Sashe 14
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Magana na ke, kike kunnen uwar shegu da ni. Wato ga mahaukaciya ko? Kin ga wallahi zamu saka kafar wando daya dake, ba zan lamunci wannan isgilancin na ku da kuka gado ko a ina ba. " Sai kuma ta sausauta murya ganin halin ko-in-kula da ta yi mata.
"Kina ji na shalelensa jikata. Kin san ke kaɗai na fi so, duk cikin jikokina ko? Ya kamata ki tausaya mini, matar nan ta riƙe makogaron ɗana sam ba shi da wani kataɓus. Abynku ya zama mijin-ta-ce."
Wani irin takaici ne ya kamata sai ta ki ganin ba'a rabu da bakar bane aka haifi habu. Ita da take ganin za ta zo ta huta da damuwa, sai ga shi ko hutawa ba ta gama yi ba, an dauki mata wani damuwar, wannan dalilin ya sa ta so ta zauna a sashin Ammy, amma ta hana to ga shi ba'a je ko ina ba ta fara dana-sa-ni.
"To ni mai zan ce miki Hajiya Baaba? Kin san ni ban san komai ba game da rayuwar da kuke yi. Ki yi hakuri don Allah"
Tana gama faÉ—ar haka ta shige cikin É—akin da ta nuna mallakin ta don kar ta kara ce mata komai.
Ajmal bai shigo gidan ba, sai misalin goma da rabi na dare, don ya san a wanann lokacin yar rigimar ta yi bacci. Ko da Hamir ya so ya shigo da shi har ciki, amma sai ya bukaci ya yi parking a waje ya sauka.
Cikin sanɗa ya shigo zai ije mata hura da nonon da ya zame ƙa'ida kullum sai ta sha sai ka ce magani.
"Munafikin Allah! Ina za ka dawo ma za dawo na ce. Ai na ji karar bude get, labarai nake sauraro na yi ma za na kashe don na san haka zai faru. To dawo dan ubanka. "
Takaici da haushi suka cika shi, ji ya yi kamar ya wuya ya shake mata makogaro, domin ta saka shi a gaba. Ko iyayensa ba sa zagin sa, amma sai ita haka take tamkar jikar maguzawa.
Kamar ba zai juya ba sai kuma ya jiya ya watsa mata kallo yana ƙoƙarin barin wurin
"Ka dawo na ce Adamuuu ka na jima ko? Wallahi in ka tafi sai fushin nan ya shafi kowa, don gobe ba wanda zai karya ta daÉ—i. Ta shi zan yi tun asuba na fara masifa da bala'i. "
"Hajiya Babaa, na ce ki dena ce mini Adamuu! I really hate the way you pronounce it. Tun da kin ka sa kiran Ajmal please call me Adam."
Ya ƙarashe maganar cikin ƙunar rai da ɓacin rai.
"Umm, aikin bit in ji tusa. Da ba'a san asalin angulu ba, sai ta ce daga Ƙasar misrah ta ke. Inji uban ka da ga ƙauye ya fito ɗan kauye ne na gidi. Wallahi lokacin da ya fito birni komai bai iya ba. "Sai kuma ta sa kuka ta ci gaba da faɗin,
"Wallahi Allah ya isa tsakanina da ƙanina Hamisu. Haka kawai ka saka finitina ka gudo mini da yaya birni ga shi nan, zuriyana ba su da maraba da iyalan arna.
"Iyalan arna kika ce Babaa! "Ya tambaye cikin tsananin mamakin abin da ta furta.
"Ina maraban dabbe da faɗa? Bakiɗaya kun ɗauki ɗabi'ar yahudu da nasara kun ɗora ma kan ku. Ni wannan turancin ma da kuke yi shi ya fi ci mini tuwo a ƙwarya. Ƙiri-ƙiri ina gani ku zage ni ba ni da ta cewa. Ina ji ranar nan cewa ka yi ko myh God. Da ga ji zagi ne. Allah shi zai saka mini, don wallahi uwarka ka zaga na ni ba.
Takaici da dariya sun hana ya shi ce mata komai ganin ta yi shiru tana zare ido.
"Allah ya ba ki hakuri. Bar na je na kwanta bacci na ke ji. "Ya ce, tare da ƙoƙarin ficewa.
"Kan ka ake ji. Mahaukaci ya faÉ—a rijiya ya ce "Kan ku ake ji ni wankana nake yi. "
"Hmmm. Sai da safe." Ya ce yana ƙoƙarin ficewa.
Ƙunƙunai ta yi wanda bai ji me ta fadi ba, don haka ya fara ƙoƙarin ficewa a ransa yana addu'ar Allah ya sa kar ta ƙara ɗago wata maganar kamar yadda ta saba, gamakin sa sai ya ji ta mike da sauri ta nufo gurin sa da yake ƙoƙarin fita.
"Ai na manta ni jikar mantau. Dawo maza Adamuu. Zo ga yar'uwar bakuwar turai ma za shiga ku gaisa. "
Ajmal ya tsaya da takaicin abin da ta ce. "Haba da tsawon dare nan, zaki ce na gaisa da ita? Dare ya yi ki bari sai gobe. Ba ni da lokacin ta. "
"To sannu agogo sarkin ƙa'ida. Ai dama na san ba'a abin arzikin da kai. Yar gidan Anty ka Halimatuu ne fa. Kar ka manta duk da bazarta kuke rawa, shi kan shi uban na ka da wa yake taƙama in ba da ita. Arzikin ta ka ci na daina fadarda nake maka, tana hutun gajiya bana son na tashe ta." Ta dasa aya cikin murya mai raɗa kamar wacce ta shinfiɗar da jaririn goye.
Ajmal ya yi tsaye sororo. Tabbas ya saba da gorin Hajiya Baaba, amma na yau da ban ne. Yarinya ƙarama take son ya je ya gaisar? Haba wuce nan. Shine har da yi masa gorin ba. Take ya ji wani tsanar Jannah ya kama shi matuƙa.
"Ki san kalaman da za ki furta mini, kuma wallahi kika sa ta raina ni, karya ƙasusuwanta zan yi kin san ban ɗaukar raini." Yana fadin haka ya fice daga ɗakin har yana haɗawa da gudu, yana jin lokacin da take fadin,
"To sannu ubana ko mijina. Ai gidan nan duk wanda ya so zaman lafiya dole ya yi wa Jannatuu biyayya."
Komawa ta yi ta zauna tana bambamin ta tare da kunna rediyon.
"Su kuma waÉ—annan 'yan rashin mutuncin cigaba da labaren su ka yi ba su jira ni ba."Ta faÉ—i tare sa kallon agogo, inda ta ga sha É—aya da rabi.
"Oh ni jikar maigishiri! Haka lokaci ya tafi wancan mara mutuncin ya tsare ni da surutu zai ja mini makara gobe, ga shi ina da tashin asuba na badawa shalele girki, koda yar gwadashin ba dole ta ci ba. Miƙewa ta yi tare da kashe wutan falon ta fara tofe-tofen addu'a wanda ya zame mata ƙa'ida.
Jannah na kwance cikin bargo tana sharan bacci ba tare da ta san wainar da ake toyawa a falo ba, kasancewar tun takwas da ta shiga yin sallah ta yi mata sallama bacci take ji.
Yanayi garin ya yi mata daÉ—i sosai kasancewar duk da babu room heater a É—akin amma yanayin ya yi mata dadi don babu irin sanyin London.
Ba ta tashi ba sai da aka kira sallah. Shi ma karar ƙwanƙwasa ƙofar Hajiya Baaba ya tashe ta.
"Ta shi ki yi sallah. Malalaci shi ne ya ke barin jam'i ta wuce shi."Ta ce tana buga kofar É—akin da karfi.
Miƙa ta yi da salati tare da kunna wayarta. Karar tsakon mom ya shigo da ga kunnawa, wanda dalilin kiran da ta dame ta da shi tun a jirgi ya sa ta kashe wayar.
"Na tashi Hajiya Baaba! "Ta furta cikin murya kaukausa ganin kiran sallar farko ne ta tashe ta.
"Ma za ki yi nafila ki roki Allah ya ba ki miji na gari. "
Tsuka kawai ta yi jin abin da ta faÉ—a. Ta koma ta kwanta duk da ta san ba lallai ba ne ta koma baccin.
"Akan miji kika tashe ni cikin tsakar daren nan, sai kace ba ni da buri da ya wuce na aure. Ko guda nawa nake da za ki yi mini maganar miji oho. "
Komawa ta yi ta kwanta sai da ta ji limami ta tada sallah san ta janye bargo ta shige bayi tare da sauro alwala, bayan ta bata lokaci gurin wanka, don a lokacin har an sallame sallah.
Tana idar da sallah ba ta yi azkar ba ta ta koma ta yi kwanciyarta, tare da saka earpiece a kunnin ta don kar ta dame ta. Season na Korean film take kallo mai dadi mai suna penthouse.
Hajiya Baaba ta yi kiran duniya da ƙwanƙwasa kofa akan ta so ta karya ta ƙi fitowa har sai da ƙarfe goma da rabi ya yi.
Ranta ya yi matuƙar ɓaci don ita ta ɗauka bacci take yi. Tun asuba ta gama dama mata koko, kosai kuwa bakwai dai-dai Talatu kai nika an soya, amma sai watsa mata kasa a ido ba ta fito ba yanzu.
Tana murÉ—a kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya ta tasa a gaba tana kallo.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 6-7*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM