← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 99

Sashe 41

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Al'ameen na jin tautaunawar da samarin keyi akan muwaddat kawai ya tsinci kansa da jin matsanancin kishi akan magana ,cikin hanzari ya matsa gaba kusa daita yace "am har yanzu baki ga abinda kike so ba ne?

"Uhmm ina dai dubawa yace "Jimana ta d'ago da sauri ta dubeshi "idan bazaki damu ba ki koma cikin Mota ki zauna zan zabar miki duk abinda kike so ..

Mamaki ya kama muwaddat domin ita bataga dalilin da zai ce ta koma mota ta zauna ba ,kamar ta tambayeshi sai kuma tayi shiru har ta juya zata tafi sai taji yace kmr dame dame kike so?
Batare data juyo ba tace chocolate kawai nake bukata "da kuma me "shikenan nan suna maganar ne ahankali yadda duk munafurcin mutun bai isa yace yaji abinda suke cewa ba ,musamman yadda al'ameen ya lura da hankalin mutane wurin yana kanta ,duk sanda ya d'ago idanunsa sai yaga maza da suke ciki ita suke kallo hkn ya sake k'ara masa kishi a zuciyarsa ,tana fita daga ciki yaji ya D'an samu natsuwar zuciya .

Ahankali take taka kasa kamar batason takawa Yayinda duk wani matashin dake tsaye agurin hankalinsa da natsuwarsa ke kanta, wasu suyi magana azahirance ,wasu kuma acikin zuciyoyinsu a irin wannan lokacin da tasan da tare take da Auwal da yanzu sunyi fad'a yafi sau babu adadi domin cewa zai yi ita ke kiransu da jikinta ta hanyar rausaya wacce ita Sam batasan tana yi ba ,haka ta taso ta samu kanta da tafiya a natse kamar bata son yi , shi yasa duk lokacin da fita takamasu tare baya yarda ya barta ta fito ,sai dai tajirasa a mota shi yaje ya dawo idan kuwa tayi masa magana sai yace"bazai iya kasada da rayuwarsa ba ,sannan bazai jurar wasu kwaratan banza na kallar masa mata ba ,tana isa harabar gurin wayarta tashiga k'ara ,a natse tasoma k'ok'arin bud'e Jakarta batare da ta kai dubata ba ta ciro wayar tana d'aura idanunta akan screen din wayar ganin sunan dake yawo ajikin screen din wayar ne yasa take gabanta ya fad'i ,gefe daya na cikin zuciyarta sanyi taji acikin ranta jikinta har rawa yake lokacin data d'auki kiran ta manna wayar a kunnenta "hello Auwal dina "babu wani Auwal dinki ,tun jiya rabon muyi magana dake ko araye nake ko mace baki da matsala kawai kin tattara kin shareni kina harkokin gabanki ko"?
Yadda yayi maganar cikin shagwa'ba da tsigar isa yasata ta murmusa "kai my auwa ka fiye rigima , mai ma akayi daka d'auki zafi dayawa ?
"Tun jiya nake tura maka sako babu respond sai yanzu dakayi ra'ayi kirana ..

"Ai bazaki sani ba sai ki min laifi amman idan na nuna fushina ki fini fushi tun daren jiya rabon da muyi waya ban kiraki ba why not ke ki kirani ?
"To kayi hakuri, kadan bani minti goma zan shiga wanka ne idan na fito zan kiraka ta fad'i haka tana istigifarin karyar datayi domin idan ta bari yasan bata gida kuma tana tare da al'ameen mai rabata dashi sai Allah "ban yarda ba, adaidai wannan lokacin nasan abinda kikeyi ba wanka ba ,idan kuma wanka ne ki turo min nonona nagansu nayi kewarsu .....
ya k'arasa fad'ar haka yana buso mata iskar bakinsa ta cikin wayar,take numfashi nta ,ya ne mi d'aukewa ta dafe saitin zuciyarta "Auwal zaka kasheni fa "idan na kasheki nayi rayuwa dawa ?
"Ga matan nan dayawa a duniya sai ka zaba ka durje.

"no no Sam bazasu min ba ,karki manta inda nayi karatu cikin kyawawan matan turawa Wanda yawo tsirara agurinsu bawani Abu bane duk banji daya daga cikinsu Sumin da zan iya rayuwata dasu ba ,ni kece macen Da zuciyata ta yarda ta amincewa rayuwa daita .
Ta k'arasa jikin mota taja ta tsaya tana cigaba da sauraransa gabadaya ta manta da inda take saboda yadda maganarsa ke shiga cikin jikinta da zuciyarta .

Al'ameen kuwa tafiyarta ya bashi damar yi mata tsiyaya sosai sannan ya fito ya sameta jikin motar tana waya ,bai ji komai ba aransa saboda tunaninsa ita da iyayen goyonta ne ,batare da yayi magana ba ya bud'e mato yashiga ya zauna itama ta bud'e ahankali tashiga ta zauna tana jin zai tayar da motar tayi saurin katse kiran gabadaya ,koda ta gama katse wayar batayi magana ba suka wuce .

M.A kuwa yayita k wayar taki d'auka akalla sai da yayi mata missed call biyar bata d'aga ba, sai zuciyarta dake dokawa saboda fargaba tasan tana d'auka wayarsa ta saka kanta cikin matsala,Dan zai fahimci inda take , daidai sun kai wani traffic al'ameen yace "ki d'auka mana ko kiran bashi da mahimmanci ne ?

"Sannan ma waye mai kiran ?
Yayi mata tambayar batare daya juyo ba yana taka motar saboda danja ta tsaya Kan layinsu tace "karka damu da kowaye kacigaba da tukinka kawai "
Bai ji dadin abinda tayi masa ba, dan hk ya sake wani magana ba ya maida hankalinsa kan tukin dayake ita kuma tana kallon gefen titi shi kam jifa jifa ya kan juyo ya kalleta, yanayin yadda take yin magana yana bashi sha'awa ,ta d'an juyo ahankali ta kalleshi suka had'a yayi saurin kawar da idanunsa tamkar ba ita yake kallo ba ,tacigaba da kallonsa yanayin yadda yake tukinsa taji ya burgeta saboda wannan karon Jan motar yake sannu ahankali cikin natsuwa da kwarewa da nuna ganintar tuki kowa yaga yadda yake sarrafa sitiryarin yasan ya kware da tuki ,agaskiya tukin nasa ya burgeta tunda har taji tana sha'awar itama taja mota da kanta dan dai abi ne bayason can al'amen kamar yasan abinda yake zuciyarta ai ya d'an waigo ya dubeta "kin iya mota kuwa?

Ta d'an kada kai "eh to Auwal ya fara koya min amman har yanzu hannuna bai fad'a ba "ya had'e rai dosai jin ta ambaci sunan Auwal ya cigaba "ai ina jin ko kin koyi tuki ina ganin dady'nki bazai barki kija mota ba da kanki ba, "nima ina tunanin haka shiyasa ban maida hankali wajen koyo ba .

"Amman yana da kyau ki iya koda bazaki dinga ja ba, cikin murmushi tace " zan yi kokari naga hannuna ya fad'a suka dan yi shiru ,sai dai muwaddat ta damu da yadda ya takura mata da kallo can ya sake takalota da magana "Amman tunda zaki dade agarin nan me zai hana ki dinga yawan kaiwa minal ziyara kmr yadda ta bukata?
"ba damuwa duk sanda na sami lokaci zan rinka zuwa "idan kin samu lokaci ko idan mai kaiki yasamu lokaci?
Jin ya jefa mata tambaya sai tace "daga ni har mai kai ni din ."amman ai ke kina da lokaci tunda ba karatu kikeyi ba kina cikin Hutu ba kuma aiki kike zuwa ba ..

"Haka ne amman ina karatu saboda wannan zango gabadaya zan rubuta jarabata ta karshe ta bashi amsar tana had'e fuska saboda ta lura hira yake son suyi ,ita kuma bata fiyye son hira dashi ba ,haka suka cigaba da tafiya yana janta da magana tana d'an sharesa har suka iso gidan tana shirin fita daga motar yace "am...aysha.

Ta waigo da sauri "kin mata kayanki ta kai ganinta ga kayan manya ledoji ne guda biyu shake da kayan ciye ciye ta d'an yi murmushi "nagode sosai amman chocolate kawai zan d'auka aciki daman kuma ita nace ina so ..

Yace "shikenan naji amman ki d'aure ki shiga dasu ko su eiman da mamana suna so ,ta d'an yatsina fuska saboda bata son kinkimar kaya tace "bari idan nashiga sai na turo su d'auka ,ta fita ta fara tafiya zata shiga cikin gidan yana zaune a motar har tashige gidan ba abinda yake banda kallon tafiyarta taku take cikin natsuwa irin na matan da suka amsa sunansu mata ,shi kansa yasan tana da mugu kyau kmr yadda mutane suke fad'a kuma ya yarda da had'uwarta da ajinta ,yasan bazata ta'ba d'aukar kayan tashiga dashi ba ,da haka da kansa ya kinkimi kayan ya bita dashi cikin gidan ya tadda kannenta zagaye daita kowa na tambayarta guraren daya kaita ,ita kuma tana cewa su bari sai ta huta ..

Al'ameen nashigowa parlour'n ya ajiye mata kayan gefenta ya tafi abunsa ta bi bayansa da kallo Wanda batasan dalilin hakan ba ,Allah sarki ta furta cikin zuciyarta tana jin rashin dadin abinda tayi masa ,tasan da Auwal ne sai dai abar kayan ,amman ko sama da kasa zasu had'e bazai d'auko mata ba ,ta ina ma girman kai da miskilancinsa zai sa ya biyota dashi "my Muhammed Auwal kenan yaro da izzan , shi Sam baya d'aukar raini ga kowa ga tsabar miskilanci Wanda yake daya daga cikin abinda yasa take naci akan kaunarsa .

Tana son Auwal tamkar yadda take son rayuwarta ,tana son shi tana son su rayyu tare muddin rai Auwal daban yake acikin maza bazata gaji da furta hakan ba....
Tunda take kallon maza bata taba ganin mai irin yanayinsa ba komai yafisu ,ba dan tana son shi ba ,sai dai tasan ummi bazata bari aurensa ba saboda kaninta ne ...
Tasan dakace auwal yayanta ne ,tasan sai inda karfin ummi ya kare amman sai ta mallakamusu juna

Mummy ta fito daga d'akinta tana fara'a "aa yan yawo kun dawo ?
Muwaddat tayi murmushin tace "Eh momy mun dawo "kece yau wata yarinya tasha yawo har ina da ina kukaje?

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!!

don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

page 18

....muwaddat tayi shiru tare da tsurawa kannenta fararen idanunta tana tunanin abinda zata fad'a musu har momy ta fice daga parlour'n ,aiko faiza da eiman suka dameta da tambaya,gashi ita guraren data sani kad'an ne acikin garin ilori , tana gudun kada su kureta,lumshe fararen idanunta tayi ahankali saboda tuno wasu daga cikin sunaye gurare siyaya data sani , dan haka atsanake tashiga lisafowa .
Chapter 41 · 0% Book details