Sashe 89
Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye inda aka faka motar data dawo dasu daga hospital d'azu suka nufa daita , direba na hangosu ,ya zabura ya mike ya nufo inda suke cikin sauri ,dan ko ba'a fad'a masa ba ,yasan babu lafiya ,domin fuskokinsu da gangar jikinsu kad'ai ya nuna masa haka ,cikin sauri ya bud'e musu gidan baya , bunayya yayi saurin shiga yana rungumo ummi jikinsa ,abi yasanya gangar Jikinta cikin motar ya rufe,kana ya nufi gidan gaba , gabad'aya jikinsa a sanyaye yake ,cike yake da fargaba da tashin hankali ,ya sani ya rasa mukaramarsa har abada , ya kasa kamanta halin dayake ciki , duk yadda ake jin mutuwa Yana jinta fiyye da haka a gangar jikinsa ,zai kaita hospital ne domin bunayya ya tabbatar da bata raye ko ta fawwalawa Allah komai ........
Shi kuwa bunayya jikinsa Banda rawa babu abinda yake ,ya sake birkicewa ,sai faman zuba sambatu yake rike da hannu ummi ,yana jin babu wata bakar rana arayuwarsa kmr wannan ranar ,tun da yake arayuwarsa bai ta'ba jin makamancin bugun zuciya da tashin hankali irin wannan ba ..
ya d'auka tashin hakalin rabuwa da muwaddat wani bangare ne na rayuwarshi ,a she rabuwa da umminsa yafi komai tashin hankali da ciwo ...
" hakika bai san yadda rayuwarsa zata kasance nan gaba ,"shin me yasa mutuwa zatayi masa haka ?
"Karya ne wallahi umminah bazata mutu ba ya fad'a da karfi Wanda yasa direba taka motar da karfi ,shi Kuma abi yashiga goge hawaye yana sake maimaita "Inna lillahi wa Ina ilaihi raji'un.....
Cike da tashin hankali Abi yaciro wanshi yasoma neman layin d'aya daga cikin likitocin asibitin Ummi ,yana shaida musu halin da Ummi ke ciki, ikon Allah ne kawai yakai su asibitin, domin wani irin shararan gudu da driver yake tsulawa akan titi.
wani irin mahaukacin burki me k'ara direba ya taka dai dai lokacin daya shigo haraban asibiti ,da isowarsu asibiti,sun iske bakin k'ofan emergency cike da manyan likitoci, take likitocin suka soma k'ok'arin k'arasawa inda motar take , yayinda wasu daga cikinsu ke turo gadon d'aukar mara lafiya ,cikin gaggawa gaba d'aya likitocin hankalinsu a tashe yake sanadiyar ganin Ummi cikin mawuyacin hali.
cike da tashin hankali aka ciccibi Ummi aka dorata akan gadon asibiti aka fara turata Bunayya yafito a guje , kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin matukar tashin hankali, hannu Ummi ya rike cikin nasa yana binsu gudu gudu sauri sauri ,yana gunjin kuka yana Kiran "Ummi nah karki min haka.....
" Ummi na na tuba bazan k'arawa ba.."
" Ummi nah ki tashi karki tafi kibarni please Ummi, yayinda ruwan hawayensa ke d'iga a saman fatar hannun ummi , kai tsaye d'akin likita akayi da ita, nan take likitoci suka rufa a kanta ,suna bata taimakon gaggawa..
Likitocin sunyi iya kokarinsu amman abun tafi karfinsu ,shi kansa bunayya ya kasa aiwatar da komai, dan kuwa kusan shi yafi su rud'ewa ,nadama dana sani babu wanda bai yi ba ,jikin likitocin yayi sanyi, suka shiga kallon juna , gabad'aya an rasa wanda zai iya fahimtar da wad'an bayin Allah rasuwar ummi, saboda ganin halin tashin hankali da suke ciki, ba d'an ba,ba uban ba ,kowanensu ka kalli fuskarsa kasan yana cikin tsananin tashin hankali ...
Da kyar Dr najib ya juyo Yana dubansu cike da tausayawa "alhj sai dai muyi hakuri ,dan zuciyar madam ta daina bugawa , ta rigamu gidan gas.......
maganarsa ce ta tsaya cak sakamakon wata uwar cakuma da bunayya yayi masa, yana sakin wata irin k'ara kana jikinsa na rawa yace "you are very stupid Dr najib........
" ummin tawa kake cewa haka?
"idan ka sake furta wannan kalmar ga umminah sai na kasheka da hannuna ...
" mamarka ce zata mutu amma ba umminah ba, ya k'arasa fad'ar haka yana matse wuyansa da rigar jikinsa da , likitocin sukayi caaaaa akasu suna k'ok'arin kwatar wuyar Dr najib a hannu bunayya ..
Da kyar abi yasa ya sakar masa wuyar riga ta hanyar buga masa tsawa,"kana hauka ne bunayya ?
"hawaye na bin kuncisa yace "abi bakaji abinda yake cewa akan umminah ba?
" wai ummina ce ta rigamu gidan gasky ,ummi nah fa .....
Mamana.... mahaifiyata ce fa....... ..
ya juyo cikin rawar jiki ya kalli likitocin dake tsaye akanta, yace "dukkaninku baku San aikin da kuke yi ba kawai dai kuna nan ne just for nothing ,ku bar min d'akin ni zan duba mahaifiyata amman sam ummina bata mutu ba .....
Abi ya rigada yasan d'ansa baya cikin natsuwarsa da hankalinsa, mutuwar uwarsa tazo masa a bazata da kuma shekarunsa na kuruciya .
Jiki a sanyaye ya kamo hannunsa "muje waje bunayya "
"a'a abi babu inda zani sai nasan halin da ummina take ciki , akwai jijiya d'aya dake jikin kowani d'an adam ,abarni abani damar na dubata da kaina matukar na dubata zan......zan.........
Sai Kuma kuka yaci karfinsa ya kasa k'arasa maganarsa ya durkushe gaban abin "shikenan nayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyata da kaina ? Abi ya kamo shi shima kukan yake son yi
"Kayi hakuri bunayya haka Allah yaso muje dai waje likitoci su samu suyi aikinsu,"abi ummina ce fa kwamce bata motsi ?
"Ka furta kalmar Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un da kyar dai abi ya janyo shi sukayo waje sam idan kaga bunayya bazakace shine mai shegen girman kan nan da dagawa ba abi ya rungumeta shi ajikinsa yana furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un ,wanda sai lokacin Allah ya raimakeshi ya rika yayita yi yana zubar da hawaye ...
Awa uku cur likitoci suka sake d'auka akan Ummi ,cikin hukuncin Allah sai gashi ta farfad'o tare da sauke naunayen ajiyar zuciya ,godiya suka shiga yiwa Allah , suna murna, sun yi farincikinki sosai domin ummi mutun ce ,akwai kirki da sanin yakamata, uwa uba sanin darajar dan adam , sam ita bata da wulakacin ,da talaka da mai kudi duk matsayi guda garesu a wajenta , rasa irinsu ba karamin hasara bane, amman idan Kiran babban sarki ne babu yadda za'a yi dole ta amsa Kira Kuma dole zuciya tayi hakuri .. . ...
Farkawa kawai ummi tayi ta ganta akan gadon asibiti, ta fahimci hkn ne sakamakon ganin mutun biyar daga cikin likitocin dake aiki akarkashinta ne tsaye bisa kanta suna Kara Mata ruwa tayi hanzarin mikewa zaune tana raba idanu tare da tuna abinda ya haddasa Mata zuwa asibitin ,Dr saratu dake bayanta ta k'araso jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya Tayi mata abinda ya faru yashiga dawowa cikin 'kwalwaluwarta idanunta kamar gauta alamar tana cikin tashin hankali Kuma har lokacin idanunta Basu daina zubar hawaye ba, ta fasa ta razananniyar k'ara tare da fizge hannuta daga rikon da Dr Salim yayi Mata ta kamkame saratu ajikinta tana kuka magana take son yi amman ganin likitocin yasa ta kasa furta komai sai kuka " to me ma zata ce ?
"Duk abinda zata fad'a a yanzu tamkar ta tonawa kanta asiri ne, dan hk ta cigaba da kukanta Dr saratu na shafa bayanta , Dr saratu ta kamkameta tana rarrashinta alamar tayi shiru ..
.
" ki kwantar da hankalinki mukarama inshallahu komai zai daidaita ganin kamar akwai wani sirri na musamman dake bakin ummi yasa likitocin suka fice daya bayan d'aya suka bar d'akin Dr saratu ta kwantar daita "ki kwantar da hankali koma meye ki damunki ki fallawa Allah .....
Ki yawaita furta Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un ,zuciyarki na matukar bukata hutu a halin yanzu ummi ta runtse idanunta gam ..
Likitoci na k'ok'arin fitowa abi ya fad'a d'akin shi kuwa bunayya da sauri ya bi bayan d'aya daga cikin likitocin yana tambayarsa ,yanayin jikin umminsa ,suna tafiya doctor na yi Masa bayani ,har suka shiga cikin office dinsa, ya dan juyo yana dafa kafadar bunayya "ka kwantar da hankalinka inshallahu zata samu sauki, ka dinga had'awa da addua zamuyi mata allurar yanzu dan ta samu relief, bunayya yayi jugun hawaye na kwarara akan kuncinsa , da kyar yayi karfin halin juyawa batare da ya cewa likitan komai ba, ya bar office din kai tsaye d'akin d'a'a kwantar da ummi ya nufa ,yana shiga ta bud'e idanunta tana ganin shine, ta d'auke kanta zuwa wani bangare tare da cewa "kace masa kar ya k'araso gareni banason ganinsa ,ya bar d'akin nan bana son ganina acikin idanuna , karaf maganarta ta shiga cikin kunnuwanshi .
tun kafin Wanda aka bawa sakon ya fad'a masa , ya tsaya daga inda yake yana duban ummi da har lokacin kuka take ..
"Ummi ....
Ba..bana son jin komai daga bakinka ta k'arasa maganar tana sauke numfashi da kyar "
Hannu abi ya d'aga masa al'amun ya tafi kawa ..
Ahankali ya juya jikinsa a matukar sanyaye ya fice ya nufi harabar hospital din yana jin wani irin kuna acikin zuciyarsa , kai tsaye bayan mota ya bud'e ya shiga ya zauna yana jin wani irin bakinciki ,batare da bata lokacin ba direba ya yiwa motar key ,suka bar hospital, zaune kawai yake a bayan motar amman shi kad'ai yasan abinda yake ji ,shi kad'ai zai iya misalta halin tashin hankali da yake ciki.
da fari baiyi tunani zai damu a dalilin cikin jikin muwaddat ba domin ganinsa haka shine sakamakon masu hali irin na iyayensa ,sai yanzu ya fahimci abun ba haka bane, suna shigowa gidan ,ya nufi part din umm domin ganin halin da muwaddah take ciki ,can karshen gadon ummi ya iske kwance tana jujjuya Kai had'e da rike kasan mararta ,ya k'arasa gareta da sauri yana k'ok'arin kamota jikinsa ta goce "karka ta 'bani ... kana ta yunkura ta mike tsaye ta soma tafiya.