← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 79

Sashe 19

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta ije watar cikin tsananin tausayawa halin da suke ciki. Ije wayar ta yi, ba tare da ta tura mata da reply ba.
Maigadi na buɗe gidan idanunta suka hango mata dad da yake zaune a swimming fool, hannunsa riƙe da jarida yana karantawa, yayin da idanunsa yake sanye da farin tabarau.
Da sauri ta yi ƙoƙarin kauda abin da take ji game da shi, wanda ba ta gane tsana ce ko haushinsa take ji ba, don tana ganin shi ne silar duk abin d ya faru da rayuwarta.
Kafin direba ya gama perking ta buɗe murfin ƙofar ta fice cikim hanzari, ba tare da ta ɗauki komai ba, tana wani irin tafiya, wanda hakan ya yi matuƙar tayar da hankalinsa matuƙa, domin tun da ya ganta haka ya san babu lafiya. Tunanin hakan ya sanya ya yarda jaridar ya bi bayanta hankalinsa a tashe, ya yin da zuciyarsa ke fargabar isa gareta don ya san yau sai Allah a tsakaninsu.
"What's wrong Halima, are you alright?"Ya ƙarasa maganar yana kamata.
Watsa mishi idanunta da suka rine ta yi tana masa mugun kallo wanda ya sanya zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
Dafe kansa ya yi da sauri ya zauna a kan kujera don ya san yau gidan akwai tremendous problem don ba ya tunanin za ta ba bar shi ya kurɓi ruwa lafiya, dama haka take yi in har ta shiga irin mood ɗin kasancewarta mace mai zafi.
"She is in trouble sir. Please try to pacify her."
Escort É—inta ya furta tare da ije mata jakarta da takalmin sauran tarkacenta ya fice.
Ya bi ta da kallo daidai lokacin da ta ƙarasa cikin ɗaki tare da buga ƙofar da ƙarfi! Dabas ya zauna a kan two seater, ba tare da ya bi umurnin zuciyarsa da take mishi umurin ya bi ta ba amma tunawa da ya yi, she could hurt herself, sai ya zabura tamkar wanda aka yi wa allura ya bi ta, har yana tuntuɓe da center table, amma bai kula ba.
Ilai kuwa domin sanin hali yafi sanin kama. Ya same ta tana ta bubbuga kanta a jikin gado.
"Be patient Halee. "Ya furta cikin tautausar murya tare da haÉ—ata da jikinsa.
"Haka zan cigaba da rayuwa ina mutane suna ha'inta na? Mai na yi nake fuskantar hakan? Mai ya sa mutane suke son ruguza kyakykyawar ninyar da na ɗaukarwa al'ummata. Ina tsananin tausayin talaka da halin da Ƙasarmu da wasu ƙasashen suke ciki, amma mutane sun son burina ya tashi a tutan ma'aho. Wurgi ta yi da laptop ɗinta.
Da sauri ya ƙara rungume ta ganin ɓarnan da take yi.
"Calm down. What go up, must come down..."
Wani irin kallon ta yi mishi da ya sa sauran maganar ta maƙale a bakinsa, sai ya ji duk kalaman da tattara su don ya rarrashe ta da su sun ɓace. To me yake son ya ce mata, kasancewar she was a victim because of his selfishness. Idanunsa suka canza kala, sai ya ji ya kasa cewa komai.
"Hence, I need to quit my good intentions." Ta ce tare da wurgi da É—ankwalinta ta fice daga É—akin.
Tsananin ɓacin rai ya ƙara shigarsa, idanunsa suka kawo ruwa, amma sai ya yi namijin ƙoƙarin mai da su ta hanyar jan ajiyar zuciya mai ƙarfi, yana jin yadda zuciyarsa ke zillo tamkar za ta fito wajen.
Kusan minti goma ya na zaune a gurin ba tare da ya motsa ba, tunani barkatai suke damun zuciyarsa, wanda ya kasa samun mafita a cikin su. Kimanin 'yan daƙiƙa, ya yi nasarar miƙewa ya yaye labulen dake jikin windon yana kallon waje, ya yin da yake jin matuƙar haushin kansa akan yadda ya biye zuciyarsa ta yi galaba a kan farin cikin rayuwarsa.
Lokaci guda Jannah ta faɗo masa sai ya ji duniyar da abin da ke cikinta na son gimshe buƙatunsa.
Idanuwansa sauka hango masa ita da take tsaye a gefen filawowi, tana riƙe da wayarta, wanda ya tabbatar da hoton Jannah take kallo, domin y lura ko shi kansa bai yi kewarta kamar yadda ta yi ba, tana dai dojewa ne.
Hawayen da take ƙoƙarin mayarwa suka gangaro a saman kyakykyawar fuskar da yake tunanin ba ta cancanci zubar da hawaye ba. Sai ya ji tsanar kansa da damuwa sun ƙara ninka na da. Sakin labulen ya yi, yana mai jin yadda zuciyarsa ke ƙara zarginsa.
Mom ta ɗuke idanunta daga kallon hoton Jannah da take yi, wanda suka yi a lokacin da ta rakata Ƙasar India. Idanunta suka ƙara kawo ruwa, har tana jin yadda zafin su ke toya fuskarta.
"Ina matuƙar son Jannah. Why Jannah? Mai ya sa ki k zaɓi cutar da zuciyata ta hanyar nisanta kanki da ni?" Ta furta tana shafa hoton.
Sai ta rungume wayarta ta ci gaba da cewa,"Don Allah ki dago gare ni, kamar yadda ba zan iya komawa Nigeria ba, haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba. Allah shi ne shedata a kan irin ƙaunarki da na ke yi, amma sai kika sanya shamaki a tsakaninmu."
Tsakon da ta tabbatar ko ta tura ba za ta duba ba, kamar yadda take tura mata, amma ba ta duba wa ta ƙara turawa cikin sanyin jiki, tare da fatam Allah ya sa addu'arta ta karɓu ta duba.
Jannah ki dawo gare ni. Mahaifinki da kika fifita kura ne da fatar akuya, amma wallahi na fi shi sonki. Burina na taimaki al'umma, kuma dole saina tara kuÉ—i zan yi hakan.Tura mata ta yi ta online cikin karayar zuciya.
Zama ta yi a gurin tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tana jin wataƙila kukan da ƙarfi zai rage raɗaɗin da zuciyarta take ciki.
Wani irin tsawa aka saki mai razanarwa lokaci guda aka fara iska, mom ko motsi ba ta yi ba, ballantana ta nemi tsira da ruwan dake shirin gocewa.
Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

*KURA DA FATAR AKUYA*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 8-9*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta, ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi, wanda hakan ya sa ta ƙi jirgawa ta ci gaba da kukanta mai amo da gunji, domin tana ganin saukar ruwan wani dama ne da Allah ya ba ta wanda za ta yi kukanta, ba tare da kowa ya ji ta ba, domin kuka rahma ce daga Ubangiji.
Haka Allah yake. Duk mulki da tarin dukiya da mutum yake da shi, ba ya rasa abin da Allah zai jarabce shi, domin cikin littafinsa mai tsarki ya na ce wa,
"Shin mun halicce ku, tunanin ku ba za mu jarabce ku ba."
"Ga misali da ni Hajiya Halimatu, uwa ba da mama, na shahara kuma Allah ya azurta ni da dukiyar da ko ni kaina ba na tunanin na san adadinsu, amma sai ya yi mini jarrabawar da na gwammace gara rashin dukiyar." Ta faÉ—a cikin ranta.
Tana wurin har aka gama ruwan, a lokacin har duhu ya fara yi sannan ta shigo gida, tana jin wani sashi daga cikin damuwarta ya ragu.
A falo ta fara ƙoƙarin cire doguwar rigarta har ta ƙarasa shiga cikin ɗakin. Kai tsaye bayi ta wuce ta yi wanka, sannan ta fito cikin rigar wanka. Busar da kanta ta yi tare da shiryawa cikin gajeruwar baƙar riga. Da sauri ta ƙarasa dining jin yadda 'yan hanjinta ke zillo suna neman agaji. Ba wani ci da yawa ba, ta miƙe tare da yin brush, ta canza kayanta zuwa kayan bacci. Ba ta yi bacci ba sai da ta tabbatar da ta samu visa, jirgin zai ɗaga karfe tara na safiyar gobe, sannan hankalinta ya kwanta.
Kwanciya ta yi, tare da jan ƙaton bargo ta kwanta idanunta a rufe kanta da shi lokaci guda bacci mai ƙarfi ya kwashe ta.
Washe gari kasancewar ta san tana da tafiya sai ba ta yi dogon bacci ba, ta shirya cikin gaggawa. Hankalinta a kwance ba tare da tunanin komai ba, ta isa filin jirgi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa Ukraine
A cikin jirgi ta zabga takumi hannu biyu-biyu, domin wannan tafiyar ya tuna mata da tafiyar da suka yi zuwa India da irin shirmen da ta rinƙa mata. Ciro wayarta ta yi tana kallon ta cikin tsananin shaukin soyayya.

Dad da yake zaune a katafaren falonsu yana ƙunar rai. Duk da cewar wannan karon ba shi ne karo na farko da ta ke yin tafiya ba tare da izininsa ba ko saninsa. Sai dai, wannan tafiyar ya fi masa ciwo. Ta ke ya yarda kuma ya amince cewar da 'yan'uwansa suke ba shi da kataɓus ya zama mijin-ta-ce, domin shi kansa ya aminta da hakan.
Lokaci guda tausayin Jannah ya kama shi na nisanta kanta da su, duk a dalilin su samu zaman lafiya, amma zai iya cewa komai ƙara rikicewa ya yi. Anyway ko ba bu komai, in har tana cikin farin ciki a inda take sai ya yi mata fatan alkhairi.
Chapter 19 · 0% Book details