Sashe 48
Muwaddat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"subuhanallah shikenan zargina ya tabbata, aljanna ce wallahi ta auresa, to ka sheidawa iyayensa ko ,dan asan matakin d'auka?
"a'a inna ni dai nakan yi masa addua alokacin muna tare ,aiko bamuga ta zama dole a nemo masa taimako..
Hira sukayi sosai har sai daya ga ala'mun inna ta fara jin bacci sannan ya bar gidan Yana mata sallama .
**********
duk inda yakamata ala'meen ya Kai muwaddat ta sada zumuci ya kaita sai yan tsirarrun gidajen 'yan'uwa da gidan innarsa ne Bai Kai ba, suka barshi sai zuwa gobe lahadi Wanda daga Nan zasu wuce . .
Tun da safe ya kaita gidan munira ta amshe su cike da fara'a tare da nuna mata gurin zama da murnata da komai ta karbeta hannu biyu biyu duk da basu wani san juna ba sosai saboda tun Tana yarinya rabonsu da juna ,muwaddat taji Dadi sosai saboda ita dai mutun ce Mai son a nuna ana sonta ,Kuma adamu daita tare da rawar jiki akan lamarinta, suka gaisa a mutunce cikin haka Mai gidanta ya fito ,yana ganin ala'meen yace "babban Yaya kun iso lafiya tun jiya nasamu labarin zuwanku ya mutane can ?ya Mika Masa hannu suka gaisa ala'meen yace "kowa lafiya duk sunce agaisheku ..
cikin farar mijin munira yace "bakuwa sannu da zuwa ya hanya ?
Muwaddat ma tayi Dan yi murmushi kad'an Tana gaidashi ,munira kuwa sai rawar jiki take Tana Nan Nan da muwaddat kafin kace me ta cika mata gabanta da abinci ...
Muwaddat Bata wani ci abinci kirki ba har gara ma lemu ta kan Dan tsiyaya Ta sha .
Bayan awa daya ala'meen yace wa mijin munera "Dan Allah Bala idan bazaka damu ba ina son munira ta raka yarinyar nan gurin sauran dangi akwai inda bazan iya Kai ta ba ,gashi goggo tace" akaita Koina acikin dagin ta sada zumuci Bala yace" shikenan babu damuwa sai ta kaita ai "Yana gama fad'ar haka yayi gaba, shima ala'meen yace Bari ya Dan shiga gari kafin su dawo har ya Kai bakin kofa ya juyo Yana dubanta karki damu munira zata Kai ki duk inda yadace .
Gyada Masa Kai kawai tayi batare datayi Masa magana ba, munira tace Bari na shiga na shirya nazo mu fita ga mamakin munira sai ji tayi tace" kariki damu kanki ki Bari kawai ba sai munje koina ba ,Nan ma kawai ya Isa wallahi garin akwai Rana sosai" keda da aka kawoki a cikin mota koina ac "
Muwaddat tayi murmushi "bana son fita ne wallahi mu zauna muyi hirarmu har zuwa sanda zai dawo , munira tayi sororo Tana kallonta sannan tace "Anya ayi haka bayan kinji abinda goggo tace .?
"Mubari kawai ai muje gurare dayawa jiya tashiga fad'a mata inda sukaje jiya dan haka muyi zamanmu muyi Hira ... ana suka wuni zir suna Hira sai wuraren la'asar ala'meen ya dawo munira tayi Masa sannu da zuwa tare da tashi ta kawo Masa ruwa Mai sanyi ,ya amsa ya Sha idanunsa na kan muwaddat ,ala'meen ne ya fara magana "yau dai kun Sha yawo .
Muwaddat tayi shiru domin ba tasan me zatace ba, sai munira ce tace "ai bamuje koina ba domin dai tace bazata iya bin Rana ba.
ala'meen ya tsira mata ido yana kallonta batare daya ce komai ba ,anan ya fahimci momy ce kawai ta damu datazo gurun danginta amman ita Sam Bata wani damu ba .
Tun shigowarsa muwaddat ta kasa sakewa bata wani Sanya baki cikin hirarsu ba saboda ala'meen dake binta da mayatacen kallo ,duk inda ta motsa idanunsa na kanta wanna dalilin yasa ta kasa sakin jikinta ..
Can bayan kmr minti goma ya dubeta "tashi muje ko Kar muyi later saboda Ina son na bita ta gidan hajiya batayi magana ba ta Mike ta d'auki Jakarta ta rataya tayi gaba .
munira ta mike tayi musu rakiya har harabar gidan inda ala'meen yayi parking din motarsa .
Ala'meen yashiga mazaunin direba itama tashiga ya tayar suka tafi har suka shiga wata unguwa, taga yayi parking din motarsa a wani kofar gida ya d'an dubeta Dan Allah kiyi hakuri zamu shiga wurin hajiya mu gaisa .
Batare data juyo ba tace "shiga ka fito ina jiranka ,bai ji dadin yadda tayi Masa ba, koda yake me yiwuwa dan batasan wace hajiyar yake nufi ba ,amman ko batasani ba sai ta tambayeshi ,shi Kuma sai ya fad'a mata gidan hajiyarsa yake nufi yasa Kai ya fita Tana kallonsa ..
har zai shiga gidan sai Kuma ya dawo ya tsaya ta bangaren da take '"ki fito mu shiga Dan Allah gidan yayan mumy ne fa da suke ciki daya, wato mahaifina kinsa mumy bazata ji Dadi kixo garin nan har ki tafi baki zo kun gaisa ba ,jin haka yasa ta fito Tana yatsina fuska tamkar wace taga Kashi .
Tasoma tafiya ahankali har suka shiga cikin gidan .
Jin kad'an ta fito ta shiga motar tayi zamanta .. Koda ya fito yasameta cikin motar Tana waya bai yi mata magana ba ya bud'e motar yashiga ya tayar .
Yana sauketa agidan inna ya k'ara gaba ,domin ya tsani yadda take yi Masa ,a yadda ya lura shi kawai takewa wannann miskilacin amman ai Yana ganin yadda takewa mutane ko d'azu daya koma gidan munira d'aukota Hira ya iskesu suna yi har da dariyata amman Tana ganinsa tayi shiru Bata sake cewa komai ba .
Da sallama tashigo gidan Tana yatsina fuska Inna ta dubeta Tana yi mata sannu "kin gaji ko Daman ziyara haka yake dole ki gaji baki saba ba "wallahi Inna duk na gaji garin nan naku akwai Rana "Inna tayi murmushi in go nan tayi mata dakuwa ,"Allah yasa dai kema garin naku ne Kuma inshallau acikin garin Zaki karasa rayuwarki "Kai Inna ina zan iya rayuwa anan ,ku dai daya zamemu ku dole kuyita fama, mu ma dinga zuwan muku ziyara ta k'arasa maganar Tana shigewa d'aki dayake Bata fahimci inda zance Inna ya nufa ba ....
Daddare ala'meen yashigo gidan yasa mu Inna Tana zaune akan tabarma yayinda muwaddat ke kwance akan gadon Tana rike da waya da dukkanin alamun chatting take, bayan sun gaisa da Inna ya waigo inda take kwance ya Kira sunanta..muwaddat
Ta yatsina fuska sannan tace na'am '"ki shirya gobe da wuri saboda fitar asuba zamuyi "to kawai tace Masa atakaice Tana juya Masa baya ..
Inna tayi kasa da muryarta can ta yadda muwaddat bazata jiyota ba "wai yana ga Kamar kana jin tsoron yarinyar, ka fad'a mata abinda ke ranka mana Kar fa wani yayi maka shigar sauri, duk da dai tunda tazo Banga Wanda ya kirata ba, ko ita takira ba ,bayan iyayenta "girgiza Kai yayi "ba yanzu ba tukunan Inna "
"ya dai tabbata dai tsoron nata kake ji?
"to kusan haka ne Inna duk lokacin Dana yunkuro zan fad'a mata sai fargaba ta hanani .."ina ganinka jarumi a she kaima lusarina ne bansani ba.... "yanzu meye abun fargaba da jin rsoro anan?
" to Bari ni na sanar da iyayen nata "a'a Inna karki yi sauri yanke hukunci haka ,kinsa fa gaugawa daga sheidan ne, ki Bari mubi komai ahankali ke dai kiyi min addua kawai "to shikenan Allah yasa rabonka ce ,yace "ammen suka shiga wata hira har sanda goma ta buga yayi mata sallama da zai wuce ya k'arasa inda take kwance idanunta a lumshe suke ala'mun tayi bacci ya Dade tsaye akanta Yana dubanta Yana jin sanyi aransa sannan daga baya yasa Kai ya fice ....
*********
Washegari tun safe suka d'auki hanyar komawa ilori d'auke da tsaraba kauye iri iri danginsu daddawa kuka da gasashen kifi sai Kuma dankalin hausa Wanda yazamoto abinda aka fi nomawa kenan agarin kalgo ....
Agajiye suka k'araso ilori saboda mugun gudun dayayi akan titi ....
Suna shigowa harabar gidan idanunta ya sauka akan muhammed auwal zaune akan motarsa Yana fuskantar kofar tafkeken get din gidan yana ganinsu tare cikin motar yayi wata irin zabura ya duro ya tsaya yana kallon motar zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu.
Ta tsura masa ido har sanda ya tsaya jikin motarsa ya harde hannayensa duka a saman kirjinsa tamkar wani babban mutun ,ahankali ta cigaba kallonsa kirjinta na wani irin mahaukacin bugu lokaci daya hankalinta yayi mugu mugun tashi ,kallo daya zaka mata kasan cewar ba cikin natsuwarta take ba ,tana cikin zallar tsoro da abinda idanunta suka ci karo dashi ne, sam batayi tunanin ganinsa a daidai wannan lokacin ba, ba ita ba hatta ala'meen ya d'an samu buguwar zuciya da irin kallon kaskanci dayake aiko musu dashi .
Gaban bunayya ya dinga faduwa ya kura mata tsumammun idanunsa yana kallonta sam ya kasa d'auke idanunsa akanta yana duban abun tamkar a mafarki ,yayi bala'in mamakin ganinta tare da ala'meen, ya fara taku ahankali zai zo gurinta sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi akan gara dai ya cigaba da tsayuwarsa a inda yake zai fi masa alkhairi ,idan ma ya k'arasa inda yake yace mata me ?
Dan haka ya koma da baya ya jingina bayansa da jikin motarsa ya cigaba da kallonta ,Kallonsa take yi itama cike da matsanancin tsoro sannan a matukar kidime tun daga kasa har sama kirjinta na bugawa, zuciyarta kuwa kamar zata fito daga cikin kirjinta .
Gabadaya halitar jikinta babu inda bai amsa ba .
Da kyar tasamu ta yunkura ta zata fito daga cikin motar dan tuni ala'meen yayi parking taji sautin muryarsa a kasalance "koma ki zauna tukunna......
Mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_
~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~
warning!!!
don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk .....
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
page 20
....Tun bayan fitar bunayya daga d'akin abi,abi ya kasa samun natsuwar zuciya a game da al'amarin tillon d'ansa,
" a zahirin gaskiya yana jin tamkar ya biye masa ne, yayi masa abinda ya bukata, amman lokacin daya tuna shekarunsa a duniya a halin yanzu sai yaga gabadaya lamarinsa na tattare da kuruciya da sharrin soyayyar farko ne , Wanda mafi akasari akan samun haka acikin wannan duniya .