← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 79

Sashe 69

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba kiranki na yi ki mini kirari da ƙarya da ƙarerayin da kuka saba na 'yan siyasa ba, wanda sai mun zaɓe ku ku fito da manufofinku na zalunci da yaudara."

Shiru ta yi tana jinjina abin da ta ce sai kuma ta gyara murya ta ce,"Amma kya yi mini fatan alkhairi na zamo ta ƙwarai na kuma banbanta da saur.."

"Ke kika sani Halima, ai ni kin gama sire mini tun da kika yi mini haka. Maganar auren Jannah, an saka rana wata uku sai ki fara shiri." Ta ce tare da gimtse wayarta ba tare da ta jira abin da za ta ce ba.

"Ka ji wai har ansa rana wata uku fa? Kai Hajiya ta É—auki lamarin nan da girma." Ta ce tana jinjina lamarin da tunanin halin da Jannah take.

"Humh, a rigimarta in ba an yi bikin nan ba ba za ta taɓa samun sukuni ba."

"Ina fatan ta ƙulla alkhairi."

"Amin, in sha Allahu." Cewar dad sai kuma ya É—ora da cewa," Ki ce zuwa Zariya rarrashi ya kama ni."

"Aiko dole don yanzu Allah kaɗai ya san halin da take ciku, kuma ga shi ko na kira wayarta ba za ta ɗaga ba. Ka ƙara gwadawa ko za ta ɗauka."

"Humh, kamar ba ki santa ba sai ta huce." Ya ce yana É—aukar wayar sa kira amma har ta gama ringing ba ta É—aga ba.

"Ni kam na rasa wane irin kaya zan yi mata domin so nake gidanta ya banbanta da sauran 'yayan duniya dole na kashe mata kuÉ—i."

Dariya ya yi jin abin da ta ce."Gaskiya ita ce ya É—aya tilo wanda Allah ya bamu. Yanzu fa shikenan, girma ya kama ki za ki É—auki suruki."

"Hararsa ta yi cikin wasa tana faÉ—in,"Ban gane ba ko ka barwa Ya Bala surukutan ne."

"A'a ni ai yanzu nake tashen kuriciyata, kin san zan iya aura mace budurwa ke kuma kwanannan za a fara ce miki kaka."

Dariya sosai ta yi jin abim da ya ce wanda har ya sa ta tashi da sauri zata kai mishi duka sai ya ruga ta bishi da filo yana maka masa.

"Allah ba ka da kirki, wato tsufata kawai kake hangowa ko injinjiya? Ko dayake in dai 'ya'yan Ajmal ne ina fatan ta haifa mini su da yawa domin zan yi alfahari da su, ban haihu da yawa ba ina son ta haifa harda nawa. Sai dai, kuma ganin yadda auren na su yake hakan zai faru?"

Ta ce cikin murya sanyi wanda ya sa ya rungumeta yana faÉ—in," In sha Allahu za su zauna lafiya auren nan sai mun yi alfahari da shi."

"Ina fatan hakan." Ta ce tare da É—aukar wayarta tana faÉ—in,"Bari na fara kira na gayi sa ranar na kuma fara shiri."

"Ah amara kirjin biki. Akwai lokaci ba."

"A'a barni Injiniya mai zurfin ido da wuri yake fara kuka." Ta fara kiran ƙawayenta.

Aby na fita bayan sun ɗan tautauna da Alhaji Umar wanda ya ba shi baki, da ƙara tausasashi kan su ci gaba da neman zaɓin Allah, sannan ya yi masa sallama ya rakashi har ya shiga motarsa ya tafi.

Ɗakinsa ya koma ya kwanta sharf! Yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
"Abby, jikin ne? Ko za mu je asibiti ko da yake bari na kira doctor Irfan."

"Karki kira shi na ji sauƙi don na sha magani a sahshin Hajiya."

"To me ya faru you look worry?" Ta ƙarashe maganar tara da dafa shi tana taɓa goshinsa.

"Akan maganar auren yaran yanzu Hajiya ta tursasa aka sanya rana wata uku."

"Sa rana?" Ta tambaya cikin tsananin mamaki da ruÉ—ani.

"Eh, dad ya naɗa ni waliyin Jannah, Alhaji Umar da ya ƙara tsayawa a waliyinsa."

"Ikon Allah!" Ta ce tare da nisawa. Sai kuma ta saki numfashi ta ci gaba da cewa,

"Ajmal É—in ya sani?"

"A'a da shi da ita babu wanda ya sani yanzu dai zan kira shi na sanar masa, Jannah ce ban san yadda zan yi ba you know how rude she is."

"You have to hurry, kafin ta kira su ta hargiza su ta yadda zamu kasa shawo kansu, domin ka san ba za ta gaya musu da dadi ba"

Wayarsa ya ciro da sauri don ya kamata tun tuni ya kira shi kafin ta kira don da biyu za ta gaya masa don ya harzuƙa.

"Hello Ajmal, where are you?"
"At home dad, ai na zo gidan you were in ofis."

"Ok, can you come? We need to talk."

"Lafiya Aby?" Ya tambaya jin murya sa wani iri.
"Lafiya lau sai ka zo." Ya kashe wayarsa yana tausayinsa.

Ajmal ya juya yana kalon Mushiirat da ta fito daga É—aki cikin riga da wando iya gwuiwa rigar kamar singeleti.

"Zauji, ya ka gani? I told you it would fit me sosai."

Tsayuwar da ta yi masa ya tafi da imaninsa domin cikin jan hankali ta yi da gantsarewa.

"Wow you look amazing and nice in that outfit, ashe na iya zaɓe."

Dariya ta yi tare da rungume shi tana faÉ—in,"I told you."

Juyo da ita ya yi yace,"Kin yi kyau sosai É—in nan fa matar kirki, musamman hibs da waist É—inki sun É—auki kayan."

"Allah ko?" Ta ce tana canza tsayuwarta har sai da ya É—auke ta hoto da yawa.

"Eh, Aby ya kira ni yanzu, I'm thinking is urgently lemme go, I will be back soon, na ɓata gayun nan don ya tsokale ni."

Dariya ta yi ta kashe masa ido."Ok, waiting don Allah ko na biyo ka."

"No, za a yawo ko?" Ya ce tare da ficewa don kar ta ƙara ce masa komai domin baya son ta san da maganar auren Jannah sai komai ya warware.

Tsayawa ta yi a bakin ƙofa tana kallon shi har ya fita ta ƙara sakin murmushi ta koma ta zauna tana begen sa.

Ajmal kuwa, a hanya yana ta tunanin kiran sai ya ji gabansa ya faÉ—i tunawa da bai gaishe da 'yar mulki ba, wanda zuciyarsa ta zargi akan shi ne.

Ko da ya shigo bai leƙa sashinta ba kai tsaye shashin iyayensa ya shige.

"Abby, ga ni ina ta tunanin lafiya." Ya ce tare da zama a gefen kujerar da yake.

"Lafiya lau, kuma ni da É—ana don ya yi auren ya yi nisa dani ba zan kira in na so na ga ganshi ba?"

Dariya ya yi yana shafa kansa jin tsokanar da ya yi masa."Ba haka bane Abby, I was thinking something differently."

"To zauna ka natsu na so na ganka kuma a kwai maganar da za mu yi."

"Ok."Ya ce tare da ije wayarsa da take hannunsa ya tattara dukkan hankalinsa, ya mai da ga mahaifinsa ganin yadda shi ma ya yi serious ya san dama dole akwai wani abu, sai yana addu'ar Allah ya sa alkhairi.

"Ya maganar da muka yi shekaranjiya akwai update?"

"No, Abby amma har yanzu ina addu'a ban cire rai ba." Ya ce tare da zaƙuwar ya je direct to streat point ba ya tsaya kwana-kwana ba.

"Ok, Allah ya sa mu ji alkhairi."

"Amin." Ya amsa zuciyarsa cike da zaƙuwar jin musambabin kiran.

"Da ma na kira ka akan maganar auren ka da Jannah, an saka rana wata uku." Ya yi ƙarfin faɗin hakan domin tsoro da rawar murya ya ji.

"What Aby! Ni Jannah aure na ga gaya muku ba na sonta kuma ba zan aure ta ba."

"Calm down, and be matual Ajmal." Cewar Ammy da ta daga shi ganin yadda ya miƙe a razane jijiyoyin jikinsa suka tashi.

"No Ammy! Na gaya mata bana sonta, lafiya nake zama da matata, ban ga dalilin da zai sanya na ƙara second wife ba. Besides that ,am not interested in her so there is no way." Ya ce cikin ɗaga murya wanda har ya sanya su Jannah da suke ɗakinsu suka ji.

Zubbur ta miƙe kamar wacce aka tsikara."Rana ni da Ya Ajmal, aka sa? Ai dama wannan fitinanniyar tsohuwar ba ta bar maganar auren nan ba?" Ta ce tare da fara hawaye sai ta ruga sashin Hajiya Baaba tare da ta damu da kiran da su Ummu suke mata ba.

"Mene ne haka? Muna magana cikin sirri za ka ɗaga murya kowa ya ji.Tabbas yanzu aka sanya ranar da Jannah, kuma yadda ta nuna aure babu fashi, domin ko ƙwandala ba ta bari na biya ba."

"Ba zan amince ba, tun da bana so ai ba a aure dole, don haka sai ta janye sa ranar nan." Ya ce tare da ficewa daga É—akin ya yi sashinta ba tare da ya damu da kiran da suke masa, wanda suka rufa masa baya.

"Kin san Allah saimkin janye sa ranar nan, saboda na fita harkanki ko kallonko ba na yi don me kuma za ki dage sai an yi bikin."

"Don ubanki to za ki buge ni, ko ki tsare ni a fasa. A tunaninki shiru da banzan da na yi muku na ƙyale ku ne? Habawa yara sai ka ce ba ku san wace ce ni ba."

Ta ce tare da wafce rigarta da ta riƙe wanda ta sa kuka da faɗuwa ƙasa tana birgima.

"Ki fasa aurenan, na ce bana son shi in ba haka ba, saina sha guba na mutu."

"Kisha gubar bera in kin so, iyayenki kika yi wa asara ba ni ba." Ta ce daidai lokacin da Ajmal ya buga kofa da ƙarfi Yana huci ya shigo.

"Hajiya Baaba, tun ina miki mutunci ki janye maganar aurennan, domin ina da matata mai tarbiya babu yadda zan yi na auri jikarki fitsararriya."

"Au haba mai hurul ain, ai ba ka gaya mini matar taka daga sama aka sauko maka da ita ba saboda malinta, da ban damu kaina na aura maka wannan mara mutuncin ba, amma ka ga yanzu ka makaro sai dai a guji gaba. "
Chapter 69 · 0% Book details