← Book details Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 99

Sashe 47

Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke sannan ta koma ta zauna tana dubanta had'e da nazarinta "har ga Allah ta yarda da maganar diyarta, saboda tasan yadda shakuwar dake tsakaninsu da uwarta tafi karfin haka ,domin kuwa daya baya iya d'aukan dogon lokaci batare daya ba ,yanzu haka kullun garin Allah ya waye akalla basuyi waya ba sai sun yi sau Goma hatta bacci suke tashinta wani lokacin ko abinci zata ci sai takirata tana cin suna waya haka zalika abi ,Yayinda komai akayi ta bangaren kowanensu ,yanxu ne zasu bugawa juna suna cike da tsantsar farinciki suna labartawa juna "
Ahankali mumy ta bud'e bakinta "to kuma shine zaki zauna kina kuka?
" idan kin gaji da zama damu kamata yayi kiyiwa umminki magana tasa azo a tafi dake .. .. ba wai ki zauna a d'aki kina kuka irin hk ba "
Amman yanzu ki bari zuwa wani sati sai ki koma, saboda ina son kije kalgo ki ga inna kafin ki koma, ki d'an yi kwana biyu agurinta ,dan koda yaushe idan munje sai tayi maganarki ,Dan haka zan saka ala'meen ya kaici gobe tunda weekend ce sai kiyi musu kwana biyu "zuwa lahadi ko manday sai ku dawo, ki soma shiri komawa
Muryarta a matukar raunane tace "to mumy "

Mumy tace "Muje ki ci abinci Sam baki son cin abinci muwaddat, shiyasa gashi nan kullun jikin naki babu laka bare kuzari ,muwaddat ta Mike tsaye jikinta a matukar sanyaye tayi gaba tasoma tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki , mumy ta bi d'akin da kallo sannan ta kai hannunta Kan wayarta dake yashe Akan gadon ta d'auka tana duddubawa, babu abinda ta gani duk number's din yan gidansu ne Dana kawayenta , sai number guda daya data ga an rubuta (man ) muwaddat...mumy ta kira sunanta. ...
ta D'an tsaya tare da juyowa ta tsaya tana duban mumy "waye kuma man ?
"Tayi shiru can tace " d'an makarantarmu ne "meye tsakaninki dashi ?
"Babu komai momy "to ki goge lambarsa bana bukatar ganinta cikin wayarki ,sannan ki dinga kiyayewa ,Allah kuma ya kiyaye mana ku a duk inda zaku sanya kafafunku .

Muryarta ahankali tace ameen ta amshi wayar ta goge number man har ma data Auwal gabad'aya sannan ta sake juyawa ta cigaba da tafiya mumy ta biyo bayanta ,
Mumy na fita ta kira ala'meen a waya ta sheida masa abinda take so ayi a gobe idan Allah yasa suna raye ta kirasa Dan ya kwana da shirinsa ,yace mata "babu damuwa Allah ya kaimu.
Tun daren al'ameen ya shirya kayansa set biyu kacal ya d'auka sai kayan Pajams dinsa haka ma muwaddat mumy ce ta shirya mata kayanta cikin yar k'aramar akwati ..

Washegari tunda sanyi safiya suka d'auki hanya zuwa kalgo, gudu kawai al'ameen yake sharara akan titi batare daya juyo ya kalli inda muwaddat take ba ,haka zalika itama bata kalli inda yake ba idanunta naga kallon titi ne, domin haushinsa take ji acikin zuciyarta, ganinta duk shine silar damuwarta silar da yasa ran bunayya ya 'baci har suka samu sa'bani dashi , Dan da kace bai aiko kiranta ba alokacin da duk hakan bata kasance ba ..
Tun yana dauriya har dai yasoma janta da hira tana amsa masa tana yatsina fuska amman ya dakewa zuciyarsa ya cigaba da janta Dan dai ta saki ranta sannan yana bukatar tafiyar tayi masa dadi gashi ga rabin rayuwarsa ,tafiya ce mai nisa tsakanin ilorin da kalgo sannan suka iso ..
suna shigowa kauye ya rage gudu
Adaidai wani madaidaicin gida yayi parking din motarsa ya fito yana Mika had'e da salati ,kusan minti goma ta fito tana kallon yanayin garin ,yana nan dai tamkar yadda ta sani acan baya sai 'yan canje canje kad'an da taga garin ya samu na cigaba ,ciki kuwa har da gidan kakarta ,Kafin kace me tuni kofar gidan sun cika da kananun yaran unguwar da almajirai suna kallonsu had'e da zagaye motar .

Daya daga cikin yaran ya k'araso gurin ala'meen yana washe baki "yaya ala'meen sannu da zuwa "yauwa musa sannu ya kake ya gida ?
ala'meen ya fad'i hk yana zagayo ya bud'e boot ya d'auki akwatin kayanta,musa yayi sauri ya amsa had'e da shiga cikin gidan inna .
Ya waigo ya dubeta tana kallon yaran dake zagaye suna wasa da tsalle tsalle "Muje ko ,nasan kin gaji dayawa "ba tace masa komai ba ta nufi hanyar cikin gidan tun
daga farkon shigowarta gidan tasan ba iyayenta kad'ai rayuwa ta sauyawa ba har da kakarta , koina tsaf tsaf sannan a tsaftace malale da tayis har cikin tsakar gidan bakinta d'auke da sallama tasanyo kanta ta k'arasa shigowa, inna dake tsaye jiran shigowarta tun shigowar Musa ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tana murnar ganin jikarta, "marhabun lale da mutanen iko da ilorin "muwaddat ta saki murmushi me tattare da gajiya sannan ta k'arasa ta rungume inna ajikinta "inna mun sameku lafiya ?
"Lafiya kalau ya hanya ?
Bata amsa ba ta saki inna tana dubanta "mu shiga daga ciki sannu kun kwaso gajiya "babban ango maraba sannu ,kun sha hanya "sai yanzu kika ganni tun dazu nake ta faman bud'e makoshi ina rattafa sallama amman kikayi min banza "yi hakuri mai gidan asaliyyan, ni na isa in shareka ai ko zan yi shariya sai dai in share wancan mai wuyan kamar lagwani , amman ba kai ba ,suka saka dariya ita dai muwaddat tayi gaba tashiga d'akin da inna ta nuna mata .

Tana shiga ta zauna gefen gado tana tunanin abinda zata fara yi sallah ko wanka cikin haka inna tashigo d'akin tana sake yi mata sannu ,muwaddat ta yatsina fuska "Sannu me kuma zaki min ni da ke wuya kamar lagwani ?
Inna tasa dariya jaira haushi kikaji kenan ?

"Dadi abun yayi min shiyasa "ke jaira banciki da bakin ranki ,yanzu dai dame zaki fara wanka ko sallah ko abinci ?
"Ina bayi tukunna dan gaskiya wanka zan fara ,
Inna ta nuna mata bayi sannan ta sake yin waje .
Muwaddat ta Mike tsaye ta bud'e akwatin kayanta ta ciro white towel ta d'auki makilin da brush ta nufi bayi wanka tayi ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga sannan tashiga Jero sallolin dake kanta ..
Bayan ta idar ta kai idanunta Kan hadadden kafet din dake gabanta kwanunka abinci ne sama da Goma ajiye ta d'ago tana duban inna tamkar zatayi kuka "wadan nan abincin fa inna?
",duk ke akawowa ki bubbude kiga Wanda yayi miki ,kai ta girgiza sannan tace "wane kika dafa aciki ?
inna Ta janyo wata kula blue ta bud'e "ga Wanda na dafa miki "to shi kawai ma ya isa shima din kad'an zanci .

Inna ta Mike zata fita amman jin abinda ta fad'a yasa ta d'an tsaya "ki dibi abinci kici sosai sannan ta sanya kai ta fita muwaddat ta d'auki plet ta dibi abinci kad'an tasoma tsakura bayan tagama ta nemi guri ta kwanta akan gadon inna ta ciro wayarta ta kunna takira mumy ta sheida mata sun iso ,sannan takira iyayen goyonta, suka hira har sanda ala'meen yashigo wayar take ,Dan haka bai ce mata komai ba ya koma gurin inna .

**********
Alameen Suna zaune tare da Inna suna Hira, cikin hirar ne take Masa zance aure" ala'meen yakamata zuwa yanzu ace ka'ajije iyali ga sa'anin haihuwarka Nan daga masu mata biyu sai uku sannan kowane da ya'yansa abun sha'awa, Mai zai Hana kai ma kasamu sukuni ka samu ka duba yarinyar data dace ko anan cikin dangi ne ka zaba ..?

Ala'meen Yayi murmushi kawai Yana duban Inna har sanda ta numfasa sannan yace "maganarki gaskiya ne Inna yakamata, sai dai har yanzu ina kan dubawa dai, inshallah Nan ba da dadewa ba zan kawo Miki kyakkwar kishiya wacce tafiki kyau da komai ..

Koma wace balarabiya ce fatana ka kawo ta gari yar gidan mutunci , ni kuwa sai naji ina maka sha'awar auren ayshatu ,wallahi baka ga yadda kuka dace da juna ba ,da zaka yarda da shawarata sai ka nemeta nasan babu abinda zai Hana ubanta yaki baka ,Kuma Nima zanyi farinciki sosai, Kai kowa ma zai ji Dadi hakan ta fad'a Tana duban ala'meen,ta ga yadda zai d'auki maganar .

yadda take dubansa din yasa kirjinsa bugawa saboda maganar ta bugesa Sosai ,jin yayi shiru tace banji kace komai ba .?

"To me kike son nace Inna ?ni kaina abinda ke cikin Raina kenan ,amman gabadaya yarinyar taki bani damar fahimtar daita, zan dai Bata lokaci Nan da kafin ta koma zanyi kokarin sanar mata," to ka hanzarta Dan dai saboda Allah zuwa yanzu yadace ace ka'ajiye iyali ,idan Kuma kafinson na mutu Banga aurenka ba to shikena..
ya kamo hannuwanta duka cikin nasa Yana Bata fuska "Kai Inna karki fad'i haka ,da yarda Allah bama aurena ba hatta ya'yanmu nida akram sai kin gansu,
"kai rabani da zance wancan ja'irin tsohon tuzurun, koda yaushe shima hk nake fama dashi akan batun aure, har ma gara kai yanzu tunda nasan inda ka dosa, shi fa ko mgnr auren ma baya kauna yanzu, byn shekaru baya da kansa ya kawo min karar iyayensa akan yana son aure amman yanzu na rasa dalili , wasu abubuwa ma nagani nayi kmr wanda aljanna ta aura ..
"duk yarinyar da aka nuna masa sai yace batayi masa ba.
ala'meen ya numfasa kana yace "ni kaina abubuwan akram na damuna da ta'ba min zuciya, gabad'aya tun dawowarsa daga canada na rasa gane kansa da gindinsa , gashi yau ciwo gobe lafiya, kwanaki dana yi masa rakiya ganin likita ,karkiji irin fad'an da likitoci sukayi masa akan wasa da rayuwarsa da yake ,wai zuciyarsa na daf da bugawa, tambayar duniya nayi masa amman amsa daya akram yake bani babu komai ,shi baya tunanin komai alhalin ni nasan akwai abinda ke damunsa boyewa kawai yake , dan wallahi inna kwana akram yake yana kuka da buge buge a d'aki shine ma dalilin dayasa na bar masa d'akin na koma sama.
Chapter 47 · 0% Book details