← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 79

Sashe 38

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

komawa ta zauna zuciyarta fal tamkar gonar addu'a ganin yau Allah y mallaka musu junansu. Bayan ya ɗauko ya juye musu banƙararrun kaji da drinks masu sanyi. Kaɗan suka ci sannan suka je bayi suka yi brush tare da canza kaya. A wannan daren Ajmal ya nuna mata irin sonta da yake yi da dakon jiran ranar da ya yi, domin ya shayar da ita ƙauna mai tsuma zuciya ya sa ka manta komai, wanda ya sa ta farinciki ta san ta wuce zarra. Sosai take ganin wautan 'yan matan da suke faɗin ba sa son auren ustazu domin auren riba biyu ne. Ga soyayya kuma ga sa mace kan tafarkin tsira. Washe gari da safe bayan sun tashi sun yi sallah duk yadda ya so Mushirat ta ƙi barin sa ya kunna wuta a ɗakin sabod wani irin kunyarsa da take ji. Haka dai ya daure ya ja su sallah bayan sun idar sun yi azkar shine kawai ya yi karatun ƙur'ani, amma ita komawa ta yi ta kwanta sakamakon zazzaɓi da ya rufe ta. Bayan ya idar ya yaye bargon da ta lulluɓa da shi yana kallon fuskarta da ta yi saurin rufewa da zanin gado. Dariya ya tare da ƙara janye zanin gado."To kuma mene ne abin ɓoyewa kamar wacce ta yi laifi? Ai yanzu mun zama ɗaya babu kunyar wannan a tsakanimu." Ƙara ɓoye fuskarta ta yi tana dariya ciki-ciki ta ce, "Please ya Sheshk ka bari don Allah." Sakin zanin ya yi tare da ƙarasa wa kan gadon ya haɗata da jikinsa ya rungume yana dariya cikin jin daɗi. "Ina alfahari dake matar kirki Allah ya bamu tsawoncin rayuwa da zuriya ɗayyiba." Ba ta amsa ba saboda da salon tsokana ya yi maganar. "Au kin ganni ko? Abinci na haɗa miki a maimakon na kira ki kici na tsaya ina tsokananki." "Abinci ya Sheshk?" Ta tambaya cikin tsigar mamaki sai kuma ta ɗora da cewa bayan ya amsa mata da gira. "Ai da ka bari na ɗan samu tsauƙi na yi tun da na sha magani saboda bana son ka wahala." "Ai ko da bani da tausayi matar kirki. Kar ki damu watarana lafiyarki lau ma zan hutar dake in yi miki abinci ko na taya ki, domin koyi da rayuwar Annabi zan yi." "Tabbas duk macen da ta samu namiji mai addini da aiki da shi ta dace sosai. Uwa uba ga kyau da hankali har ma da natsuwa." Ta ce tana ƙoƙarin miƙewa. Fuska ya ɓata yana faɗin,"Mene ne haka ina za ki?" "Zan tashi muje dining." "Haba sai kace ba ni da tausayi? Bari ki ga ɗaukarki zan yi don yau babu ke babu tafiya. Ko kin manta daren jiya ai kin cancanci a ɗauke ki." Matsawa ta yi cikin kin kunya tana dariyar abin da ya faɗa." Don Allah karka ɗauke ni zan iya tafiya ka ji." Ta ce ganin ya nufo ta amma bai kula ba y sungume ta ba tare da ya ji nauyinta ba har sai da ya kai ta daining ya ije yana ɗan nishi. Dariya suka kwashe tare ya manna mata kis tare da buɗe soyyayyen ƙwai da tea da ya haɗa sai ƙamshi yake ga bread sai kajinsu da ya yi warming. "Laa! Ashe Zaujina ya iya girki ji wani suyan ƙwai yadda ya yi kyau?" Ta faɗa cikin sigar mamaki da zuba masa idanu. "Au ba ki sani ba? Ai Ammy ba ruwanta da namiji ko mace gabakiɗaya yaranta tana koya musu girki I will give you suprised anjima ina yi mana jallop na rise." "Really?" Ta tambaye shi tare da buɗe baki a hankali cikin jin kunya ganin ya gutsiri ƙwai ya nufo ta da shi wanda ya saka mata yana ɗaga mata kansa.Dariya suka kwashe da shi ya manna mata kis. Amarcinsu suke dirza cikin so da ƙauna domin kunyar da amarya ta nuna duka bai wuce kwana biyu ba, ta fito masa da kalar zahirinta wanda dama abin da yake ƙauna kenan shi ya sa bai kai soyayyar ga ƙwaila ba. Yana son macen da za ta kula da shi ta mai da shi tamkar ƙwai ta nuna masa bajintar ta ta ko wane fanni kuma tsaƙar shi ta yanke a matsaƙa domin ya samu Mushirat ta cika ko wane fanni. Ta fanni gayu da tsafta ba a magana uwa uba tunbinsa sannan fannin auratayya sai ya ce ita kaɗai ta ishe shi. Jannah kuwa hankalinta ya kwanta sosai ganin ta yi kwana biyu babu wanda ya takurawa rayuwarta. In ta kwanta bacci sai Hajiya Baaba ta yi da gaske take tashinta. A lokacin da Nahlin ta sanar da su ya ba ta umurnin ta rinƙa koya musu. Wani banzan kallo suka yi mata ba tare da sun furta kalami ba, sai Jannah da ta turo baki, "Taɓ, amma wasa yake yi ko? Don ni da karatu sai na islamiya, ai yanzu ni ba jahila ba ce." Bayan auren da sati biyu Nahlin ta sanar da su za su fara karatun asuba. Da asuba bagan ta yi sallah ta biya wa sauran yaran gidan amma babu ƙeyarsu, don babu tashin duniyar da Hajiya Baaba ba ta yi musu ba suƙa tashi, don tunda suka yi sallar asuba suka koma, amaimakon su tafi karatu. A ƙalla sai Nahlin ta yi kwana uku tana fama da su, ganin sun fi ƙarfinta ya sa ta sanar da shi, wanda washegari da asuba bayan ya yi salla a masallaci ya wuto gidan. Hajiya Baaba na zaune a falo da carbi a hannunta ya yi sallama ta buɗe masa ƙofa tana faɗin, "Yauwa gara da ka shigo, waɗannan yaran sam ba na tunanin suna sallah cikakkiya. Su hana kansu bacci da daddare sai safiya ta yi suce lokacin za su yi bacci, ai dare shine mahutar bawa. Ƙofar ta tura masa ya shiga tana faɗin,"Ita kanta Ummu da nake ganin ta fi ta hankali, ashe kura ce da fatar akuya. Gabaki ɗaya ta ɗauki ɗabi'unta ta sanya wa kanta." Kai tsaye bayi ya wuce tare da ibo ruwa mai sanyin gaske ya watsa musu, Wanda ya sa ta mike a firgice tare da sakin ajiyar zuciya mai karfi. "Uban wa ya zuba mini ru..?" Maganar ta maƙalewa mata a maƙoshi lokacin da suka yi ido biyu da shi, wanda ya sanya ta tashi da sauri tana zare ido. "Na shiga uku! Na mutu, wallahi na ɗauka Anty Nahlin ce ta turo Adal ya tashe mu, don na san shi ne kawai zai iya watsa mana ruwa. Don Allah ka yi haƙuri." Ta furta cikin rawar murya tana shirin kuka. "Rufe mini baki ja'ira, kin dai ɗauka ni ce marainiyar wayonki." Bulala ya zuga mata wanda yasa ta canyar ƙara tare da miƙewa da sauri tana sosa bayanta va tare da ta damu da kayan da ke jikinta ba. Ummu kuwa har ta fara kuka don ta san yau sai buzunta. Ganin kayan da yake jikinta ya sa ya saki bulalar yana faɗin,"Ma za ku shirya ku same ni a falo, marasa jin magana kawai." Ya fice cikin ɓacin rai. Hajiya Baaba ta bi shi tana ƙara zuga shi, don ita ba haka ta so ba. "Wai yau Allah ya taimake mu kayan bacci sun yi ceto." Cewar Ummu da ta miƙe ta nufi bayi. Da sauri ta sanya key a ɗakin ta dawo ta zauna,"Wannan jarabben ba zai barmu mu huta ba duk da yabar gidan." "Au zama kika yi kin manta yana jiranmu ko?" Da sauri ta miƙe jin abin da ta ce. Cikin ikon Allah results ɗinsu ya fito kum duk sun cinye. Baƙaramin murna Aby ya yi ba ganin sun fito da sakamako mai kyau. Washegari da safe suna Hajiya Babaa ta fito daga kicin tana faɗin,"Ani ma zaku raka ni gidan Adamuu, amaryarsa ta zo har sau biyu ban je ba. "Ni dai ba zani ba, ku dai je ke da ita." "Iko wallahi ba ki isa sai kin je, don haka ku shirya zamu je." Kan dole ta shirya ba don tana so ba. Sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu. "Hajiya bari na karɓo key gurin Musa direba na tuƙa motar." Ta faɗa cikin tsokana. "Ke dakata, tsaya na ce ko!" Ta furata cikin ƙaraji tare da ɗorawa,"Ce miki akai na gaji da duniyar, ko mutuwa nake son na yi? Don haka ki bari na mutu maza su kaini ba mata ba. Ni da nake son ganin har jikokinki." Dariya suka kwashe da shi duka ganin yadda ta firgice. "Su Hajiya akwai dogon buri na kusa da ƙasa ana hangen gaba." Uban tsaki ta yi ba ta ce komai ba ta shiga motar tare da kamewa a gidan gaba. "Wow! gaskiya gidan Ya Ajmal ya tsaru. Ina mishi kallon ɗan ƙauye ashe ya san me yake yi. A rayuwarsa gidansa ne kawai ya burge ni." Ta furta tana kallon gidan cikin mamaki d sha'awa. "A gida kam ya yi sai dai fatan rai ya mora. Adamuu ya yi ƙoƙari sosai, Allah ya yi masa albarka. Da ina shiri da maigidan nan kwana nan wuni." "Taɓ!" Ummu ta ce a ranta domin za ta iya rantse yau ce ranar da ta ji ta sa mishi albarka. Jannah da Ummu suka ciro wayarsu ana ɗaukar hoto da bidiyo za a yi posting, har da yi wa Hajiya Baaba bidiyo da take ta kare fuskarta tana zaginsu wai ta zo kwaɗayi. "Gafara masu gida." Hajiya Baaba ta ce da ƙarfi. Dariya suka kwashe mata da shi."Hajiya wa zai ji maganarki a irin wanann gidan." Hannu ta kai ta danna ring bell wanda ya fargar da Mushiirat da ke tsaye da kaskon wuta a hannunta tana turare falon da shi.
Chapter 38 · 0% Book details