← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 79

Sashe 20

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

NIGERIA
Jannah zaune a cikin falon Hajiya Baaba tana kan doguwar kujera. Ta haÉ—e fuska sai kubbure-kubbure ta ke yi, sakamakon yau ko baccin kirki Hajiya Baaba ba ta kyale ta ta yi ba, ta bijiro mata da rigima. Yanzu É—in ma kallon ta yi tare da zabga mata wata uwar harara ta ce,
"Kin san Allah ba zan zauna ƙazama ba, dube ki mace har mace amma ko ɗan kamfai ba kya iya wankewa, kuma wai abin takaici kike kiran kanki da mace."Ta ce tana kallon yadda take ta jijjiga tare da ƙara harararta. Sai ta ɗora da cewa,
"Ke fa gabakiÉ—aya rayuwarki matsala ce, domin in za'a sanya ni rubutu akan matsalarki wallahi saina cika littafi. Mace ba addini ba iya iya girki ba tsafta. Kullum sai shan kaÉ—e-kaÉ—e da raye-raye. Yarinya sai ka ce dangin dujal. Ke ni da tarihi ya zo cewar a mace dujal zai zo sai na ce ya bayyana a jikokina."
"Kin ga Hajiya ki daina ce mini Dujal."
"Rufe mini baki ina magana kina magana shashasha kawai!" Ta kai mata bugu da carbin da ke hannunta, wanda ta ji zafi sai ta saka kuka sosai." Kika duke ni? Wallahi saina gaya wa dad, kuma ba zan ƙara kwana a sashinki ba." Ta ce cikin tsigar shagwaɓa.
"Au iyye kashe ki na yi ba duka ba, É—an wannan shauÉ—ar da na kai miki? Taf ai ko kina da aiki, don wallahi gidan kowa ya sanni duka nake yi, ke hatta Ajmal ban raga mishi ba, kuma kifi ruwa gudu."
"Ashe ko wallahi za ki dukan ma kanki, domin na san right É—in.."
"Au ramawa za ki yi?" Ta tambaye ta cikin sauri tare da ƙara kai mata bugu.
"Ni bance ba, amma kuma ni ban san mai zai faru ba."
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Hajiya ta ce tana salati tare da tafa hannayenta.
"Oh ni jikar mai gishiri. Ina ta murna jikallena za ta zo, zan huta da waɗancan marasa mutuncin ashe, lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi za'a kawo mini. Ko da yake ni dama tun da na ga idanunki ya soye na san cewar kura da fatar akuya ce ke."
Jannah ta buga kafafunta don ba ta gane karin maganar da ta yi mata ba, sai kawai ta É—auki wayarta tare da tare sakin kuka.
"Dad zan kira na gaya mi shi kirana kike da sunayen sabbobi."
"Kira shi don ubanki. Daga shi har uwar ta ki ba su ishe ni na. Yo ni da ake jifana da tsafi amma na kasa taɓuwa, ballantana ke da iyayen na ki da kuke shashashu, ba ku riƙi komai ba sai aƙiddar banza ta yahudu da nasara. Ani na sha tabara na sha yasin tun ina ciki."
"Oh ko me kika ce dai ba zan saka atamfar nan mai kama da ruwan tumbuɗi ba. Mom na sanya atamfa amma ba irin wannnan marasa kyau ba, don haka dad zan kira ya turo mini kuɗi na siyo zaɓin raina"Ta ce cikin sangarta da shagwaba tare da dorawa.
A haka na taso, Kuma tarbiyar da 'yarki ta ba ni kenan, don haka masu aiki za'a É—aukar mini.
"A'a bayi za'a siyo miki, ba masu aiki ba. kuma wallahi ba ki isa ki rinƙa zama mini a gida tsirarara ba. Ki gode wa Allah, da na ba ki atamfofina da ake siya mini duk sallah."
"Ba na so. Na lura "yar dirama ce kuma wallahi na fi ki iya tsiya." Ta ce cikin tsiwa.
"Ashe ko za'a kwashi 'yan kallo, ba ki san wace ce Hajiya Baaba. Lokacin ƙuruciyata saɓa ƙato nake na nuna ma Allah na buga da ƙasa, sai da na gagari hatta mai-gari ballatana ke karan kaɗa miya kina ji da kwakwankaso kamar an ɗaurawa tabarya zani"
"Ki dai ce komai, islamiyar ma ina dama ba zan je ba."
Da sauri ta dawo tana jifan ta da kallo ta ce,'Inda kika yi kaɗan kenan, daƙiƙiyar banza kawai."
Haƙura ta yi da neman dad sakamakon layinsa da ya ƙi shiga, sai ta miƙe tana harararta har da su muguɗa baki, wanda hakan ya ƙara ƙular da Hajiya ta bita a guje har zuwa bakin falo. Tuntuɓen da Hajiya ta yi da ƙofa ya sa ta daina gudun tana nishi.
"Wayyo Allahna! Wanann sheɗaniyar yarinyar ta ja na fasa ƙafa! Allah ya isa tsakanina da ke."
Jannah da har ta shige sasan su Aby ba ta ji me ta ke cewa ba.
"Hello dad ka na ji na? Please I need to upgrade my drower." Ta furta cikin shagwaɓa tare da fatar Allah ya sa ya ba ta kuɗi da yawa tana son ta yi sub na data don kuɗinta yawanci a data da chaculate yake ƙarewa.
"Ok, I will send you 200k, but please do answer your mom's calls."
Jan numfashi ta yi jin abin da ya ce."But dad.."
"No kar mu yi haka dake, ki bi umurina. Mahaifiyarki na buƙatar ki. She is in depressed and she needs your acompany. Trust me she really adore you."
Wannan karon shiru ta yi na É—an lokaci domin tunaninta ya ba ta kawai yana faÉ—in haka ne don ya shirya su, ko kuma ta hura masa wuta da rashin mutuncinta kullum.
"Ni gask.."
"I said please! For the sake of me."
"Shikenan ta ci albarkacinka I will give her a call."
"Good girl. I know you will.
Sure, why not dad?" Sai ya yi dariya yana jin daÉ—in abin da ta ce.
"But seriously dad, don't put the blame on me. Don har yau ina jin babu daÉ—i yadda take yi maka. Ka duba yadda ta É—ora ma kanta wahala kula da duniya, amma a gidanta ta kasa bamu farin ciki. Shugabanci a gida ake fara yin sa. I knew tafiyar da ta yi, shi didn't seek your permission. Arrogant woman kawai."
"Well, my girl I see you poin, but please na ga ya miki your mom has good intention and she is doing the right things."
"Oh please dad! She isn't, you are just depending her as you do always." Dariya ya yi sosai jin me ta ce.
"Ni dai ƙara roƙon ki na ke da ki kira ta, support her and encourage her for havean sake, will you?"
"Sure I will, za ta ci albarkacin son da na ke maka." Ta ba shi amsa.
"Promise?" Ya ce cikin muryar roƙo hakan sai ya ba ta tausayi matuƙa, ta san cewa mahaifinta na matuƙar son ta wanda dalilin da sanya take garasa kamar ƙwallo.
"Saboda hakan zan tura miki da 300k sai ki saya harda abayoyin da mom ɗinki take sawa, yauwa ba ri na zaɓa miki colour."
Sai ya É—an numfashi yana tunanin can ya ce,"Uuummmm! Pink, pich, and purple. It will fit you, like it does to your mom. Ba ki ga kalar da ta sanya ba da za ta yi tafiya ash colour, sosai ta yi kyau. Tamkar na sace ta na gudu. Yauwa ki haÉ—a har da ash."
Dariya suka yi sosai yana faÉ—in." Your mom is really beutiful and she has Charming charisma.."
"Dad, kai ma fa wani lokaci ba ka iya controlling kanka a kan soyayyar da kake mata shi ya sa ta yi ta gara ka kamar ƙwallo. Please do pretend you don't, don ita ma pretending kawai take yi, amma ai tana sonka, don babu macen da za ta kalle ka ba ta kware ma ka ba."
Sosai ya ji daÉ—in abin da ta ce."Ya zan yi Jannah? Ba ki san soyayya ba shi ya sa., kuma ke yarinya ce har yanzu..."
"Common dad am not under age, am 18years. So am full grow woman."
"That is why I keep calling you baby." Ya furta tare da kashe wayarsa yana faÉ—in,"Bye do take care of youself."
Ya faÉ—a jin abin da ta ce ya yin da zuciyarsa take cike da farin ciki don ya san in har ta kira zai samu sausauci daga gurinta.
Rungume wayar ta yi cikin farin ciki matuƙa domin tana matuƙar son mahaifinta.
Suna gama wayar sai ga alert ya shigo daga gurinsa. Murmushi ta yi mai sauti. Wayarta ta ciro ta tura mata da tsaƙo hi, wanda ko sakan biyu bai ya ba sai ka kiranta. A gadare ta ɗauki wayar.
"Wane ne?"
Zuciyar mom ta karye sai ta ji babu daɗi duk da ta san ta yi hakanme don kawai ta ɓata rai, amma ta san cewa ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta numbarta ba.
Chapter 20 · 0% Book details