← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 99

Sashe 62

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Plz muwaddat ki fad'a min mana kina sona ko bakya sona ..?
Kirjin bunayya ya sake bugawa da karfi take jikinsa ya kama rawa kad'an ya rage bai kai kasa ba ,yasamu ya dafa gefen kujera .

"ta runtse idanunta kana ta fixgo abinda zata fad'a masa da kyar "kayi hakuri yaya ala'meen ka bani lokaci zanyi tunanin akai "zuwa yaushe kenan zan baki lokaci?
" wallahi bazan iya d'aukar dogon lokaci batare da nasan matsayina ba .

"ni kawai dai ka bani lokaci zanfi son haka "shikenan na baki lokacin amman zan iya kiraki a waya babu damuwa ?
Tayi shiru can tace "shikenan had'e da zare hannunta cikin nasa, har ta juya ,bunayya ya kira sunanta tana juyowa sukayi four eyes dashi tsaye cikin matsananci tashin hankali ........

take gabanta ya fad'i wanda ya had'e mata da rawar jiki ,tunda ya kira sunanta bai sake magana ba haka zalika bai d'auke idanunsa akanta ba ,wani irin d'aci zuciyarsa ke masa gabadaya ma ya rasa abinda zai ce mata .

parlour'n ya d'auki shiru na tsawon mintuna ,batare dukkanisu sun sake cewa wani abu ba, illa dokawar da zuciyoyinsu keyi ,muwaddat ce tayi karfin halin cewa "ya akayi kanina .... ina 'bata maka lokaci ko?
Wani shuumin kallo ya watsa mata batare da yayi magana ba .

Shi kuwa ala'meen dadin sunan data Kira shi dashi yaji, ko babu komai zuciyarsa ta samu natsuwar dayake son samu a shakuwarsu , domin yanzu dai ya cire zargin da zuciyarsa keyi masa akan alakarsu, yayi murmushi yake yace "bari na baku guri ke da kaninki ,dama zai taimaka min daya bar tafiyar nan zuwa gobe ko wani sati saboda ina son ayi tafiyar dani dan na dinga debi miki kewa dan naga shima Miskilili ne d'anuwanki ko me kika ce ?
bunayya ya jefeshi da wani kazamin kallo me tattare da tsagwaron wulakanci yana furzar da iska domin shi kad'ai yasan irin rad'adin da yake ji akirjinsa , ji yake kamar an dora masa dutsen dala ne a saman zuciyarsa ,kusan wannan bakinciki ne ya hanashi magana ,domin idan yace zai yi maganar ma to babu abinda zai fad'a sai ashariya ..

Ita kuwa muwaddat murmushin karfin hali ta qaqalo tare da cewa"ayi haka kai kuwa yaya ala'meen ,daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki?
"yayi murmushi to ya na iya kamawa tayi ,duk cikin mahimmanci da kike da shi ne agurina, ki bada umarni kawai kiga aiki da cikawa ,yanzu sai na had'o kayana ,ko cewa kikayi idan na biki kar na dawo zanyi zamana matukar ina tare ......
tun bai k'arasa mgnr ba bunayya ya juya a matukar fusace ya bar parlour'n yana Jan tsaki .

Ala'meen ya waigo ya kalleta yana sakar mata laulausar murmushi "wai ni me yasa kanin nan naki ya fiyye shan kamshi ne ?
"Na kanyi mamakin yadda duk da wannan miskilancin nasa amman ke kuna d'asawa dashi ,koda yake ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da zamanku guri daya "muwaddat tace babu laifi muna dasawa dashi sosai, sai dai ni kaina wani lokacin sai mu d'auki tsawon lokaci bamuyi magana ba, idan bashi yayi min ba .
suna cikin haka faiza ta sauko ita da eiman daga d'akin ala'meen .

muwaddat na ganinsu tace "yauwa faiza taimaka dan Allah kije d'akina keda eiman ku had'a min komatsaina, "au daman baki had'a kayanki ba shine baki fad'a ba?"to muje na had'aki miki kinga su sun gaji..inji cewar yaya ala'meen ..

muwaddat tayi murmushi "haba yaya ala'meen ta yaya zan sanyaka aiki irin wannan bayan gasu faiza a gida "to meye Dan kin sani aiki nayi miki ?
"Babu komai ta bashi amsa atakaice saboda ta kagu ta bar gurin gashi shi sai k'ok'arin riketa yake.
Ala'meen ya dubi faiza yace "muje mun had'awa wannan miskilar kanwartawa kayanta.
faiza tace "ka dai kaje ka had'a mata,tunda naga kasoma zaman bita zaizai, nima ina da abun yi kunga tafiyata ..

"suka sa dariya suka nufi d'akin muwaddat tare eiman ,ita kuma ta nufi hanyar waje, suna shiga suka shiga harhad'a kayanta dana tsarabar da mumy tasa ayo mata tun bayan dawowarsu daga kalgo ,suna hira suna shirya kayanta cikin babban akwatinta har lokaci ya tafi sosai, shi kuwa ala'meen yana sane ya dinga 'bata lokaci yana janta da hira dan ya sake 'bata musu lokaci ,domin dai so yake a fasa tafiyar dan ya k'ara samun kusanci daita ....

**********
Bangaren bunayya kuwa iya bakinciki da 'bacin rai zuciyarsa ta kamu dashi ,yana komawa bangarensa yashiga zagaye d'akin yana zariya tamkar Wanda yayiwa sarki karya ya dunkule hannunsa ya naushi iska "aikin banza kawai wai ni za'a kawo bariki ,ai kuwa zaka ga aikin barikanci, ba dai son muwaddat kake bil hakki ba, ni kuwa nayiwa kaina alkawari muddin ina raye ba zaka aureta ba ...
shi bama sonta dayake ne yafi 'bata masa rai ba kamar yadda ya rike mata hannu ,hakan yafi komai d'aga masa hankali da ta'ba masa zuciya, itama km har da wani murmushi take masa tana biye masa dan iskanci, idan yayi magana tace bakinsa na wari ,shi yasan abinda zai yi ,zai dasa soyayyarsa ta karfin tsiya acikin zuciyarta ta yadda idanunta da zuciyarta bazasu ta'ba amsar wani d'a namiji ba bare har ya kai ga ta'ba mata jiki matukar bashi bane ...

yana cikin wannan tashin hankali kiran ummi yashigo wayarsa da kyar ya fesar da numfashi ya d'auki wayar muryarsa can kasa "Assalamu alaikum ya ummi..
daga can bangare ummi ta amsa masa da "waalaikas Salam ya bunaiyya "nace na jiku shiru daga kai har muwaddat babu Wanda ya kirani ,to ya zance tahowarku ?
InshaAllahu yanzu haka muna kan tasowa "ummi tayi shiru can kuma tace "ka kuwa duba lokaci?
Ya kai idanunsa kan agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa karfe hud'u sauran kwata "ummi to four yanzu "to yanzu a irin wannan lokacin yaushe har zaku iso da wuri nifa banason tafiyar dare kubar tafiyar kawai zuwa gobe saboda kwanciyar hankalina.

"no ummi ya furta yana runtse idanunsa domin dai bayason ya k'ara daidai da seconda daya acikin gidan ,gabadaya jikinsa zafi yake masa "addua kawai zaki mana ummi dan oready mun gama shiryawa, tahowa kawai zamuyi .
"ummi tace "ni dai ason raina nafi son abarshi zuwa gobe amman tunda ka nace shikenan Allah ya kawoku lafiya"ameen ummina " bari na kira muwaddat din, yana jin ta fad'i haka ya katse kiran yana furzar da iska.

ahankali yaji ana kwnoking din kofar bai amsa ba ,har sanda ta sanyo gangar jikinta har ta k'araso gabansa ta durkushe bisa gwiwowinta tare da tsura masa ido ,bai d'ago yaga halittar dake gabansa ba, ta cigaba da durkuso tana kallonsa tamkar ta rungumeshi ajikinta, tana jin tamkar ita tafi kowa rashin sa'a a duniya tunda bata samu damar mallakar zuciyarsa ba,
da kyar ta hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi, faiza idanunta taf da ruwan hawaye ta sake tsurawa bunayya ido ,cikin muryar kuka tace in har zaka iya soyayya da yayata wacce ta girmeni ta girmeka, ni mai zai hana ka so ni tunda nima jininta ce uwa daya uba daya?
"gashi ni Allah ya jarabeni da matsanancin soyayarka, nice daidai da kai ba yar'uwata ba, ni yafi dacewa kaso ,ba ita ba ta k'arasa mgnr tana kuka ....

bunayya batare daya d'ago ya dubeta ba, yace "nayi rantsuwa da Allah har yau sama da shekara sha takwas kenan ban ta'ba kaunar wata diya mace ba sai yayarki muwaddat......
" ban ta'ba jin sonki daidai da second daya ba, ni matsayin k'anwata na d'aukeki batu na soyayya babu shi atsakaninmu, muwaddat ce kad'ai acikin kokan raina, ina sonta tamkar raina, ita kad'ai ce macen da nake jin zata kashe min ki shi ruwan danake d'auke dashi na tsawon shekaru.. ..
yana gama fad'ar hk ya mike tsaye ya janyo
Jakar kayansa ya d'auka ya rataya ya kwashe wayoyinsa ya fito harabar gidan kai tsaye inda motarsa kirar lexus, Rk 330 ke parke ya nufa, tun daga nesa ya dannan key'n motar sannan ya isa ya bud'e gidan baya ya jefa jakarsa ciki ,ya nufi cikin gidan yaga uwar da akeyi da ake ta faman 'bata masa lokaci yana shiga a parlour'n ya tarar da duka ahlin gidan suna zagaye da muwaddat banda dady dake cikin d'akinsa sai faiza daya baro a bangaren yaya akram .

Mumy na ganinsa tayi murmushi "ka gaji da jira ka biyo sahu ko ?
"Wai sallama muke ,bai ce mata komai ba haka zalika bai kalli inda muwaddat ke tsaye tare da ala'meen ba ,illa kansa daya daga mata kawai,kana ya juya ahankali ya fice dan bai son ganin ala'meen "ke eiman d'auki jaka daya ki bishi dashi eiman tayi saurin zaro idanu "kai mumuy yanzu nice zan d'auki wannan jakar wacce kmr a zuba kawunan mutane aciki?
" bama wannan ba Allah ni bazan iya bin bayan yaya bunayya ba ,saboda tsoronsa nakeji ...

"Bakiga yadda ya wani had'e rai ba kamar wani bijinmin sa, ta k'arasa mgnr tana sakin dariya " bakiga yadda na kagu ya bar gidan nan ba ,na sakata na wala nayi budurina son raina.....

"Ungo nan jarar kawai akanki yake da zakice kin kagu ya tafi ?
"Ke da yakamata kiyiwa d'an uwanki addua "to ni mumy ai nayi musu addua amman dai su tafi har ma aunty muwaddat din na huta suka sa dariya .
"dan tani yarinya ki kwantar da hankalinki sai kin nemini da kudi ma baki ganni ba "

ihsan tace "karyar iskanci take me yasa batayi magana agabansa ba ,taga yadda zai yi daita .
"to gumaida ,Kanwa uwar had'i ,idan bai ji ba ,ai sai kije ki fad'a masa, ta fad'i haka tana mugud'a Baki.

"ke dai Allah ya shiryeki wallahi mijinki na da aiki ja agabansa, dan duk wanda ya auriki ya auri hauka inji cewar ala'meen ....
Chapter 62 · 0% Book details