Sashe 15
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana murÉ—a kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya a gabanta.
"Ungo nan! Na ce ugo Jannatu. Uwarki kika yi wa banza ba ni ba."
Ƙarasowa ta yi ta zauna kusa da ita tare da rungumeta. "Haba tawan ni kaɗai, kin san bamu faɗa. "
Murmushi ta saki tare da kama hannunta. "Ke kaÉ—ai na damu dake, amma kika wulakanta ni. Kusan awa É—aya ina buga kofarki. "
"Hajiya bacci na ke yi fa. "Ta faɗa a sangarce cikin muryar shagwaɓa jin abin da ta ce.
"Kai dai rashin zaman Halimatu ya sa ta yi sakaci da koya miki addini? "Ta faÉ—a cikin razana da mamaki.
Sai ta É—ora da cewar, "Ko karatun kur'ani ban ji kin yi ba, kamar yadda muka saba a gidan nan, sai kika koma bacci kika rinka shafa bacci kamar rago. "
Haɗe rai ta yi jin abin da tace. A ranta take tunanin ina mom take da lokacin ta ballantana ta koya mata karatu, gara ma dad shine ma yake dan ƙoƙari har ta ita haɗa baki a gurin sa.
"Aiko da sake. Yaran gidan nan duk sun sauke kur'ani da hadda ke kina nan. "Sai kuma ta kaÉ—a kanta tana faÉ—in,
"Halima Allah ya yi mace mai taurin kai, ni da ubanta sam bamu da wannan zuciyar ta rashin yafiya. Haka kawai ki nisanta kan ki da kowa saboda wani kuskure da ya wuce."
Jin abin da ta ce hankalin Jannah ya koma kanta. "Yauwa Hajiyata. Don Allah ki gaya mini abin da ya faru tsakanin ta da dad wanda ya sa ta ki yafe masa. "
"Kiyi hakuri, sai da na É—aukar mata alkawarin ba zan gaya miki ba, sannan ta yarda ki zauna a gidan nan, amma na san dole watarana su gaji da kumbiya-kumbiya su sanar miki. "
Taɓe bakinta ta yi "To koma dai mene ne su suka sani. Na yi nisa da su ta yarda bazan cigaba da ganin abin da ke faruwa tsakanin su ba. "
Janyo plaks din koko ta yi tana faɗin, "Manta da su shalele, can suka sani. Ma za janyo kofi musha koko da ƙosai da na yi mik... "
"Koko da ƙosai kuma Hajiya? "Ta tambaya cikin muryar mamaki.
"Eh koko da kosai fa wanda ada yake gararan iyayen ki shi na dama miki, a tunanina za ki yi murna da hakan tun da kin gaji da cin abincin nasara."
"Ni ban gaya miki na gaji ba. Kuma ruwan tea zan sha da soyayen dankali na fi karyawa sha biyu da rabi."
"Umh! Sannu haihuwar turawa. Yanzu nufin ki watsa mini kasa za ki yi kamar na jiya. Aiko in dai ni jikar mai gishiri ce bazan kara miki girki ba, sai dai kije duk inda za ki ci kici, ai dama na lura kin fi son cin na wancan kinibiyar salon a mallake mani ke kamar yadda aka yi wa É—ana. "
"Dama kin hutar da ran ki. "Ta furta a ranta a fili kuwa, shiru ta yi tana jin ta na bambami ba ta tanka ba, sai ta kwanta tare da daukar remote zata canza tasha.
"A'a, a'a bar mini tashana ina kallon al'adun Hausawa, ki canza mini da wani yaren banza. " Ta fadi tare da wafce remote É—in a hannunta, yayin da ta yi fici-fici da ido tsabar masifa.
Dariya ta yi ta san duka haushin ta ki shan koko ne, sai ta kwanta tare da É—aukar wayarta ta kunna kallon ta ci gaba da kallo.
A falon Ammi tana tsaye a gaban dining tana shirya abin karyawa ita da Nahlin. Yar autar ta Ummita ta fito daga bedroom É—in su da alama lokacin ta tashi tana goge idanu.
Da sauri Nahlin ta É—auke ta tana dariya tare da nufar bedroom na su don ta yi mata wanka. Bayan ta yi mata wanka ta shirya ta cikin rigar da siket na kanti, kasancewar weekend ne ba school.
Ammi ta sumbace ta tare da faÉ—in,
"Maza kije ki kira ƙanwar ki ta karya in Hajiya ta yarda. "
Miƙewa ta yi da sauri. "Ba dolen ta ba, ni wallahi ɗakina zan dawo da ita da ƙarfin tsiya don ba za ta ji daɗin zama da ita ba."
"Taɓ! Aiko kina da aiki in dai Hajiya ne. "Ta ba ta masa tana ƙoƙarin zama.
Nahlin ta fita hannunta riƙe da Ummita. Da sallama ta shiga falon. Jannah ce kawai ta amsa gaisuwar, amma Hajiya ko kallon inda take ba ta yi ba.
"Ina kwana Hajiya. "Ta faÉ—i ba tare da ta ji mai za ta ce ba.
Shiru kawai ta yi sai motsi da bakinta da ta yi, wanda ba za ka gane mai tace ba, don kamar motsin sakamakon goron da take tauna ne.
"Little sis, watching film? Ta faɗi tana leƙa wayar Jannah dake kwance.
Miƙewa ta yi tare da daga mata ido bayan ta kashe kallon tana kallon ta.
"Morning sis. "
"Morning my sis. Hope you sleep well? You know Nigerian weather doesn't like London and mosquitoes everywhere. "
A'a na yi bacci sosai, ai Hajiya ta sa maganin zauri. So I must say I enjoyed it. "
"Good. "
Ta faɗi tana kallon Hajiya da ta yi fiƙi-fiƙi da ido jin an ambaci sunan ta. Dariya ya so ya ƙwace mata amma ta dake.
"Allah ya sa ba yi dani ake ba eh! Don na fi ƙarfin mutum ya san da wanda zan yi. "Hajiya ta ce tare da ƙara ɗaure fuska.
Dukkanin su babu wanda ya amsa mata, sai Nahlin ta É—auki wayar Jannah tare da kunna kallon film da take kallo.
"Korian film sis, you do like it? Ni ko they are not cup of my tea. Infact I don't have interest. "
"Really"Ta tambaye ta cikin mamaki sai ta É—aga mata kai.
"Kin ga ni kuwa da ga su sai Nigerian film I'm fan of them, kuma sam Korea ba sa film mara ma'ana unlike to Hausa movies I didn't say all sometime they do try. "
"Allah ko? Ko na fara kallo ne? Kin ga dama admission na ke jira. "
"Gaskiya I recommend you should start, you will enjoy it. "Ta ba ta amsa tana kallon ta.
"I will sis, since the recommendation is from you. "
"Ok, lemme send penthouse. If you don't have interest discard them."
"Sure, why not."Ta karashe maganar tana mika mata tsadaddiyar wayarta.
"Here you are little sis. "
"You will gonna enjoin it."
Dariya suka yi sannan Jannah ta miƙa hannu ta na kiran Ummita da ke kallon ta.
Hajiya Baaba ta cika ta batse sai dai ba ta ce komai ba, sakamakon rabin hankalin ta na can gurin tunanin yadda za ta yi ta canza dabi'un Jannah, da ta fahimci akwai ƙaracin kula da ibada kuma ta koyi cin abincin gargajiya.
"Mom said you should join us breafask. "
"Ok. "Ta miƙe tsunbul dama cikin ta karyawa yake sai dai ba ta ga yadda za ta yi ta sha koko a cikin ta ba.
"Ke Jannatuu ina za ki? "Ta tambaya ganin sun miƙe.
"Please Hajiyata Jannah. Ki daina ce mini Jannnatuu kamar wata 'yar ƙauye. "
"Ikon Allah! Ka kawo mu zamanin da 'ya'ya suke gudun sunayen su, sai ƙalƙalar banza.
Da sauri suka fice ba tare da sun damu da kiran da take musu ba.
"Hajiya is so dramatic! Kuma haka kuke zama da ita? " Ta tambaye ta cikin dariya.
"Tab! You never see anything, sai ta haÉ—u da Yaya Ajmal. "Ta ce mata dai-dai lokacin da suka shiga cikin falon.
"Good morning Dad. "Ta ce mishi tare da zuwa gafen sa ta tsaya. Shafa kanta ya yi cikin murna yana amsawa.
"Ya kika kwana da Hajiya da fatan ba ta takura miki ba? Na É—auka tare da Nahlin za ku zauna. "
"No, bata ta kura mini ba. I slept like a baby."
"Masha Allah. "
Ajmal ne ya yi tsallama ya shigo fuskarsa a É—aure sai dai ganin iyayen nasa ya sa ya saki fuskar tare da neman kujera ya zauna.
"Ina kwana Abby. Ammi mun tashi lafiya."Ya haÉ—a musu gaisuwar a jere.
Abby ya harare shi sannan ya ce,
"Jiya Alhaji bashir ya kira ni, ba ka je aiki ba, sai 10 kuma you took few minutes ka fita masallaci. "
"Eh Abby, na gaya maka zan je gurin aminina mahaifiyar sa ta dawo daga ummara na je gaishe ta. "
Ya giddira masa wannan karyar yana mamakin sa, domin ya san gurin sahibarsa ya wuni.
"You have to engaged, committed and be productive. Ka san kaine babba a gurin aiki so kome ya faru the blame will be on you. "
"I will Abby. "
Ya faÉ—a a gajarce don ya tsani a yi masa fada a gaban kanninsa.
"Oh na manta little sis na ka, na gurin ƙanwata Halimatu, da nace ka ɗauko ta ka ce ba ka da lokaci. She has arrived. "
"Ok. "
Kawai ya ce tare da ɗaukar filet zai yi saving ɗin kan sa ganin Nahlin ba ta da ninya, kuma ya fi ƙarfin ya yi mata magana, wanda ganin hakan da saurin ta ta shi tare da karbar filet ɗin.
Sai ya miƙa mata tare da mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake ta kira ta whatsapp duk da ya san mai kiran, ya dai ki ɗauka ne don ta faye nacin kira at many times.
Haka kawai tun jiya da Hajiya Baaba ta ce mishi ya ci albarkacin ta ya ji ya tsane ta. Kowa a gidan ba ta dafa masa kafa, amma daga zuwan ta har yaci albarkacin ta, ga shi babu abin da ya tsana face ya ci albarkacin wani.