Sashe 49
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aikin banza na san dai mugun halinta ka tsana amma ba Jannah da take son kowa ƙin wanda ya rasa ba, don ta fi matarka mai kama da doya. In dai don halinta ne ai hannunka ba ga ruɓewa ka yanke ka yar."
Ya buÉ—e baki zai yi magana sai ya kasa ya girgiza kansa idanunsa suka kawo ruwa ya fice daga cikin gidan.
"Na riga na gama magana kowa ya fice mini daga ɗaki kuka yi mini tsuru-tsuru kamar wacce ta yi ƙarya ko sata, in kuma sata na yi sai a gaya mini abin da na sata na biya." Ta daka musu tsawa tana faɗin hakan daidai lokacin da Aby ya miƙe ya bi bayansa amma ina har ya tada motar ya figeta cikin tsananin fushi.
Sum-sum suka miƙe suka fice ban Jannah da ta dawo gabanta ta tsaya bayan ta ije wayarta akan kujera.
Kallon uku saura kwata ta yi mata tare da miƙe wa.
"Bari na je na yi sallah don na ga kamar rigima kike ji ko da yake sallar ba ta dame ki ba sai kin ga dama."
"Idan bana yi ma ba damuwarki ba ce Hajiya Baaba, tun da na ga ba tare za a rufe mu ba." Ta bata amsa tana girgiza ƙafa tare da ƙara shan gabanta bayan ta fara tafiya.
"Allah ya tsare ni da mutuwa a rufe mu tare, domin wallahi na san duka da suburbuÉ—a za ki sha a hannun walakiri, kin ga kuwa da a rufe mu ta shafe ni, gara a barwa tsutsotsi naman jikina suyi watanga da shi."
"Wannan kuma ke ya shafa ba ni ba ai, in kin so ki barwa Kuraye ko a kwalar rigata." Ta ce mata tana girgiza.
"Jannah ki fita idanuna domin kin san Allah in kika cika ni zan iya zane ki da carbin nan yanzu. Kin san ke kaɗai kike mini fitsara a gidan nan na shanye da wata ce da tuni na yi ƙulin kubura da ita, ke ɗin ma albarkacin uwarki kike ci duk da albasa ba ta yi halin ruwa ba."
"Ai wallahi fitsara yanzu na fara matuƙar kika ci gaba da haɗani da wancan bagidajen. Ina 'yar minister ki rinƙa haɗani da shi, ai ni sai dai na auri ɗan shugaban ƙasa ko gwamna."
"To shikenan, sai mu zuba ni da ake shege ka fasa. Ai da uba ake ado ba uwa ba, sai ki gaya mini me ubanki yake da shi? Shi kansa rakuɓewa ya yi jikin 'yata yana cin arziki, don haka baku da komai."
"Allah ya kyauta kuma ya fi ƙarfin ki kira shi makwaɗaicin tun da duk abin da yake samu a jikinta aiki yake mata da guminshi yake."
"Jannah ki matsa na yi sallah ga shi can an tada sallah kafin na fasa bakin rashin kunya."
Harara ta zabga mata jin me tace sai kuma ta ja gefe ta matsa tana huci.
"Ko da yake sam bai kamata na tada hankalina ba, domin dad shi yake da ikon aurar da ni, in kuma na ce bana so babu wanda ya isa ya yi mini dole, ko ita 'yar taki a ƙarƙashinsa take." Ta faɗa tana zauna wa a kan kujera.
"Au haka kika ce? To zan nuna miki wannan makwaɗaicin uban na ki ba shi da kataɓus 'yata ta mai da shi mijin-ta-ce ta shanye shi da kuɗinta.
"Dama tuntuni nake zargin da saka hannunki mom take yi wa dad wulaƙanci ga shi nan zargina ya tabbata."
"Ba dole ta yi mishi ba ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi a tashar wahala da ƙasƙanci zai sauka." Ta amshe maganar.
Haushin abin da ta faÉ—a ya sa ta saka kuka tare da É—aukar wayarta ta fice daga falon ta yi sashin su Ummu tana jan majina.
"Wawiya wacce ba ta san me yake mata ciwa ba, har wani ƙarfi uban na ki yake da shi da za ki alfahari da shi. Ma gani Allah ya kaimu su dawo sai ya haɗa auren in zai iya." Ta shige bayi tare da kunna famfo.
LONDON
"Kai ni fa wallahi kaina ya É—aure! Wai mai ke faruwa ne, mai ya sanya Hajiya Baaba za ta yanke wannan É—anyen hukuncin? Gabaki É—aya na shiga cikin ruÉ—ani!" Ta furta tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar ana buga mata guduma, domin ji take kamar ta rufe ido ta ganta a Nigeria.
"Rose, please give bottle of water and paracetamol." Ta ƙwalawa Rose kira tana faɗin haka tare da dafe kanta tana kallon dad da ya kasa cewa komai sai karanta wasiƙar jaki yake tun bayan da ta kira wayar.
Karɓar maganin ta yi ta ɓalla ta watsa a bakinta ta kora da ruwa tare da shanye ruwan kofin tas, sannan ta ƙara miƙa mata akan ta siyaya mata, wanda sai da ta shanye duka, domin ji take bakinta ya bushe babu ko ɗigon miyau.
"Shin wane irin lamari ne take shirin ginginmo mana gabagaÉ—i babu shawara? Wani abu ta yi mata, ko kamata ta yi tana harkar banza."
"Never! Karki ƙara danganta 'yata da wannan." Ta ji muryar dad ya daka mata tsawa yana faɗin hakan.
Kallon shi ta yi ba ta ce komai ba ganin yadda yake tada jijiyan wuya.
"Na san wace ce 'yata, na san me zata aikata." Ya ƙara faɗi tare da komawa ya zauna.
Takowa ta yi zuwa inda yake zaune yana huci ta kama hannunsa tare da zama a gefen kujerar.
"Jannah fa 'yarmu duka kuma mafi soyuwa a garemu. Kawai na shiga ruɗu ne ya sa na faɗi hakan. Wataƙila ba ta gana sanin wace ce ita ba shi ya sa take son gingimo abin da zai sanya ta kasa zaman lafiya, domin mundin ta tursasa auren nan sai Jannah ta zamo sanadinyar wargaza zumuncinmu da Ya Muhammadu. Sam jannah ba matar da za a nema wa wani bane, don ko wanda take so ya aure ta sai ya yi matuƙar kai zuciya nesa zai iya zama da ita."
Saki ya yi ya kauda kansa bai ce mata komai ba domin duk laifin ta yake gani don ita ce ta ɓata komai kuma ta ruguza komai.
"Kai ina jin Hajiya Baaba wasa take mini, ko kuma ta yi hakanne don na dawo da tunna ta kasa ba sanar dani dalilin son aurar da ita.
Miƙewa ya yi bai ce mata komai ba zai shige ɗakinsa.
"Please injiniya, say something don't go." Ta kama hannunshi tare da marairaice fuska tana faÉ—in hakan kamar za ta yi kuka, wanda ya sa ya koma ya zauna tamkar umurni ta yi mishi amma bai ce komai ba zuwa can ya ce,
"I was very surprised Halima, ace kin iya buÉ—e baki kina faÉ—in 'yarmu doesn't has table manners."
Kanta ta dafe jin abin da ya ƙara faɗin tare da furta
"Ya salam! Please understand me, I didn't mean that."
"Even if you mean it, ai duk laifinki ne da kika kasa bata tarbiya, saboda rashin yafiya kika gudo da ita Ƙasar da take da bambanci da addininki da al'darki. I really regreted the day I came to stay with you." Ya ƙarashe maganar yana kallonta cikin ɓacin rai tare da ɗorawa da cewa,
" Na san wace ce Hajiya Baaba na san artabun da na sha da ita, in har ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta. Baba Bukar ne kuma ba shi a duniya. Sam ba zan ja da maganar ta ba, domin Jannah ta samu miji kamar Ajmal abin alfahari ne a gare ni, kuma sannan ina son ta auri É—an É—an'uwanki saboda za ki fi jin zafin rashin bata tarbiyar da ba k.."
"Enough injiniya, saboda na nemi shawarar ka sai ka fara gasa mini maganganu? Kuskure na riga na yi kuma ba zan iya gyarawa ba, don haka ban ga amfanin zama kana gasa mini magana kamar 'yarka ba."
Ta nisa tana share zufar da ya keto mata a goshinta tare da faɗawa kan kujera ta rintse idanunta, saɓanin da take tsaye tana magana cikin tsananin fushi.
"Har kana da bakin faɗin haka? Bayan kaine sanadin da ya sa na baro Ƙasata nake rayuwa cikin kewa da ƙunci. And now you have the audacity to say that to me?" Ta dasa aya da tambayar haka sai kuma ta ja tsuka ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki.
"Please am sorry, I exceeded my boundaries. Perdon me, I couldn't do it again, but you know the way we raised her wasn't the right way, we should have inculcated good morals to her."
"Is fine ya wuce, amma yanzu bai kamata mu tsaya wannan maganar ba, mun riga mun yi kuskure. Maganar auren ta ya ke damuna, I really don't know what to say."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 22-23*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*