← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 79

Sashe 17

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Hajiya Baaba da ke sallah bayan ta idar ta ji dirin motar Ajmal, tun kafin ya shigo ta fasa yin azkar na sallah ta miƙe tare fita.
"Ja'iri ma za fito daga motar nan, yau ni ko kai a gidan nan."
Ganin ta tsaye tana jijjiga ya dafe kansa."Kai wannan tsohuwar ta zame mini ƙadangaren bakin tulu." Ya ce, tare da ƙin fitowa daga motar.
"Ai wallahi ko kwana za ka yi, sai na jira ka ka fito. Ka gama tozarta ni, ka kwance mini zani a kasuwa. Na tabbata da iyayenka ne, ba za ka yi musu haka ba."
Hamdala ta yi jin hon ɗin motar Aby." Yauwa zo nan Muhammadu, gara da Allah ya kawo ka, daidai lokacin da ake buƙatar ka, sai a yi komai a gaban ka."
Ta ƙarashe maganar tana isa gurinsa da ko gama parking bai yi." Dube shi mara kunya, ya kasa fitowa. So na ke ka zana mini tsakani da shi, don ko mutuwa na yi kar ya zo kan gawata."
"Suhanallahi ashsha! Hajiya mai ya kawo wannan magamar ke da angon naki?" Ya ce, cikin tsigar tambaya.
"Allah ya tsare ni da uren miji mai baƙin hali irin na sa, ai da haka uban ku ya ke wallahi ko kaza ba zan haifa da shi ba." Ta ba shi amsa.
Ajmal tsaki ya yi, ya galla mata harara ji ya ke kamar ya shaƙe ta.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K

*KURA DA FATAR AKUYA*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 7-8*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Allah ya kyauta ni ko mutuwa zan yi ba aure ni ma gara na mutu, da na auri mace mai hali irin na ki." Ya furta a a ransa, sai kawai ya yi shahada ya buɗe ƙofar ya fito.
"Sannu da dawowa Aby, Hajiya barka da yamma." Ya furta tamkar babu abin da ya faru tsakaninsu.
"Riƙe gaisuwarka Adamuu, daga yau ba na so, in dai akanta ne za ka nemi kashe ni na haƙura. Kai ni ko atiti kar ka nuna ka sanni, inda na gode ma Allah, sam ba ka yi kama da ɗana ba, sai dangin dagiro."
Shiru kawai ya yi yana kallonta domin shi kansa Aby ya ka sa ce mata komai.
"Mu shiga ciki mu sasanta. Sam ba ka gudun fushina Ajmal, kullum ina gaya muku ku rinƙa kiyaye doka don a zauna lafiya, amma kai ne babba babban banza, ka na girma kana cin kashi, saboda kullum da ga gareka fitinar take tasowa."
Ya yi shiru ko zai ce wani abu, amma sai ya ƙi cewa komai, yayin da ransa ya ƙara ɓaci sosai, domin ya yi matuƙar wahala so yake ya huta.
"Dole na yi wa Hajiya biyayya, don na samu na gama lafiya, sannan duk wanda ke son zaman lafiya, dole ya yi mata biyayya."
"Ehe ga ya masa ni dakali ne dole a zauna da ni. Dukannnin ku albarkacina kuke ci, saboda ɗanane, ni na haife shi ba uban wani ba." Ta ƙarashe maganar cikin gadara da iko, har wani hura hanci take yi, sai kuma ta ɗora da cewa,
"Ai ni na san da arzikin shi na ke ci, da tuni ya sanya mini guba na mutu." Aby ya kalle sa da ya haÉ—e rai, burinsa kawai ya ji ya watsa ruwa a jikinsa.
"Don haka sai ka kiyaye, karka ƙara yunƙurin kashe mini uwa." Ya ce.
"Ka yi mana tsakani kawai." Ta ce tana kallo Ajmal da yake shirin miƙewa.
"Haba Hajiya ki bi abin sannu-sannu, kuma kin ga na yi masa faÉ—a, dukanninmu ikon ki ne."
"Humm." Ta ce tare da ƙara tsuke fuskarta sai ta ɗora da cewa,
"Da ma dai wasu 'ya'yan ba wannan ba, an riga an gama musu huÉ—ubar tsiya, tare da dasa musu tsanata a zuciyarsu."
Karamin tsaki ya ja tare da fara tafiya." Shikenan, zan kiyaye ba ri na shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin buɗe ƙofa.
Chapter 17 · 0% Book details