kira Dan girman Allah ki rabani da wayar nan .

Ala'meen kasa d'aurewa yayi yace "shi din waye da baza iya amsa wayarsa anan ba ?

"Batare data juyo ba cikin tausashiyar murya kmr zatayi kuka tace "auwal kanina ne fa, sannan ta amshi wayaoyinta ta bar d'akin cikin 'bacin rai , itama eiman sai lokacin ta saki ranta ,tana sakawar a'lameen murnushin Wanda za'a iya kiransa,Dana mugunta ...

Hisham ya juyo ya dubi ala'meen "ina ganin fa yarinyar nan ta gane kana son yayarsu "kai haba bana ji wannan shirmammiyar yarinyar zata fahimci wani abu ,ita kanta uwar gayyar batasani ba .
"Kana son kace min ita makauniya ce shiyasa bata lura da irin mayataccen kallon da kake yi mata ba ko? Sannan me ka fahimta a yanzu da aka kawo mata wayoyinta ?
"Na fahimci kmr tashiga firgice gabadaya dai ta tsorata "shine abinda na gani gaskiya ka tashi tsaye kar hasashenka yazamo gaskiya,kar yaron yazo yayi kuli kulin kubura da kai akasa..
hisham ya k'arasa mgnr yana dariya ala'meen yace "Allah ma bazai sa ba InshaAllahu rabona ce ...
Hisham ya Mike " to Allah yasa, nima bari tafi Dan na fara tunanin madam Dina nasan tana can tana jirana ala'meen ya hararesa nima dai zanyi madam Dina kodan rashin mutuncin da kake min babu ikon ayi cikakkiyar hira da kai sai ka tsiri cewa madam na Jira .

"to ai gara ni da matar tawa ma ina fitowa kai fa tunda bakuwar gidanku tazo aka daina ganinka ,ai ina jin duk ranar daka mallaki yarinyar nan ,an daina ganinka gabadaya suka kwashe da dariya har da tafa hannu sannan suka Mike tare suka sauko zuwa kasa al'amen yayi masa rakiya ya shiga mota ta tafi shi kuma ya dawo gidan har zai hau samansa sai yaji hayaniyar kannensa acan bangaren dady , sai ya tsinci kansa da nufar bangaren ba Dan komai ba sai Dan ya kalli muwaddat yana shiga ciki ya iske gabadaya yaran gidan suna ciki hjy hajara tacel kardai abokin naka ya tafi tun ba'a kai muku abinci ba yace mumy "ai kinsa halin hisham in da yana son ci da kansa zai tambaya..

Idanuwa yashiga budewa yaga ta inda zai ganta ,babu ita babu alamarta a parlour'n Dan haka ya juya ya wuce ya koma samansa hankalinsa a matukar tashe saboda yasan watakilla tana can tare da Auwal a waya
Chapter 45 · 0% Book details