← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 79

Sashe 27

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"I hate her. My mom is so selfishness. Za ta dawo Nigeria saboda she wants to be a politician? Or my God! I can't imagine this. Bayan ta ki dawowa saboda umurinin mijinta da ni. Allah ban taba ganin maiyar kuÉ—i ba irinta. So take ta kwashi kuÉ—in gwamna..."
"Haba Jannah, duk waÉ—annan mugayen kalamai ga mahaifiyaki kike furtawa. Wannan fa cigaban ahalinmu baki É—aya ne, ke da za ki yi murna za ta dawo kusa dake."
"No, I won't go. Na fi son na zauna a gidan, amma babu inda za ni don ba ta da lokacina. So am happy here."
Hararar sakin mata tare da miƙewa" You know what? I can't deal with your shit right now, and is this attitude of you that annoyed me."
"You don't know everything. You don't know her shi ya sa kike faÉ—in haka.
"Then disclose it to me, kinga.."
"No I don't have that time, abin da kawai na sani ba ta sona." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
Hajiya Baaba ta fito daga ɗakinta ta balla mata harara,"Ke dai wallahi anyi 'yar baƙinciki. Ni ban taɓa ganin yar da take wa uwarta hassada ba sai ke. To ta Allah ba ta ki ba, mahaifin na ki da kike so ya fi ta ba haka Allah ya so ba, sai dai ki mutu.
Miƙewa ta yi ta tura baki tare da zabga mata harara kamar idanun za su faɗo ƙasa.
Ɗaki ta ruga tare da kulle ƙofa tana kuka sosai. Numbar dad ta kira wanda bugu ɗaya ya ɗauka,
"Helle dad, is it true that mom wants to come back to Nigeria because of politics?"
Shiru ya yi kamar ba zai amsa tambayar ba har sai da ta kara maimatawa cikin ƙaraji.
"Oh yes but understand her."
"Haba dad, supporting her all the time, you don't have right in your house. Na tabbata in har ta fara siyasa, sai kayi watanni ba ka ganta ba. Please ka rabu da ita ka dawo Nigeria ka yi aure mu yi zamanmu da matarka, ta haifa mini ƙanni, saboda ita mom neman kuɗi ya sa ta ƙi haihuwa. Ni ɗaya kawai ta haifa kamar mayya."
Wani irin abu ya daki kansa mai kama da guduma. Ko kaɗan bai taɓa tunanin za ta yi ƙorafi game da rashin haihuwar mom ba. Idanunsa ya rintse yana jin anya in ta ji shine sanadin hakan za ta yafe masa. Take zufa ya keto masa har yana ɗiga a jikinsa.
"Haba Jannah, ya kamata.."
ÆŠif ta kashe wayar tare da jifa da ita."Na rasa wane irin so yake mata ba wanda ya kasa yin wani abu a gidansa. Anya ba asiri ta yi masa ba, don ta juya shi son ranta." Ta tambayi kanta cikin ruÉ—u.
Har ta danna numbarta za ta kira sai kuma ta ga rashin alfanun hakan, domin tunda ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta.
"Rayuwarta ne ta je ta yi kowa yana da ikon zaɓa ma kansa abin da yake so. Kamar yadda take rayuwara son ranta ni ma ba ta isa ta ba ni umurni na bi ba." Ta faɗa a hasale

Don haka ta cire abin a ranta tunna shi kansa wanda yake da iko da ita ya kasa komai ballantana ita da ba ta bata mahimmanci a rayuwarta ba.

Jannah na kwance wayarta ta fara neman agaji. Ganin numbar mom ya sa ta yi tsaki ta koma ta kwanta.
Tunawa da motarta ya sa ta zabura daidai lokacin da wayar ta tsinke. Tana ƙoƙarin kira kiran ya ƙara shigowa.
"Hello Jannah, motarki ta iso. In sha Allahu gobe yayanki zai É—auko miki ita." Ihun murna ta saki sosai tana tsalle.
Maganar mom É—in da take yi yasa murnarta ta koma ciki."Haba mom, kan me za'a hana ni driving? Ni gaskiya ba zan yarda ba."
Sauke ajiyar zuciya ta yi tana faÉ—in,"Kafin ki gama sakandiri ne, amma da zarar kin gama za ki fara tuki, kin san Nigeria ba kamar London ba." Kashe wayar ta yi tana gunaguni.
Hajiya Baaba da take ƙoƙarin shiga ɗakinta ta ja ta tsaya jin tana ta magana ciki-ciki."To 'yar gidan fitsara, jikar marasa kunya. Uban wa kike zagi, in dai ba 'yata ba?" Harara ta banka mata ta miƙe ta shige cikin ɗakinta sai kawai ta sa kuka.
A mota Aby ke nuna w Ajmal motar da zai É—auko wa Jannah a Abuja. Tsananin mamakin motar da kyauta da tsadarta yake yi.
"Yanzu Aby wancan ficiciyar yarinyar mom za ta siya wa mota, kuma ta yi driving da kanta?" Ya faÉ—a cikin tsantsar mamaki.
"Kar fa ka manta mahaifiyarta wace ce. Kuma ita kaÉ—ai ta mallaka."
Jinjina kansa ya yi, bai ce komai ba, wanda ganin hakan Aby ya ci gaba da cewa,"Ka ji maganar an tsayar da ita takarar minister ko?" Kallonsa ya yi sai kuma ya mai da hankalinsa kan tuƙi.
Chapter 27 · 0% Book details