← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 79

Sashe 48

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To tsaya kiji da kunnin basira auren ku babu fashi sai dai ina mutu."

"Abu mai sauki saina saka miki gubar matuƙar kika ce za ki aura mini shi."

"Wayyo na shiga uku na mutu ba zan ƙara zama dake ba, kuma dole Halimatuu ta dawo cikin satinnan, ta ɗauke masifa da bala'in da ta kawo mini, don na tabbata za ki iya kashe ni saboda ba imani kike da shi, wanda baya sallah sai ya ga dama ina imani a ransa. Daga can a tattaraki akai ki gidansa kin ga sai ku kashe kanku in kun so." Bilhaƙƙi take kukan tana kallon mutanen ɗaki.

"Ai kuka yanzu kika fara matuƙar ba ki janye ƙudurinki ba, kuma ko baki faɗa ba dole na koma gurin iyayena."

"Ba ki da wannan hujjar na tursasa ni na aure ki don ba ki da iko da mu." Cewar Ajmal yana mata mugun kallo.

"Amma na isa da iyayenku, da suka haife ku ? Ni da ku mu zuba shege ka fasa."

Har ya buÉ—e baki zai yi magana Aby ya daka masa tsawa.

"Abin kunyar da za ku yi mana kenan? Kamar ƙananan yara haba Hajiya bai kamata ki biye musu ba saboda yara ne su."

"Allah Sarki! Da ma laifina za ka gani, tun da ni ba ni da iyayen da za su kare ni duk sun mutu." Sai kuma ta ƙara saka kuka." Allah ya jikan ku iyayena na san da kuna raye da kun kare ni. Allah ya jiƙan ku da rahma domin yau ga ranarku."

"Don Allah mu bar maganar nan mu tafi gida zai fi a sasanta kammu a can."

"Sasancin kenan ayi auren tun da na faÉ—a kai ma ka san babu uban da ya isa ya hana sai dai in Allah bai kaddara ba."

Lamarinta sai ya ƙara bawa kowa mammaki. Ammy ta ka sa cewa komai sai jinjina lamarin take yi domin ta san tun da ta furta sai wani ikon Allah, kuma in har ta sanya aka yi auren ba ta yi ma su duka ukun adalci ba. Da wani idon za ta kalli iyayen Mushiirat akan ɗan su zai yi wa 'yarsu kishiya auren da ko shekara ba a rufa ba. Sannan ita kanta Jannah ba da take karatu bai kamata ayi mata aure da wuri ba, uwa uba da ba ta da ra'ayin auren miji irin sa. Ga Amal da ya tsane ta da halayenta sannan ta ya ya zai fuskanci matarsa da maganar.

"Kai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba!" Ta furta cikin tashin hankali tana girgiza kanta.

"To amma wa zai hana?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ruÉ—ani wanda in dai babu lallain akwai sauran rina a kaba.

Hajiya Baaba ta miƙe ta bangaje Ammy dake tsaye a gefenta wanda ya sa ta yi saurin matsawa domin ta yi hakanne don ta tofa albarkacin bakinta ta ƙara baƙin jini a gurin ta. A ranta ta yi alƙawarin ko tari ba za ta yi ba in suna maganar, ita dai na ta kallo da fatan alkhairi. Da sauri ta matsa gefen tana kallonta.

Tun da Abby ya tsawatar babu wanda ya ƙara ko tari har suka shiga mota, sai dai Hajiya Baaba da take dafe bandejin da aka lulluɓe mata ciwon da shi, tana musu Allah ya isa don rabonta da ta ji ciwo har ta manta.

Ko da suka isa gida Aby ya hana kowa tafiya aka zauna a falon Hajiya Baaba don yin taron gaggawa.

Tsaki ta yi ta zauna tana faÉ—in,"Ko me za ka faÉ—a a taron oho, bayan na riga na yanke magana kuma babu fashi."

Ajmal ya ɗago idanunsa yana kallonta ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ma ya huta, domin da ya san in ya dawo abin da zai faru kenan, da ya tabbata acan har duniya ta naɗe in ya so matarsa ta bi shi can. Tun yana yaro take shigar masa hanci da ƙudundune ga shi ba ta sake zani ba, rana tsaka tana ƙoƙarin shigo masa da wata aba can, wanda ko a tarihin mafarkinsa bai taɓa tunanin rayuwa da ita ba, ballantana a zahirce, don haka a ransa ya sanya ayi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma, ai maganarta ba ta Allah ba ce.

"Kai ina ba za ta taɓa yiwu ba bindiga a ruwa. Da wane ido zan kalli abokanaina da mutane na nuna ta amatsayin matata ina matsayin malami, sai ta nemi aura mini 'yar tasha. Yariyar da ko Kur'ani ba ta sauke ba ballantana aje maganar hadda da manyan littafai." Ya furta a cikin ransa zuciyarsa a dagule.

Ummu ta É—ago tana kallon Jannah da ba ta wani damu ba, domin ta É—auki maganar kamar wasa gani take ba ta da right É—in da za ta yi mata auren dole.

Tausayinta da na Huzaifah suka sanya hawaye taruwa a gefen idanunta, musamman Huzaifah da ya mutu akan sonta, ba shi da buri sai dai maganar aurensu.

Kallon tausayi ta ƙara mata lokacin da ta ga sai danna wayarta take ba tare da damuwa ko da yake za ta iya mata uzuri don ba ta san wace ce Hajiya Baaba ba, don in har ba'ayi auren ba za ta iya iƙirarin tsinewa iyayensu wanda ba za su so hakan ba. Ba tare da ta sani ba hawaye suka fara shatata a fuskarta.

"Kai this is absolutely impossible! Auren nan ba zai taɓa yiwu ba. Huzaifah shi ya dace da ita kuma yana matuƙar ƙaunarta, don Allah Hajiya Baaba ki tausaya rayuwarsu."

Cikin zafin nama ta yi kanta za ta zabga mata mari. "To don uwarki sai ki hana in kin isa ba wai ki tsaya kina zagina da turanci ba don kin ga ban yi boko ba. Akan me gida bai ƙoshi ba za a bawa dawa."

Da sauri ta matsa bayan Ajmal ta ɓoye domin ita ba ta san maganar zuci ta fito fili ba.

Miƙewa ta yi tana gyara zaninta."Wallahi kun ji na rantse in har ni na haifi Muhammadu sai an yi aure nan, don haka ban ga amfanin taron nan ba, in dai ba so ake na sanya fitinar dole a ɗaura a yau ba."

Ta ja numfashi tana girgiza tare da balla ma Jannah harara da ta É—ago ido tana kallonta tana dariya domin har yanzu ba ta É—auka da gaske take yi ba. Ba tare da ta kula da bidiyon da take mata ba ta ci gaba da cewa,

"Idan Jannah ba ta da hali da tarbiya ni ina sonta a haka, kuma in bai rufa mata asiri ya aureta ba wa zai aure ta. Kai Muhammadu a gabana kake nuna ba ka son haɗa zuriya da 'yar ƙanwarka wanda kuka rage mini ku biyu tal a duniya, sai na ce sam ba ka yi wa Halimatuu adalci ba. Ka ƙi aminta da auren 'yarta ɗaya tal aduniya."

"Haba hajiya na gaya miki ki daina ce mini bani da tarbiya. Sai wani maganar aure aure kike yi, kin san babu yadda za a yi ni kamata ace wai zan auri ustazu kuma mara wayewa. Wallahi ko driver ba zan iya ɗaukarsa ba domin tuƙi zai rinƙa na rashin wayewa. Abin kunya ne na gaya wa frinds ɗina wai zan yi aure da mijin da zan aura. Wato irin rayuwar gidadancin da matarsa take yi kullum cikin ƙumbiya-ƙumbiya da hijabi da safa da niƙabi kike son na je na yi? I know values, noms, and dignity.."

"Rufe mini ba ki banza kawai! Kunyar gareki? Kamar kin ci ƙwadun ɗan akuya haka kike. Ga yi nan tun ba a je ko ina ba kin fara girban abin da kika shuka domin kan idonki ake nuna ba a son rayuwa dake, ko shi Huzaifah da kike cewa yana sonki, ba za ku daɗe ba zai wartakoki ki zama ƙaramar bazawara saboda rashin kunya da mugun hali irin na ki."

"Ai gara na yi rayuwar zawarci da rayuwa da wanda kike son haÉ—a ni da shi, ballantana na san Huzaifah yana mugun sona ba zai yi mini haka ba. Kune dai kuka É—auki mace baiwa kuna ganin in har ba ta iya girki da kula da miji ba ba za ta iya zaman aure ba, amma shi kansa a waye yake ya san 'yanci da hutu." Ta ce ba tare da shakku ko kunyar wani daga cikinsu ba.

"Tsakanina dake fa duka kawai ya rage amma kin daÉ—e da zageni tatas, domin duk wanda ya ke mayar maka da wannan maganar watarana duka zai kai maka. Ai ni dai wallahi Halimatuu ta haifar mini jaraba."

Banza ta yi da ita ba ta ce komai ba sai kaɗa ƙafa take yi cikin tsantsar rashin kunya da fitsara.

Ajmal ya yi shiru ya ma ratsa mai zai ce domin rashin kunyar da take yi ji yake kamar ya maƙure ta. Allah ya gani shi mutum ne mai tsananin son girma da kamun kai sam baya ƙaunar rashin kunya. Ko Mushiirat da take matarsa akwai lokacin da baya sakin mata fuska, ballantana ita da Hajiya ke son jawo masa raini ta haɗa su aure. Ai da ya yi rayuwar aure da ita ya gwammace ya mutu ba tare da aure ba. Duk rashin kunyar da take zuba wa sai ya zuba mata idanu kawai, burinsa ta fahimci wacce take son haɗa rayuwarsa da ita. In kuma ta yi gigin haka watarana sai dai a kawo musu gawarta domin bugu ɗaya zai aika ta lahira.

Miƙewa ya yi zai fice sai ya tsaya gab da ita ya fara da cewa,"A haka kike faɗin na auri 'yar da ba ta ganin ki da gashi? A haka kike son na kwashe ta na kai gidana Hajiya Baaba? In har kika yi mini haka sam ba ki yi mini adalciba ni da matana da muke zaman lafiya. Ina roƙonki tun wuri ki janye maganar auren nan kafin na canza mafa kammanni na yi wa wanda za ta aura asara don ni ko da gida da mota ba zan karɓa ba, saboda na tsane ta bana son ta ko mai kalarta ba na son gani."
Chapter 48 · 0% Book details