← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 99

Sashe 52

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

barin jiknsa tayi ta waigo inda motar ala'meen take sai dai babu shi babu alamarsa ajiyar zuciya ta sauke tana adduar Allah yasa bai ga sanda Auwal ya rungumeta ba ,juyo da fuskarta Auwal yayi suna fuskatar juna "shine kika shareni ko ?
Sai ki min laifi amman ki fini fushi ,dan Allah ki daina yin abinda zai dinga d'aga min hankali.

"ni me nayi ?

"A bar zance kawai ki shirya dake zan wuce gobe "ta juya tasoma tafiya "ka wuce kawai saboda ba tare mukazo ba, yasoma taku ahankali ya biyo bayanta yana cewa "Baki isa ba ,sai kin bini ,domin bazan zauna jiran gawar Shanu ba , ina can ina bacci ana nan ana min shari ba ,dolenki ki shirya mu koma inda muka fi wayo ,idan ba haka ba karfin soyayyata zata fallasa abinda ke tsakaninmu ,tana tafiya tace "ka dad'e baka bayyana ba ,binka ne dai bazan yi ba ,dan haka kana iya juyawa a yanzu ka koma inda ka fito. ....

Tana shiga cikin gidan kanneta dake tsaye jiran shigowarta suka Mike suka rungumeta, sauran kad'an su kaita kasa suna murnar dawowarta dan tun da ala'meen yashigo suka san sun dawo, sun dai dakata ne saboda sanin da sukayi yaya bunayya na harabar gidan ,shi kuma ba d'aukar nonsense yake ba .
parlour'n ya kaure da hayaniya amman suna ganin shigowar bunayya kowace tasamu natsuwa, ya dubi eiman dake rungume da muwaddat tamkar zata shige jikinta "ke ki barta haka mana ta huta kin wani rungumeta kina k'ok'arin kaita kasa ,ko zaki ballata ne?
"kai yaya bunayya yaushe zan iya balla big sister ai sai dai ta ballani, tsaki ya ja "kina hauka ne da ina magana kina maida min ?
" Ki shiga hankalinki, daman tun shekaranjiya nake tattare da haushinki dan Allah kiyi abinda zai tunzira zuciyata Kafin na bar garin kiga yadda zanyi dake .

Tsit gabadaya parlour'n yayi babu wace ta sake magana har sanda ya samu guri ya zauna yana duban muwaddat kasa kasa ..d'auke kanta tayi tamkar bata ga irin mayataccen kallon dayake binta dashi ba .

Faiza ce tayi karfin halin cewa "Sannu aunty muwaddat kun sha hanya yasu inna?
"duk suna lfy sunce agaisheku ,"muna amsawa ai naga yaya ala'meen ya shigo hujiga hujiga "muwaddat tace "dole hanyar ce sai a slow daga hk bata sake cewa komai ba illa runtse idanunta datayi alamun gajiya sannan taja kafafunta da kyar zata nufi hanyar d'akin mumy sai gata ta fito daga d'akinta tana murmushi "har kun karaso ?

"Eh momy mun dawo da Dan karan gajiya, bakiji jikina ba wallahi duk inda na motsa ciwo ta k'arasa maganar tana shagwa'be fuska kmr zatayi kuka "ai dole wannan hanyar tamu sai ahankali k'arasa kiyo wanka ki rage gajiyar ina ala'meen yake ?
"Ina tunanin yana d'akinsa dan tun dazu yashigo "to sannunku da hanya maza k'arasa ki watsawa jikinki ruwa kiji sanyi ......sannan ta kalli inda bunayya yake zaune ya hard'e kafafuwansa yana jijigawa "bunayya akawo abinci ne?
girgiza mata kai yayi kafin daga baya yace "sai dai zuwa anjima "okay idan ma akwai abinda kake son ka sanar min "okay mumy "
muwaddat ta nufi hanyar d'akinta yayinda mumy ta nufi d'akin dady domin sake gyara masa kafin ya dawo, su eiman kuwa tuni sun bar parlour'n zuwa lesson room.

parlour'n ya d'auki shiru na wani lokaci, kafin daga bisani faiza ta mike tsam daga mazaunita ,ta isa inda bunayya yake zaune a mazaunin mutun uku,yana jin ta zauna kusa dashi, yayi saurin matsawa saboda daf da junan da sukayi, dan sam bai lura zama zatayi a kusa dashi ba ,ya d'auka kitchen zata shiga.
naunayen ajiyar ta sauke tana dubansa sannan tace "har matsayina ya kai ka dinga guduna yaya bunayya?
yana jinta yayi mata banza tmkr ba dashi take mgn ba ,har sanda ta kiran sunansa a raunane "yaya bunayya i have to talk to you again akan soyayyata gareka coz i has to that ,bazan gaji ba, ba kuma zan hakura ba saboda ina son........a matukar tsawace yace "short up there with your rubbish before everything could mess up wit us , "kina sona ni bana sonki, ki tsaya matsayinki na sister dina, ni kuma zan cigaba da tsayawa a matsayin yayanki... ..period
"ni ..ni banason hk ,nafi son ka soni soyayya irinta aure da dukkanin zuciyarka da rayuwarka, i have to dash the love I have for you out ..."ka taimaki rayuwata yaya bunayya kasoni ta k'arasa mgnr muryarta na rawa ala'mun zatayi kuka.
sai lokacin ya fuskance sosai fuskarsa a had'e tmkr wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya kira sunanta a kausashe. "faiza you really have to carryover your tears , muwaddat is mine and me alone ...muwaddat ce a zuciyar muhammed auwal, ba kuma zan iya sonki ba, ruwanki ne ki taimaki rayuwarki ki cire soyayya, ruwanki ne ki cigaba da haukan da kike kwakwa da sunan soyyaya ,yana gama fad'ar hk ya mike yana jan tsaki "aikin bazan kawai yarinya k'arama dake sai shegen naci da kwakwar soyyayar tsiya, "yaushe ne ma aka haifeki i tough duka baki wuce 17 ba.. ya k'arasa fita ,yana maseefa a harabar gidan suka had'u da yaya akram wanda dawowarsa kenan daga office ,yana ganinsa ya fad'ad'a fuskar da murmushi, bunayya ya k'araso garesa ya mika masa shima yaya akram ya miko masa nashi hannun suka gaisa kana suka jera zuwa cikin part dinsa, yana tambayarsa dan ganin yadda ya bala'in had'e rai"ya na ganka hk bunayya
kmr kana cikin damuwa?
"damuwar ma akwai shi yaya.."to mu k'arasa daga ciki naji damuwar kanina..

*********
daddare da misalin karfe takwas ,gabadayansu suna zaune a main parlour'n din gidan ,bayan yaran gidan sun gama cin abinci muwaddat ta fito sanye da doguwar riga ja har kasa wacce samanta ke da igiya dake tsuke brest ,wanda hakan yasa manya boob's dinta suka cure guri daya, kasan riga kuma a bud'e take ,kanta sanye da hula shima batayi tunanin sanya hijab ba,dan tasan iya yaran gidan kawai zata iske a parlour'n, har zata zauna mumy tace "ga abinci can fa yana jiranki, tun dazu bunayya yake jiran ki fito ki zuba mishi.
ta d'an waiga inda mumy ta nuna mata yake zaune,ahankali idanunta suka sauka akansa yayi tagumi tare da tsura mata tsumammun idanunsa yana kallonta kmr karta k'arasa, in dayake, sai kuma taga rashin da cewar hkn, domin mumy zata fahimci akwai wani abun daya faru tunda ba haka ta saba ganin suna yi ba ,dan haka kawai ta ta k'arasa inda yake zaune, har ta k'araso dining area taja kujera ta zauna idanunsa na kanta ,ya kasa d'auke idanunsa akanta,ahankali ta bud'e kular abinci, sannan ta jera sarving plet guda biyu ,ta zuba abinci a natse tayi sarving dinsa ,shi kuwa har lokacin kallonta yake yi, ya kasa d'auke idanunsa akanta ,harara ta buga masa tana jan tsarki can kasa, yayi miskilanle murmushinsa sannan yasoma k'ok'arin zuba musu drinks a two cups .

Ta zauna a natse tare da kai spoon din abinci bakinta ,taji sautin muryarsa ahankali ta hanyar dakatar daita sannan ya amshi spoon din hannunta yana ture plet din gabansa "bari na taimaka miki ko "
a Sanyaye ta sakar masa tana d'auke idanunta akansa saboda Sam batason wani dogon magana yashiga tsakaninsu, ta rigada ta kudurcewa zuciyarta bazata sake sakar masa komai nata ba, yanzu tana biye masa ne saboda idanun mumy.

ahankali wajen ya d'auki shiru sakamakon barin parlour'n da eima da ihsan sukayi , daman faiza tana d'akin tun rana taki yarda ta sake fitowa , itama mumy ta tashi ta nufi bangarenta .

kasa jurar ya bata abinci abaki kmr yadda yayi niyya tayi, dan haka ta kai hannunta ta d'auki wani spoon yana kallonta ya shareta ya cigaba da cin abincinsa yana kallonta while yatsun kafarsa daya na yawo a tafin kafarta yana mata tafiyar tsutsa ,gabadaya ta kasa cin abincin tsagar jikinta suka shiga mikewa........
wani irin zirrrr.. take ji agabadaya sansar ajikinta ,ahankai tayi baya da kafafunta tana daidaita natsuwarta dan kar ya fahimci halin data tsinci kainta ,idan takai loma daya bakinta sai ta tsaya juya spoon kafin ta kai wani , shi kam babu wani alaman jin wani abu attare dashi ya cibaga da cin abincinsa normal, sai dai shima duk Loma daya sai ya tsaya ya kalleta most especial kirjinta dake fuskantarsa ,ya ajiye spoon din hannunsa tare da tsurawa kirjinta idanu sosai yana kallon saman brest dinta, da sukayi wani irin fresh sai sheki suke ,bawani abinci kirki taci ba, ta ture plet gefe zata ajiye spon yace ",cigaba da cin abinci mana, me kika ci anan dan Allah yayi magana muryarsa can kasa ?

Yatsina face dinta tayi alamun ba tason ya dameta ,sannan tace "na koshi ne, bai kulata ba ya sake tura plet din abinci gabanta yana tsareta da manya tsumammun idanunsa masu raunata mata jikinta a duk sanda ya d'aurasu akanta "ki tabbatar da kin ciye abincin nan, dan nasan wancan sakaran bai tsaya kin ci abinci ba, yana kaiwa nan yayi shiru ya d'auki cup din drinks ya kai bakinsa "wancan sakaran ta maimaita acikin ranta ,Sam ta rasa dalilin dayasa bunayya bashi da kunya, yaya ala'meen din zai kalla yacewa sakarai kamar shi da wani kaninsa ,ko sa'ansa, bashi ba koita data girmesa , bazata cewa yaya ala'meen sakarai ba ..

Shiru tayi kawai tana kallonsa a sanyaye batare data sake kai abincin bakinta ba, ya tashi rike da cup din drinks a hannunsa ya nufi kan kujerar kushin, ya d'auki remut ya canza cheenal.
Chapter 52 · 0% Book details