Sashe 9
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
*KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 4-5*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ciikin ƙufula ta ce, "ke dalla ja'ira ki karɓi wayar nan kira mini ɗan banzan yaron nan ya siyo mini madarar shanu, yau ba ni da wanda zan sha fura, kuma Faɗuma bata kawo mini ba."
"Ni dai Hajiya Baaba in dai ba za ki iya kiran sunana daidai ba, ki faɗi ainihin sunana, haka kawai ki rinƙa ɓata mini suna." Bata amsa tare da juyowa da sauri, sakamakon da har ta saka ƙafarta a waje.
"Ungo nan! na ce ungo nan, mutuniyar banza kawai." Ta ja numfashi tare da gyara zaninta sannan ta ci gaba da cewa, "zagi na kike mara mutunci! Ni za ki yi wa rashin mutunci kan na zagi wannan uwar taki mai baÆ™in hali.â€
Nahlin ta karɓi wayar cikin ƙunƙunai jin abin da tace. "Daɗin abin Ammy ba liability ba ce tana da abin yi, don haka rashin ƙibarta ba zai saka ya zama aibu ba, kin san ko babu Aby zata iya ɗaukar hidimar gidan nan har da ɗawainiyarki." Ta ce tare da ci gaba da ƙunƙunƙunanta.
"Barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe. Ai dama hali gado ne, amma ba ki gado ɗana ba, Allah dai ya raba mu da gadon baƙin hali. Ki gaya mini magana son ranki mahaifinki zai dawo." Shiru ta yi ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta miƙa mata wayar.
"Ƙin miƙa mini waya ba ki ce komai ba za ki fice ga jarababba ta fara ko? To maza dawo ki zauna yau sai mahaifinki ya dawo sai na ga in shi ya ɗaure miki gindi."
"Wayarsa a kashe yake."
Tsaki ta yi tare da galla mata harara da fici-ficin idanunta da suke cike da rigimar tsufa. "Babu komai tun da ba za ki yi mini ba, bari na kira uwarki daÉ—in abin uwarki ta yi karatun boko kin ga ba za ki yi mini rashin mutunci ba, don ban yi boko ba sai na sanya ita ko mai aiki ta yi mini kiranta ta kira mini mahaifinku."
Da sauri ta miƙe jin motar yaran gidan sun dawo daga islamiya ko banza ta huta da rigimarta na ɗan lokaci. Ta ƙarashe ficewa daidai lokacin da take faɗin, "Tunda ba za ki kira mini shi ba, ga su andal take ko dal ya kira mini shi."
Ba ta san lokacin da ta bushe da dariya ba tana faɗin, "Kya ji da shi fitininanniyar tsohuwa kawai. Ba ki iya faɗin suna ba, ki yi ta ɓata ma mutane suna kamar ance dole, ke dole sai kin shiga zamani."
Hajiya Baaba ta ja tsuka cikin ƙubula ta fara ƙoƙarin miƙewa tana salati, sai wani juyi take tamkar wacce zata yi wani aiki. Kusan minti uku tana ƙoƙarin miƙewa saboda ƙiba da ya yi mata yawa, wanda kullum Abby yake mata magana, akan ta rage cin kayan da zai saka ta ƙiba sakamakon ciwon jiki da take fama da shi, amma ta yi kunnen uwar shegu da shi. Sam bata da wani abinci sai waɗanda zasu sanya ta ƙiba da maiƙo. Tun yana mata faɗa har ya gaji ya ƙyale ta.
Gyara ɗaurin zaninta sannan ta shige ƙurya ɗakinta tana faɗin"Bari na kira Musa mai-gadi ya siyo mini da alama Faɗuma jikinta ya tsananta."