← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 99

Sashe 80

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu haka kina sake
' bata lokaci ne ,har sai kinsa ummin ta fahimci wani abu, ki bud'e kofar kawai ta ganmu ,ba sai na fad'a Mata cewar Abi ne yace na taimaka na duba lafiyar ki ba.....

"ni..ni..dai a'a ,ummi nada saurin fahimta abu, hanyar bayi ta nufa dashi tana kuka "muje bathroom dan Allah karka a'a .. suna shiga suka tsaya cirko cirko suna duban juna ,shi kam bunayya ko dar bai ji ajikinsa ba ,asalima tsumammun idanunsa ya tsura mata yana k'ok'arin rungumeta a ajikinsa, "muwaddat ki natsu plz duk kin wani rud'e ,ki samo mana mafuta , ummi fa zata iya shigowa nan is better ta ganni a bedroom dinki akan nan ....
ba tace dashi komai ba, illa hawaye data cigaba da zubarwa tana k'ok'arin barin jikinsa kafin kace me jikinta ya sake d'aukar zafi ,hankalinta a matukar tashe ta fito daga cikin bayin tana kulle kofar tare da Murd'a key ta zare , jikin na rawa ta shiga gyara gadon dan gabad'aya ya hargitse a wasaninsu , ta janyo doguwar rigarta ta Sanya , ta nufi kofar d'akinta wanda zuwa lokacin har ummi ta juya da niyyar zagayowa ta dubata ta window ,tana gama bud'e kofar ummi ta juyo da wani irin sauri ...

Lumshe idanuwanta tai tana saisaita natsuwarra kana ta juya ahankali tana dafe kanta da take jin yana Sara Mata tmkr zai cire tsabar tashin hankali ,fad'awa tai kan gado tana fidda numfashi sama sama ta sake sanyawa jikinka natsuwa .

Ummin ta k'araso da sauri zuwa inda take kwance ,ta tsura mata ido tana kare mata kallo, saboda doguwar ramar data ga tayi, ahankali idanunta ya sauka akan kirjinta gabanta yayi wani irin mugu mugun fadawa kafin daga bisani ya shiga dokawa , kirjinta taga yayi wani irin mahaukacin cikowa , yayi mata hake hake ,numfashinta na sauka ahankali ,girgiza kai tashigayi tana kawar da abinda taji ya tsarga Mata acikin zuciyarta "a taanake tashiga kallon d'akin still zuciyarta na dokawa Wanda ta rasa abinda yasa hk hk Nan take jin tsinkewar zuciyar ...

Jikinta a sanyaye ta samu guri a gefen katifa ta zauna ta d'aga kan muwaddat ta meida kan cinyarta, taji zafin da jikinta yayi ,ya ratsata ,ta dafa goshinta tana kiran sunanta ahankali "muwaddat dina...... ...Sannu "
"shi yasa hankali yaki kwamciya a duk wuni yau ,ashe baby nah bata da lafiya"

muwaddat ta bud'e idanunta da kyar tana duban ummi sannan ta kirkiro murmushin dole tana mikewa da kyar ,ummi tace "kiyi kwanciyarki ma ,ina da ina ke miki ciwo?
"ko kanki ke ciwo ta fad'i hakan, saboda tasan tana da yawon ciwon kai, muwaddat dake atsorace ta rasa mai zatace Mata , kawai ta d'aga mata, saboda ita alokacin babu abinda ke damunta sai tsananin tsoron dake tattare daita .

jikin ummi na rawa tace "okay bari naje na kawo miki magani ki Sha ,wannan zafin jikin naki ya wuce
kaida, ta ajiye kanta akan pillow ta nufi kofar fita cikin sauri ,kai tsaye ummi hanyar d'akinta ta nufa .

cikin wani sauri muwaddat ta zabura ta mike, jikinta na rawa ta bud'e kofar bayi ta janyo hannusa ,suka fito tare dashi tana rokonsa ya fita kafin ummin ta dawo amman kememe bunayya yace "bai zuwa koina , aiko ta d'aura duka hannuwanta bisa kanta ta rushe da wani irin kuka mai ta'ba zuciya ....

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yace "Kinga fa wannan shirmen da kike yi Allah shin zai saka ummi ta fahimci wani abu ,ki natsu ki kwantar da hankali ...ta d'ago da sauri tana kallonsa da idanuwanta da suka gama canza kala tsabar tashin hankali..
Ummi kuwa nashiga d'akinta ta nufi dorowarta dake ajiye magunguna ta d'auko mganin zazzabi da Maleria ta dawo d'akin muwaddat cikin sauri .. turus tayi tana binsu da wani irin kallo mai cike da tambayoyi iri iri .

Muryarsa a kasalance yace" ummi sannun da zuwa,"yauwa Daman kana cikin gidan ne ko yanzu ka shigo ?
Bayan keyarsa ya tsutsa Yana duban muwaddat dake k'ok'arin runtse idanuwanta,kana ta rufe fuskarta da hannuwanta yace "yanzu nashigo "

"Okay to d'an bamu guri zanyiwa baby allura ..lumshe idanunsa yayi yana shafa sumar kansa ,sannan ya soma k'ok'arin ficewa daga d'akin,magani ummi ta'bata had'e da yi mata allura still zuciyarta na cikin taskon Dan har lokacin ummi Bata daina jin fad'awar gaba ba, kwantar daita tayi ,tana sake jero Mata sannu ,kusan minti goma ummi na tare da ita kafin daga bisani ta fito ta sake nufar dakinta .

Ummi na fita daga d'akin ta mike zaune tana d'aga hannuwanta duka sama ta shiga yiwa Allah godiya ,daya rufa Mata asiri ,aranta tayi alkwarin babu ita babu bunayya har karshen ratuwarta, ita dashi sai dai kallon kallo bazata sake barin ya kusanci inda take ba ,tunda yafi kaunar ganinta cikin tashin hankali ,kafin wani lokaci zazzabi jikinta ya sauka, ta dawo normal sai dai yanayin jikinta da take jin shi wani iri kmr banata ba komai a sanyaye take yinsa gashi bata jin dadi bakinta komai taci kmr zata amayar ...

***********

da daddare yaya al'ameen ya kirata sai da ya soma had'ata da 'yan'uwanta suka gaisa sannan suka shiga hira , wanda duk hirar shine ke yinsa amman ita daga uhm sai uhmm, ba wani abu yake fad'a mata mai Dadi ba ,illa sake jadadda mata yadda tayi tasiri arayuwarsa, jinsa kawai take saboda gabad'aya zantuttusa sun isheta ,koma tace haushi suke bata ,km amatsayin shime ta d'aukesu, tana zaune ummi tashigo parlour'n cikin shiga ta alfarma duk yadda ta d'an manyata hakan baya hanata yiwa mai gidan kwaliyya ,bare anyi kwana biyu ba a had'u ba ta fad'i hakan a zuciyarta , tana gani shigowar ummi ta katse kiran,tana duban ummi .

bayan ummi ta samu guri ta zauna ,ta d'an dubi muwaddat, "ke da waye a waya?
"yaya al'ameen ne ta fad'a mata atakaice, ummi ta kai hannu ta amshi wayar tana dubawa sunansa ta gani sannan tashiga bincikar wayar babu komai na aibu aciki dan haka ta mika mata wayar .

"ya jikinki naki yanzu hope you are feeling better ?
ta d'aga mata kai ahankali ,sannan tashiga janta da hira tana
bata labarin yadda bikin minna ya kasance"baby muwaddat idan kikaga yadda binki fadila ya k'awatu abun sai ya burgeki , sai naji ina ma bikinki ake yi ,amarya da ango sun sha kyau har sun gaji , kema dai zuwa yanzu yakamata musan mai kike ciki da al'ameen, yaron nan na da kirki da hankali matuka ,uwa uba yana da natsuwa sannan ya had'a Master's dinsa zaku dace da juna, dan irin miijn da nake miki fatan samu kenan arayuwarki ,wanda nasan kema shine irin zabinki dogon namji kyawawa mai haiba ko ba hk ba?

muwaddat ta had'e rai sosai tana turo baki, ummi ta cigaba "amman ke sai naga kmr kina basarwa a duk sanda aka yi miki maganarsa,ke kowa yazo kice bai yi miki ba gashi wannan shekarar zaki kare karatunki, zan so ki saida miji , da zarar kin gama karatunki musha biki "gaskiya ina sonki da al'ameen sosai sai dai bazan matsa miki ba, idan kinji baki sonshi shikenan sai a bashi hakuri shima kmr sauran ...
muwaddat tayi shiru kawai tana sauraron ummi har tagama maganarta.

ummi ta du'beta sosai tana nazarinta kafin daga baya tace "kinyi shiru shima bazaki auresa ba ko?
kin fi son kiyita ganina ina yawon zuwa bikin mutane, ni kar azo nawa?
muwaddat ta girgiza mata kai kawai ala'mun a'a amman a cikin xuciyarta cewa tai lokacin da nake son aure ba'a min ba ,sai yanzu za'a dameni to ni banason Yaya al'ameen .....

Kmr ummi tasan abinda ke zuciyarta tace "nifa bazan Miki auren dole ba sai Wanda kike so zan baki ,idan baki son shi abar zancesa kawai ,amman idan kin amince kin yarda da auri al'ameen nasan kowa zai ji dadin wannan had'in.

a kasan zuciyarta kuwa cewa tayi "ni auwal fa nake so ummi bawani Yaya al'ameen ba ...,da zaki aura min shi da kin gama min komai ,da na samun duk wani jin dadi duniya ,"auwal shine cikar burina da kwanciyar hankalina, duk wani wanda zaki so na aura ,bazai ta'ba kai min kmr auwal ba......., banason yaya al'ameen din nan wallahi..amman ummi kina neman takura rayuwarmu ..

"tunanin me kikeyi mueaddat kinyi shiru kina jina ?
ahankali ta bud'e bakinta tace "babu komai ummi, tunda kin amince dashi, kin yarda na auresa ,naji na amince zan auresa kawai amman ina son ki min alfamar d'aya ummi?

ummi ta fad'ad'a murmushinta tana murna saboda jin dadi tace "wacce irin alfarma ce wannan mamana?
"ki fad'a min shi, ni kuma nayi miki alkwarin zan yi miki shi muddin bai fi karfina ba, idan bani dashi zan nemoshi matukar akwai shi acikin duniyar nan..

muwaddat ta numfasa ta runtse idanunta saboda d'acin abinda zata fad'a sannan tace " duk abinda za'a yi na aurena da yaya al'ameen har zuwa lokacin da komai za'a kankama , inason ayi shi a boye cikin sirri ummi...

"ta yaya kike tunanin za'a yi maganar aure cikin sirri ?" waye bakyason yasan zakiyi aure?
muwaddat tayi shiru taki magana har sai da ummi ta sake maimaitawa, sannan tace"auwal .....
"ummi banason bunayya ya sani saboda banason yashiga damuwa "bakyason yasani saboda bakyason yashiga damuwa ?
ummi ta sake maimaitawa tana dubanta .
"bakyason yasani ko kema kina son kaninki kmr yadda yake naci ..?
har zatace eh sai kuma tayi saurin girgiza mata kai ,"banason shi ummi amman kuma bazan so na gansa cikin damuwa ba ,ta k'arasa mgnr hawaye na ciccikowa a kwarnin idanunta "ummi tsakanina da Allah banason yaya al'ameen amman tunda kin yarda da natsuwa da nagartarshi wallahi na amincewa zan aurensa ...
,nasan zan so shi daga baya....amman a halin yanzu gsky banason shi...

ummi tayi saurin kamo hannuta tace "anya kuwa yarinyar nan lafiyarki kalau?
"Anya kuwa muwaddat baki da aljannu kowa kice baki so ..?
" tun tasowarki kike samun masoya amman kowa yazo sai kin kawo aibunsa"
"nifa bani da komai ummi kawai dai banasonsu ne ta k'arasa mgnr hawayen da take k'ok'arin makalewa suka samu nasarar zubowa..
Chapter 80 · 0% Book details