← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 99

Sashe 22

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

byn tafiyarsa ummi ta dubi muwaddat "bby bunayya ko ya karya?ta fad'i hk saboda ganin har lokacin abun Karinsa na ajiye akan k'aramar kujera .
Muryarta a sanyaye tace "Bai karya ba "what har wannan lokacin?
"Ga abincin nan yace bazai ce "
ummi tace akan wani dalili kenan da bazai ci ba ?ni fa banason zama da yunwa ya dawo kenan za'a yi ta fama dashi akan abinci ..

"Nima dai bansan dalili ba ya dai ce bai ci , ummi tayi shiru kawai Amman gabadaya hankalinta ya karkata garesa,ganin zaman bazai fisheta ba ta yunkura ta Mike tsaye "bari naje na dubo shi ...

Koda ummi ta isa bangarensa ta iske shi tare da abokinsa nabeel Suna hira ummi cikin fara'a tace "a'a nabeel yaushe kazo gidan ?

Nabeel ya sunkuyar da kai yana shafa keyarsa alamun jin kunya "wallahi banjima da zuwa ba mun sameku lafiya ?

"Lafiya lau yaya gurin mamanka da kanenka fatan duk suna lafiya ,nima InshaAllahu zanyi k'ok'arin nashigo unguwar taku mu sada zumunci tunda kai kaki kawosu "nabeel yayi murmushi " kiyi hakuri ummi InshaAllahu kafin ma kizo zan kawosu "shikenan Allah ya taimaka yayi albarka "ameen ummi "

"Bunayya ummi ta kirasa ya d'ago ahankali yana shagwa'be mata fuska "me za'a dafo maka naji ance ko breakfast bakayi ba ?

"Yatsina fuska yayi yana D'an tunani abinda zai ce kafin daga baya yace anything ..cowslow ummi "to shikenan Amman ka dinga cin abinci mai Dan nauyi ,ni sai naga kmr ma bakajin dadi ,ko wani guri na maka ciwo ne ?
"Fuskarsa ya shafa da hannuwansa duka kana ya bud'e baki da kyar yace "Gani nan dai ummi ni kaina na rasa abinda ke damuna ta k'araso har inda yake zaune ta kai hannunta ta ta'ba gefen wuyansa "jikinka yayi zafi bunayya bari zan bawa baby magani ta kawo maka yanzu "yauwa ummi kice mata tazo min da coffee , ta juyo ta koma bangarenta sai lokacin tasamu natsuwar zuciya ta bawa masu aikinta umarnin su shirya masa lafiyayen abinci da cow slow, sannan ta aika muwaddat da magani.

bakinta d'auke da sallama tashigo d'akin ta nufi Kan karamin table din dake gabansa ta'ajiye tiren hannunta dake d'auke da flask da cups guda biyu ko kallon inda suke batayi ba shi kuwa tunda tashigo d'akin ya kafeta da tsumammun idanunsa yana kallonta har ta bar d'akin sannan ya maida hankalinsa kan nabel .
Nabeel ya numfasa sannan yace "ina fatan dai zuwa yanzu kasamu narasar shawo hankalin yarinyarka tare da bayyana mata sirrin dake ranka ?
M.A ya girgiza kai al'amun a'a Dan bayason nabeel din ya gane bai samu kar'buwa agurin muwaddat ."kana nufin baka fad'a ba ?
Ya sake d'aga masa kai "kai ko dai kana jin tsoron tinkararta ne hade da jin tsoron karka tace bata sonka ?

Murmushin gefen baki M.A yayi irin nasu na wayyayu "haba nabeel yakamata zuwa yanzu kasan halina kasan who's Muhammed Auwal? "Ka ta'ba ganin na furtawa wata mace kalmar so balle har tace bata sona ?
Yadda ban ta'ba furta hkn ga kowace mace ba haka nasan bazan kasa yin nasara da zuciyar muwaddat ba,zuciyar da nasa tana cikin shaukin kaunata, kawai dai zan barta zuwa wani lokaci kafin mu koma ..

Nabeel yayi shiru yana kallonsa ,shi kuwa M.A banda shafa qirjinsa dake kwance da suman gashi babu abinda yake yana sakin murmushi saboda fuskar muwaddat dake yawo acikin kwayar idanunsa.

'"Dan Allah friend kayi k'ok'ari ka fahimtar daita yadda kake matsanancin sonta kafin mu koma dan gsky banason ganinka cikin tunanin ,"karka damu zan yi k'ok'arin yin haka ,wannan ba wata matsala bace ,daga nan suka zarce da hirar makaranta, nabeel shine babban aminin M.A ,a London suka had'u a Jimi'a,tare sukayi karatu dashi ,dalibi ne mai kwazo kamar yadda M.A yake da tarin ilimi , couse dinsu daya ,suna karanta orthopaedic sugyre shima nabeel asalin Dan Nigeria ne karatu ne ya kai shi kasar har suka had'u da M.A ,nabeel na d'aya daga cikin mutane da suke mugun shiri da M.A babu abinda nabeel bai sani ba a game da soyayyar M.A da muwaddat ...

********

Misalin karfe biyar na yammacin ranar yashigo parlour'n ummi da akwati daya , yayinda direban ummi ke rike da daya ,
akwati guda yayiwa ummi tsarabar , Wanda kusan duk dogoyen riguna ne da takalma , da turarruka designer masu kamshi gaske ,da mayuka masu kyau da tsada, dayar akwatin kuma na abi ne shake da kaya ..

Gabadaya ummi ta duba taga babu abinda ya danganci na muwaddat aciki har sun soma hira ta kasa hakuri tace "ni kuwa naga tsarabar kowa agidan nan banga na auntynka ba ?
Iska ya furza sannan yace" wace haka kuma ?
"Kaci gidanku da wace haka ,aunty muwaddat nake nufi ina nata tsarabar ?
"Kai ummi dan Allah ki daina min irin haka wallahi bakin san yadda nake ji ba idan kikace muwaddat aunty nace ..

"To sannu gyambo sarkin son girma ,ko ma mai zakaji sai dai kaji amman muwaddat na nan matsayin auntynka ,kuma kabani amsar tambayata ina tsabarta take Dan nasan da kabata Zata nuna min ?

Ya had'e rai sosai kmr Wanda aka aikowa da sakon mutuwa yace "yana part Dina ki gaya mata tazo ta d'auka idan tana bukata .

" wani irin magana ce hk kmr kai da sa'arka ,kasani fa ko awa daya baby ta baka a duniya ta girmeka balle shekara har hudu "
"Ta girmeni a shekaru ni kuma ai na girmeta aciki da jiki , dan idan ba'a an fad'a ba babu me cewa ta girmeni ,ni Dan Allah ummi ki daina cewa haka Dan allah ,idan kina fad'ar haka kina da kusar min da burina akanta ," wani buri ne shi wannan?

Ya. tsotsa bayan keyarsa tare dana waskewa "ki ce mata tazo ta d'auki akwatinta, ko kuma ni kike son na kawo mata tasamu damar raina ni?

"Duk ma yadda kagani ,tunda dai ma zaka bata ai shikenan Allah yayi maka albarka "ameen yaso kwarai yayi mata zancesa da muwaddat sai kuma ya share ya dan Jima zaune hira ko zai ga fitowar muwadda bai ganta ba Dan haka ..
Ya baron parlour'n yana fitowa daga cikin part din ummi sai ga me gadi da saurinsa "yana ganinsa ya ja ya tsaya yana gaida shi, shima ya gaisheshi cike da girmamawa saboda yana ganin girman mutumin sosai "mai gadi yace ranka ya dade wani ne ke sallama da muwaddat a waje...

"Wani ya furta a d'an razane Gabansa na dukan uku uku cikin rawar murya yace "waye shi ?"gsky nima bansani ba amman yau shine zuwansa na biyar baya samu ganinta..

Batare daya sake cewa komai ba kawai yasoma tafiya yana yiwa mai gadi al'amar ya koma bakin aikinsa, shi kuma ya fito harabar gidan inda ya iske wata lafiyayiyar Mota kiran TOYOTA COROLLA LE fara sol, ya isa har jikin mota hannuwansa duka zube cikin aljihun wandosa ,cike da jin kai ya ciro hannunsa daya ya kwankwasa glass din motar Wanda ke ciki motar yayi warning glass tunaninsa ko itace Amman sai yaga sabanin haka ..

Ai take Fara'ar fuskarsa ta d'auke ,ya tsurawa M.A ido kawai yana kallonsa saboda tsabar kama da sukayi da sahebar ransa ,cike da karfin hali M.A yace "malam lafiya tsayuwar me kake yi anan sannan wa kake nema ?

barrister Abdul yace" ammm uhmm muwaddat nake nema Dan Allah ko tana ciki ?
M.A ya sake had'e rai sosai kmr an aiko masa da sakon mutuwa yace "tana ciki me zata maka ?
"No daman bawani Abu bane kawai dai nazo ne dan ..."dan Allah malam dakata ya katse masa hanzari cikin zafin zuciya " daga yau karka sake zuwa kofar gidan nan da sunan kazo gurinta Dan muwaddat matar aure ce ..."

"matar aure fa barristers ya furta hankalinsa a matukar tashe ?
M.A yayi masa banza yana watsa masa wata uwar harara datasa hantar cikin barrister kad'awa cikin tsoro yace "dan girman Allah kuyi hakuri wallahi ban sani ba, watakilla shiyasa taki saurarata tun farko, cikin rawa jiki yasoma k'ok'arin tada motarsa .

shi dai M.A bai sake cewa komai ba ,ya juya ya koma ciki gidan yana bawa mai gadin umarni kar ya sake zuwa kiranta ,a duk sanda Wani yazo nemanta yace matar aure ce ..
mai gadi yace "babu ma mai zuwa gurinta ,ai hajiya akwai kamun kai ," kai dai kawai kabi abinda nace maka "to angama.

M.A ya nufi part dinsa ya bar mai gadi da mamaki wannan al'amari ,ya dad'e yana tunanin wannan matakin da M.A ya d'auka, Amman dayake yasan hatta ita kanta hjyr gidan batason ana zuwa gurin muwaddat din ,yasa ya amshi dokar da mahimmanci.

Anwar na shiga part dinsa yashiga sintiri gabadaya ya rasa wa zai tunkara da matsalarsa kusan minti goma yana zariya sannan yasamu guri ya kwanta akan gadonsa ya janyo wayarsa yashiga what's app aiko yaci sa'ar tana on line bai tsaya wata wata ba ya hau tura mata sakon kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭..

Cikin minti daya kacal ta turo masa da martani sakonsa, har biyu ,Amman ta goge
" me yasa kika goge abinda kika turo? Ya sake turo mata had'e da kuka.

"Nothing ta turo masa ."

Ya sake turo mata uhmmmmm wallahi mun 'bata dake ..🙅🏼‍♂

Ita kuma ta turo masa alamar dariya 😅😅daga k'arshe ta rubuta masa "kace mun 'bata ko ,to ai kayiwa kanka wallahi ?

Jikinsa na rawa ya rubuto mata "yi hakuri mun shirya ai bamu fad'a da juna .."

"No bana son shiri da kai yanzu , sai na tsula maka tsiya.

",uhmmm plz kiyi hakuri kinji tawan bazan iya dogon fushi dake ba.

"tawan ta turo masa da alamar 🤔🤔mamaki ..

Shima ya turo mata "to ta waye idan ba tawa ba?
" ke din tawace muddin rai babu Wanda ya isa ya rabamu..
Ta turo masa alamar 🤺🤺🤺🤺zata zanesa sannan ta sauka .shi kuwa yana ganin ta sauka yaja tsaki ya kwanta ,bai farka ba sai can yamma yana tashi ya tashi da zazzabi sosai sai dayayi kansa allura ya janyo wayarsa yashiga what's app yashiga turawa muwaddat sako .
Chapter 22 · 0% Book details