← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 99

Sashe 38

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin wani irin tashin hankali ya daka mata tsawa "kina hauka ne da zaki rike min hannu?"ko kin fara shaye shaye ne bansani ba ?
cike da kuzari da karfin zuciya tace " an rike maka hannu me zakayi?
" muhammed auwal bari na gaya maka lokaci yayi da tsawarka ta daina firgitani ,lokaci yayi da kowa dake cikin danginmu zasu san abinda ke tsakanimu da kai ......
tasss tasss taji ya saukar mata wasu gigitattun maruka har guda biyu akan fuskarta "ki kyaleni faiza ...ki rabu dani faiza, tunda nace ki kyaleni ,ki kyaleni mana ko ana so dole ne?
in soyayya ce nace bana yi ana so dole ne?
bari kiji daga yau karki sake takura min akan wannan shirmen saboda bana sonki bana sonki ba kuma zan ta'ba sonki ba ..yana gama fad'ar hk ya juya fuuuuuuu a fusace ya kalleta anan .

tabi bayanshi da kallo fuskarta cike da tsansar damuwa da nadamar rike masa hannu datayi watakilla da bai kai hannunsa jikinta da sunan mari ba, hawayen dake boye acikin kwarnin idanunta suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta, tasa hannu ta goge wasu na sake zubowa cike da matsanancin sanyi jiki ta bi hanyar baya dan kar wani ya ganta cikin damuwa ,most especial aunty'nta muwaddah wacce kwata kwata bata kaunar ta ganta cikin damuwa, koda faiza ta shiga d'akinta sai ta rushe da wani tsumammen kuka ,kwantanta damuwar data shiga baya fad'uwa duk yadda take tunanin M. A ya wuce nan,, ya wuce da tunaninta sam ba itace agabansa ba, "to ita yanzu ya zatayi da rayuwarta.. ?
"hakika bata san yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba matukar M. A yaki amincewa da soyayyarta ,"shin me yasa bazai sota ba ya rabu da aunty'nta tunda itace daidai shi ba muwaddah ba?
har yammanci rana tana kwance a d'akinta taki fito dan batason kowa yasan halin datake ciki ..

zaman M. A a gidan yasa faiza ta nemi takurawa rayuwarsa ,dan kuwa baya samun damar ke'bewa da sanyi idanunsa yadda yake so, duk abinda yake idanunta na kansa ,dan hk a daren ranar daya cika sati biyu da zuwansa ,ya kudurci a niyyar komawa lagos a washegari , lokacin da yake sanarwa dady zance komawarsa tana gurin, aiko taji haushi maganarsa, taji tmkr ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta ta rusa ihu ne dan bakinciki tunda tasan saboda ita yasa zai koma.. ranar dai bata samu ishashen baccin kirki ba sbd tsananin tunanin M. A.
tun da garin Allah ya waye yasa awanke masa motarsa .
yayinda shi kuma yana can makale da muwaddah yana romacing dinta da sunan sallama ,yaso kwarai su koma tare ,amman taki sai daya gama tsotse mata baki da laguda mata jiki zuwa kirjinta sannan ya barta ya d'auki hanyar birnin iko..

da daddare suna zaune su duka a parlour'n dady ban da faiza dake kwance a d'aki cikin bargo tana fama da zazzabin tafiyar M. A ,ana cikin hira ala'meen ya shigo gayar da dady Wanda kaida ne kullun daren duniya zai shigo gurin dady su gaisa kmr yadda yaga yaya akram nayi, ihsan tace" yaya ala'meen d'azu na hau samanka ban sameka ba ,nayi zaton ko zance ka tafi gurin latifa ya cilla mata muguwar harara "to idan can naje sai me kin ganki ko mumy ... ,wallahi da ba dan ke din mai sunan mahaifiya bace dana shuka miki rashin mutunci yau..
Suka kwashe da dariya "ai kuwa da munganku arana inji cewar eiman ...

ihsan tace "bama za'a ganmu arana ba ,daman sako zan bayar ka kai mata,"sai ki bari idan zani ,eiman tace yaya ni kuma ina son zuwa gurinta ta min lalle da kitso , ala'meen yace "Allah idan kuka dameni da zancen wata latifa zan mazgeku yanxu, kun ji min yara da tonon silili kowa sai yasan da wata latifa..

suka sake kwashewa da wata dariya har dady ,wanda cikin dariyar yace ",ku rabu dashi zan sa direba ya kaiku sai kuje har muwaddat itama ta gano gari ala'meen ya dubi inda take zaune tana waya ,magana take kasa kasa a waya Amman babu mai jin abinda take fad'i ,saboda a hankali take magana ya tsura mata idanunsa yana kallonta yana magana da kannenta, kallo daya tayi masa ta d'auke kanta tare da gaisheshi ",ina yini maimakon ya amsa gaisuwarta sai yace ya zaman bakunta ?"lfy tace akaitace bai sake cewa komai ba ya samu guri ya zauna yacigaba da kallonta .

M. A datake waya dashi yace "Halan wannan tsohon mayen ne ?"nifa Allah zan masa rashin mutunci akanki dan me zai dinga shiga tsabgarki, kema har da wani gaishe shi ya k'arasa fad'ar mgnr yana Jan tsaki"cool dawn kanina babu komai fa atsakaninmu, ka cire zargi zuciyarka "karka manta shi da kai duk abu guda ne agurina kmr yadda zan mutuntaka haka yazama dole na mutuntashi sannan na girmama shi ...
"tsaki ya ja " ki shirya next week zanzo in tafi dake sannan ya kashe kiran ..
Tayi shiru ta d'ago idanunta ahankali suka had'a ido da ala'meen yayi sauri kawar da fuskarsa gefe yana cigaba da hirarsa "hanyar d'akin ta nufa kar dai zargin Auwal ya tabbata al'amen sonta yake ?

"kai impossible hakan ma bazai ta'ba yiwuwa ba ,shi da yake da matar da zai aura ..shi kuwa al'ameen binta yayi da wani shu'umin kallo zuciyarsa na sake bun kasa da soyayyarta da tayi masa kamun kazar kuka .

Washegari da safe bayan an gama kalaci duk yaran gidan suna parlour'n mumy ,dady ya shigo gabad'aya yaran suka kaceme da hayaniya, kowa da abinda yake fad'i muwaddat ce kawai tayi shiru ta kama kanta saboda tun jiya da M. A yayi fushi daita akan yaya ala'meen ta rasa samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya dady ya dubeta yace "muwaddat ki shirya direba ya kaiki yawo ki d'an ga gari eiman tayi saurin cewa "Amman dady har damu ko? Dady yace da dai kun bari an kaita ita kad'ai idan kuka fita tare zaku dameta da hayaniya" kai dady yau fa week ce babu makarata kabarmu mu fita tare itama zatafi jin dadi ko aunty ?
Kafin muwaddat ta bata amsa dady yace "ko babu makaranta malamin lesson dinku zaizo an jima ..

Ana cikin haka sai ga ala'meen yashigo a shirye cikin shirin fita ,t shirt ce ajikinsa da bakin wando jeans, dady yace" yauwa tunda yayanku yau yana gida bama sai na had'a muwaddat da direba ba ,ala'meen ga kanwarka nan ka d'an fita daita taga gari, Dan tun zuwanta ba inda taje .

Ala'meen yayi shiru yana kallonta soyayarta na sake huda zuciyarsa, yana da inda zashi Amman hakan bazai hanashi bawa wannan fitar mahimmanci ba ,
Cikin rawar jiki yace ,"to dady ta shirya mana ai sai mu fita ya kalli eiman " fushin me kike yi ?

ihsan tace "wai Dan dady yace ba damu za'a je ba saboda lesson din zaa yi mana , alameen ya harari eiman "ai ko babu lesson bazaki shigar min mota ba sai dai ku fita direba ..

Dady yayi murmushi" wai me ke had'aka da eiman ne sam kafi biyewa faiza da ihsan akanta?
"dady yarinyar ce bata da kunya "eiman tayi saurin cewa "wai dady Dan akan aunty Ltifa tayi min waya ta tambayeni yana gida shikenan tun lokacin ya tsaneni ,dady yace to kai meye abun jin haushi ba kai da kanka ka nuna kana sonta ba nima fa na lura a yan kwanakin baka zuwa gurinta kmr da ala'meen ya shafa sumar kansa yana murmushi "babu komai dady kawai ina hutawa zata janyo azo a dameni bayan nayi mata gargadi ko abokaina suka zo nemana karta kuskura tace ina gida sai dai idan ta tambayeni amman dayake mara jin magana ce da an xo nemana sai tace ina gida dady yace "ke eiman kinji abinda kikayi daga yanzu in ana nemansa kice yayi balaguro eiman tace "to dady ai shine yake cewa idan mutane sunzo nemansa su tambayeni kuma haka kawai sai na dinga yi karya,byn karya babu kyau ala'meen cikin wasa yace"zaki rufewa mutane baki ko sai na bubbugeki ,tayi shiru tana gunguni ya d'an waiga bai ga muwaddat yace "wai ina wace zan fita daita ne ?

Faiza tace bari na dubota tana ciki tana shiryawa tana shiga d'akin ta iske muwaddat kwance a d'akinta mamaki yakamata tace ",kai aunty ke da ake jira za ki fita yawo tare da yaya ala'meen shine kawai zaki zo ki kwanta .

Muwaddat ta d'an yatsina fuska ",nifa wallahi banason fita haka kawai ,ni bancewa dady ina son ganin gari ba A6mman dan rigima wai wani sai an kaini yawo "ko dai da yaya ala'meen ne baki son fita ?
"amman ina laifin a fita dake kiga gari tunda har yanzu bakigama sanin garin ilori ba ..

"Ke nifa ban iya fita da wannan magananne mutumin wallahi sai yasa Kan mutu ya d8auki caji Sam Sam maganarsa bata da limit "ke ina ruwanki da maganarsa ,tunda ke ba mai magana bace bare kice maganarsa ta dameki?
"Kuma ba surutu garesa ba ,wallahi idan kikaji yadda a waje ake complain din rashin kula mutane da bai yi sai kinyi mamaki agida kam ya kan 'bata lokacinsa akanmu, kuma yanzu kinga fita nashi uzurin zai yi dady ya sashi"
"Kin fahimcesa ba daidai ba shiyasa naga kin sauya fuska lokacin da dady yace ya fita dake yawo ..

"Kinga faiza banson dogon turanci kema yanzu na kula zama dashi yasa kin dawo aku kuturu , abinda za'a yi yanzu kawai kije kice kaina ke ciwo shiyasa nashigo na kwanta .
Chapter 38 · 0% Book details