← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 79

Sashe 10

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

LONDON A yau safiyar Monday aka tashi da hazo ya rufe gidaje, wanda sakamakon hakan ya ɗaga hankalin mom ƙwarai, domin ta san ba karamin ciwo Jannah za ta yi ba. Duk irin ɗumama ɗakin da room heater da ta yi, amma hakan bai yi wani tasiri ba. Jannah kwance akan makeken gadonta wanda ta koma can gefe ta rukuɓe cikin blanket. Gabakiɗaya jikinta rawa yake haƙoran sai haɗuwa suke yi tamkar za su fasa fatar bakinta. Hannunta mom ta janyo tare da ɗorawa akan cinyarta lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ganin yadda take yi tamkar zata fasa gadon ta shige. Ta miƙe tare da janyo ledar magani mai ɗauke da tambarin pharmacy ta ciro maganin da ta bata ba da jimawa ta ɗauki ruwa tare da hawa kan gadon. "Please kar ki taɓa ni don Allah kar ki buɗe bargon nan, sanyin nan ba zai bar ni ba, domin kamar numfashina zai ɗauke." Ta faɗa cikin rawar sanyi tare da ƙara ƙuɗunɗune jikinta a cikin bargon, sannan ta riƙe shi sosai yadda ba zata ita janye wa daga jikinta ba. Tsananin tausayin ƴar gudaliyarta ya cika mata zuciya. Miƙewa ta yi tare da jingina kanta da mirrow. "Tabbas ya kamata na kawar mataki akan ciwon nan, ba zan iya ganin 'yata a cikin wannan halin ba, hakazalika ba na jin zan iya komawa Nigeria." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Dad ya yi sallama ya shigo tare da dosan kan gadon da take kwance ba tare da ya kalli in da take ba. Kan gadon ya zauna tare da janyo ta ta kwanta akan jikinshi yana shafa kanta, sai kawai ta fashe da kuka cikin muryar kuka tace. "Daddddddddi." Ta ja fasali tare da cewa, "Sanyi nake ji!" Ta ci gaba da kuka cikin muryar shagwaɓa. Shafa kanta ya yi, ya ɗaga idanunsa ya kalli mom da ta yi kamar ba ta san da shigowarsa ba ya ce, "Jannah za ta koma Nigeria zuwa gobe in sha Allahu yau zan kammala mana visa sai ki fara shiri.Ya karasa maganar cikin ɗaga murya. Wani irin kallon hadarin kaji ta yi ma sa tare da taku biyu ta isa gare shi, idanunta cikin na sa ta fara magana. "Ka san me kake faɗi Jabir?" Ta kira sunan shi ba tare da shakku ba, sannan ta ɗora da cewa, "Umurni kake bani akan rayuwata kuma yata da na haifa wacce ba ni da kamarta?" Dariyar takaici ta yi tare da fara taku ta matsa nesa da shi ta tsaya. "Idan har kana tunanin zan bi umurninka na koma gida, tabbbas ka yaudari kanka, domin hakan ba zai tama faruwa ba. Don haka ka daina wannan mafarki, domin ba zan koma ƙasar da zata zamo maƙabarta a dare ni ba. "Halima!" Ya kira sunanta cikin ɗaga murya tare da daka mata tsawa, sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya bari ta furta komai ba. "Ki sani daga yau ba zan ƙara lamuntar mugayen kalamai daga gare ki ba, ya isa iya wanda kika gaya mini. Ina jin zuciyata zata iya bugawa in har ban ɗauki mataki ba." Ya ɗan jinkirta tare da rage murya ya ƙara matsawa gareta. "Na gaji Halima ki sani mi mijinki ne, uban yarki, ina da ikon na ba ki umurni kuma ki bi, saboda duk matsayinki a ƙarƙashina kike, don haka ki iya kalamanki kar kiyi dana sani!" Wani banzan kallo ta yi mishi lokaci guda idanunta suka fara zubar hawaye."Yanzu kake da bakin faɗa mini waɗannan kalamin, bayan ka ɓata rawarka da tsalle. Na ce ba zan koma ba kuma ba zan bi umurnin ka ba, don haka duk abin da zaka iya ka yi ba ni da haufi a kansa." Girgiza kansa ya yi cikin takaici lokaci guda idanuna suka kaɗa tamkar garwashin wuta. "Do you know that Jannah is dealing with a mental disorder, and she’s in therapy secretly That’s cause of your careleness." Idanunta ta zare tare da Kallon shi cikin tsananin mamaki. "What! Are you crazy? Ka San me kake faɗi Jannah ce in her age take shan waɗannan pills ɗin?" Sai kuma ta girgiza kanta tana faɗin, "Impossible! No way this could ever happen!" "Saboda kin ba ta kulawar da ko wace uwa take ba wa 'ya'yanta? Sam ba ta yi miki komai ba, i dar har ba za ki iya yafe mini laifin da na yi miki ba, to ki hukunta iya ni din kawai." Kuka sosai ta sa tana dukan shi tare da cin kwalarshi. "Anya zan iya yafe maka Injiniya? Ka cutar da rayuwata." Sai kuma ta sake sa da ko gezau bai yi ba ta kai mata mari. "Ashe dama mahaukaciya ce ke ban sani ba? Kin san me kike son jawo ma kan ki, kin san irin side effects din da suke da shi." "Leave me, mom! Do you even care about ne?" Ta ce tare da fisge rigarta tana mata wani irin mugun kallo. "Yes, I know all the side effects.” Ta ja numfashi tana kallon dad cikin tsananin mamaki don ba ta taba tunanin ya san tana sha ba kuma Bai tana muna mata ba ko da wasa, lallai yana matuƙar sonta. "Amitriptyline’s for dealing with depression and anxiety, but it also works as a sleeping aid if you can’t crash. Olanzapine’s mostly for depression too, but it can help with eating disorder and can knock you out for some sleep too." Ta furta cikin rashin shakku sai duma ta ɗora da cewa, "Na sani, amma amfani nake don na samu sauki da bacci. Sam ba na iya bacci da karatu, Kuma kin takura mini da dole sai na yi karatu, bayan kin kasa zama da ni, ki bani farin cikin da zan iya mai da hankalina na yi karatu da shi." Sai ta karashe maganar cikin kuka sosai har tana sheshsheƙa. Dad ne ya ɗora da cewa, "In har ba za ki bi umurnina ba dole na ɗauki mataki domin ba zan yarda na zamo mijin tace ba. Na kashe rayuwar 'yata daya da Allah ya ba ni Ina ji ina gani." Ya karashe cikin ɗaga murya. Dariya ta yi mai sauti sosai har ta tafa hannu kamar ta kalle shi sheƙeƙe, duk da cewar ta yi matukar razana da jin abin da take yi, amma hakan bai sanya ta sauko daga dokin na ki da ta hau ba, sai dai ta dauko aniyar daukar likitar da za ta kula da ita har ta daina. Kallon shi ta yi cikin raini ta ce, "Yanzu ka san da wannan? Yanzu ne ka san akwai matakin da za ka ɗauka. Ai tun tuni kake jiran wannan lokacin, don haka gara ka ɗauki ko wane irin mataki, karka damu da ni na shirya tsaf wannan ranar nake jira." Ransa ya ɓace hankalinsa ya tashi ya dafe kansa yana jin yana sara mishi tamkar zai rabu gida biyu, sau biyu yana ƙoƙarin magana, amma duk lokacin da ya buɗe baki sai ya ji wani irin baƙin ciki mai kama da ƙwallo ya taso ya tokare masa maƙogaro kuma ya ƙi wuce wa. Tabbas a yau ya gane ta gaji a zama da shi nemar hanya take yi. In kuwa hake ne bata yi masa adalci ba, musamman ƴarsa da yake ganin ta fi buƙatarta fiye a shi, sai dai ta yi nisa ba ta jin kira. A hankali ya buɗe bakinsa domin ya furta abin da ya san daga bakinsa ne ko iya leɓensa, amma ba daga cikin zuciyarsa ba sai ya ji ya kasa, musamman da ya juya ya kalli Jannah da take ta kuka tun da suka fara muhawar kamar yadda ta saba kuka duk lokacin da suke sa'in sa, sai ya ji matuƙar tausayinsa. "In har da gaske kike kin shirya karɓar duk matakin da na ɗauka to ki...." "Daddiiiiiii." Ya ji muryar Jannah ta kira sa tare da janye bargon da ke jikinta ta sauko daga gadon ta ƙaraa gurin shi tare da rufe masa baki. "No daddy.” Tace cikin matsananciyar kuka tana yi wa mom wani irin kallo. Sai ta juya ta kalle sa tare da girgiza masa kai, duk da cewar ita kanta a wannan lokacin ta fara tunanin rabuwar iyayenta shine kawai matsalar rikicin da sike samu, domin tana gani auren da babu zaman lafiya rabuwa yafi, tun da har ba zata iya yafe masa ba, amma ba akan dalilin ta ba. Sam bata son iyayenta su rabu saboda ita gara ace akan matsalar da suke samu ne, don haka ta girgiza masa kai a karo na biyu cikin kuka tace. "Idan har a kaina zaka rabu da mom don Allah dad ka haƙura na koma Nigeria ni kaɗai karku damu kuyi zaman ku, amma ina roƙon ka don Allah ka kai ni gidan Abby zan fi samun natsuwa a can tun da akwai sa'oina don Allah." Ta ƙarashe maganar tare da ƙara rushe da kuka. Dukkkannin su jikinsu ya yi sanyi dad ya kama hannunta cikin tausayi tare da shafa kanta. Hannnunsa ta kamata haɗe tare da riƙe su duka. "Please! Dad." Sosai ya ji tausayinta duk da cewar ya so ta zauna a gurin mahaifiyarsa, amma babu yadda zai yi wataƙila amincewar zai iya bata farincikin da suka kasa bata a matsayinsu na iyayenta. Sai ya juya ya kalle ta da ta yi halin ko in kula da su, sai cika take tana batsewa tare da kada kafarta, matukar bacin rai ya kara kama sa. Cikin raunanniyar murya ya ce mata, "Na amince, idan hakan zai ba ki farinciki fatana a ce ki yafe mini don Allah." Ya faɗa cikin muryar da ta ƙara bayyanar d tsananin ɓacin ran da y ke ciki. Murmushi mai kama da yaƙe ta yi. "Thanks." Iya abin da tace kenan ta juya ta koma ba tare da ta kalli in da take ba, yayin da wasu irin zafafafan hawaye suke sauka da ga kuncinta. Tsananin tsanar mahaifiyarta yake kara samun gurbi a zuciyarta. Mom ta yi shiru tamkar gunki ta tsaya tana jin ta zuciyarta kamar zata fashe. Zuciyarta ta gama haƙiƙancewa Dad ya zama azzalimi mai son kansa, domin duk abin da yake faruwa a sanadinsa ne shine ya zamo silar komai kuma
Chapter 10 · 0% Book details