← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 79

Sashe 35

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yi miki kiss, kuma ki rufe ido." Jin hakan ta hangame baki tana mamaki ta zare ido tare da haɗiyar miyau da ƙyar. Wani irin zazzafar kis ya sakin mata har uku sannan ya ce,"Bye, ki kular mini da kanki." Cikin tsananin razana ta saki kwanon furar domin saboda tsabar gulma kayansa ta ji ya ce ta kula da shi. Ƙarar faɗuwar kwanon ya sanya ya juyo da sauri yana kallonta wacce ta zura a guje ganin aika-aikar da ta yi. Sashin su Ummu ta same ta a falo tana waya da Huzaifah. Da sauri ta ja hannunta zuwa ɗakin Nahlin tana faɗin,"Humh zo na shafa miki labari, yau na ji abin da ya girmi kakata Hajiya Baaba. "Mai ya faru sis, give me the gist." "Sai da na gaya wa Anty Nahlin Ya Ajmal kura ne da fatar akuya, fakewa yake da addini yana cin karensa babu babbaka, wi shi a dole uztasu Ahlulu sunnah, amma ta shafawa idanunta toƙa ta ƙi yarda. Ga shi yanzu na gani da idanuna. Kun san me na ji yana faɗi wa budurwarsa?" Anty Nahlin ta kasa magana sai kaɗa kanta take tana mata nuni da shi da yake tsaye a bayanta, amma gulma na cinta ba ta lura ba. Ummu da ba ta ganshi ba ta ce," Do tell me now." Ta faɗa cikin zaƙuwa da son jin gulma. "Kiss guda uku ya yi mata, kum har yana faɗin ta kula mishi da kayanshi. Oh ni Jannah ko wane kaya yake da shi a gurinta oho? Ashe ya Ajmal gogaggen ɗan duniy..." Maganar ta maƙale mata a maƙoshi sakamon Ummu da ta yi mata alamun yana jin ta. Wani irin tsalle ta yi sai ga ta a tsakiyar gado, domin ko kaɗan ba ta taɓa tunanin zai biyo ta ba. Nahlin ta buɗe baki za ta yi magana ya daka mata tsawa,"Rufe mini baki shashashar banza kawai! Kin tsaya kina jin shirmenta." "Yi haƙuri." Ta ce tare da bin bayan shi ta wuce wanda Ummu ta bita a guje domin tsuntsun da ya ja ruwa. A ranta addu'a take Allah ya taimake ta ganin yadda ransa ya ɓace. "Yau zan yi maganinki, ba ke baki da tarbiya ba. A gidan uban wa kika ji na ce ta kular mini da kayana? Saboda kallon finafinai ya ɓata ki." "Am very sorry. Wallahi ba haka na ce ba, please understand me." Mari ya kai mata yana faɗin," I should understand what? Kin ɓata tarbiyarki kina son ki ɓata na ki, sannan ki sanya suna ganin mutuncina su raina ni. Wato dama you been spying on me?" "No, wallahi I don't, I really respect you. It was mistake please forgive me." Marin da ya ƙara kai mata ya sa ta canyara ƙara daidai lokacin da Ammy ta shigo. "Kai Ajmal, so kake ka ƙara janyo wata rigimar? Ma za yarda bulalar nan." Ta faɗa cikin ɓacin rai. What has she done to you?" "I really disappointed, having you as a sister." Ya ce tare da yarda bulalar ya fice ba tare da ya amsa tambayar Ammy ba. "Ba kya jin maganar Jannah, kina ganin kowa a gidan nan, kaffa-kaffa yake kar ya shiga gonarsa amma ke kullum cikin takalarsa, bayan kin san abin da zai je ya dawo." Wuri-wuri ta yi alamun rashin gaskiya sai jan majina take yi. Ammy ta juya za ta fita daidai lokacin da Ummu ta shigo."Sory sis, I was signalling you, amma ba ki gani ba. Dukanki ya yi?" Ture ta ta yi tana harararta." A, a albarka ya shi mini, tare da ba ni kyautar kuɗi. Ai wallahi na san matsayina da inda na aje ki, you left me in, wato ya kashe ni ba ki da asara." Ta faɗa tana harararta. "Am deeply sorry. Kin san halinsa, ya zan yi? Amma ke ɗin tawa ce." "In ban da neman rigima irin na ki, ina ruwanki da wayarsa ba matarsa ba to be ba ce? Kar ki manta it remains 26 days for their weeding." Zuɓɓura baki ta yi ba ta ce komai ba sai ta kama hannu Ummu."Kin ji muje sashin Hajiya Baaba." Shirye-shiryen biki ya kankama Ajmal babu zama duk da bikin gata ake masa amma shi kansa nuna bajinta yake yi. Kmar yadda mom ta yi alƙawari ita ta haɗa lefe na gani na faɗa wanda samun sa sai 'yar gata mai ƙashin arziki. Events kala-kala aka shirya duk da angon yana nuna ustazu ne amma hakan bai hana tsara bikin yadda zai ƙayatar. Amaryar ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta kawo kanta gidanta ganin irin kayan alatun da ka shirya a ɗakin. Duk da iyyen amaryar sun yi bajinta, amma Ajmal sai da ya sanya kayan furnitures a bangarensa masu kyau. A gefe ba a bar su Jannah ba da suke jin kamar an biya musu kujerar makka, ba ma kamar Jannah za ta huta da tashin asuba karatu. Don haka suka gayyaci 'yan makarantarsu da shirya shagali na musammman. Sun ɗinka kaya masu tsada da kyau. Kowa ya yi tunanin mom za ta dawo kafin bikin amma sai dai ga mamakin su, ƙiri-ƙiri ta ƙi zuwa wanda hakan ba ƙaramin haushi ya bawa Hajiya Baaba. Ita ko Jannah ko a tsummar rigarta don ta san abu ne mai wuya tazo sai dai ra'yin kanta. "Anya ba kurciya aka yi wa Halima ba? Lamarin nan akwai ruɗarwa. Tun yaushe take waƙar za ta dawo, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa. Ƙila sai na tashi tsaye."
Chapter 35 · 0% Book details