← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 79

Sashe 8

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a kan gado. "Please, you know your condition; you hav.." "I said I will eat later! So please excuse me." Ta daka mata tsawar da ba ta san ta yi ba, domin Rose tamkar uba take a gurin ta don kular da take mata sam ba ta samun sa daga mom. "I’m sorry, Ma’am!" Ta faɗa cikin girmamawa tare da juya wa ta fice da sauri har tana haɗawa da gudu, sai kuma ta ji sam ba ta kyau ta ba. Mikewa ta yi daga inda take ta buɗe wardrobe ɗinta tare da ɓalle Amitriptyline ta watsa a bakinta tare da komawa ta kwanta tana jin yadda kanta yake juyawa tamkar ana murza sitiyarin motar da a ka ƙure mata maleji take shararar gudu a saman titi. A hankali ta fara jin kanta na saituwa zuwan can, maganin ya fara aiki wani irin ɗauyayyar bacci ya ɗauke ta. Rose ba ta ji gargaɗin da ta yi mata ba kamar yadda ta saba, bayan ta ba ta ɗau lokaci ta shigo. Ganin ta kwance rigingine ta ɗora filo a fuskarta, sai ta yi matuƙar ba ta tausayi. A hankali ta isa gare ta tare da gyara mata kwanciya, yayin da ta ji hawayen tausayinta na bin ƙuncinta. Ita kam ba ta taɓa ganin mace wacce ta fifita neman kuɗi da taimakon al'umma a rayuwarta ba. Tsananin tausayinta ya ƙara kamata domin ta san she is depressed. Hannunta ta sa ta janye mata gashinta da ya zubo a fuskarta. Mikewa ta yi da sauri ganin ta juya tuna gargaɗin da ta yi mata, amma sai ta ga ta kama hannunta ta riƙe tare da faɗin, "Momiii." Cikin magagin bacci. Ba ta tashi ba sai bayan kiran magariba sannan ta miƙe. Wanka ta yi ta fita neman abinci ba tare da ta damu da sallah ba don yunwa take ji matuƙa don haka ta bari sai cikin dare in ta tashi karatu ta yi sallah har da isha'i. Sai bakwai saura ta shigo cikin gidan da waya a kunninta tana waya. Dad da ya rigata dawowa ya shiga ɗakin Jannah sai ya ga tana bacci don haka ya zauna a falo bayan ya ci abinci ya kunna news. Ɗaga masa hannu kawai ta yi lokacin da take cire takalminta da gyalenta, wanda Rose ta karasa kan kujerar da sauri ta haɗa da laptop ɗinta da ta karɓa. Ido kawai ya bita da shi har ta shige ɗakinta. Duk yunwar da take ƙwaƙaƙularta kasa cin abincin ta yi, wanka kawai ta yi sallah sai bacci. Ba ta tashi ba sai goma da rabi a lokacin Jannah har ta ci abinci tana zaune da littafi tana karatu wanda ya zamar mata ƙa'ida kafin ta kwanta. “Jannah, ya kike, kin ci abinci?" Sai ta kalle ta sheƙeƙe cikin tsananin mamakin kalaman da ta furta wanda ta tabbata subutar kalami ne. "Oh please, Mom! since when do you care whether I eat or not? Da ma dai karatu kika tambaya as usual." Kauda tambayar ta yi ta hanyar komawa ta zauna a gefen Dad tare da ɗaukar laptop wanda hakan ya ƙara baƙanta ransu matuƙa da sauri Jannah ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta dad ya kalle ta da takaici ya ɗauki wayarsa ya nufi nasa ɗakin. Tsayawa ta yi da aikin da take yi, ta raka su da ido har suka shige, sannan ta maida hankalinta kan aikinta tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi. __________ NIGERIA A hankali ya ƙarasa gaban madubin dake gabansa, ya ɗauko wani sanyayar tureren da tun kafin ya buɗe wani irin sihirtaccen ƙamshi yake tasowa daga cikin kwabar. Sai da ya kusan daƙiƙa talatin yana riƙe da kwalbar tureren yana shaƙa idanunsa a lumshe, a rayuwarsa babu abin da ya fi so irin turaren apple, shi ya sa ko da ya je ƙasar cairo raka Daddy, babu tsarabar da ya yi wa kansa sai kwalaben turaren. Bayan ya gama shaƙar ƙamshi ba don ya ishe shi ba, sai dakin babu lokacin da zai ta shaƙar ƙamshin, sakamakon fita shi da amininsa Ridwan da zai raka shi gurin buduwarsa. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja tare da janye yarfe hannunsa ya zauna akan saman madubin yana ƙarewa ƙawataccen ɗakinsa kallo. Kusan kimanin daƙiƙa bakwai ya ɗauke idanunsa tare da tsuka mai sauti. "Na rasa mai yaran nan suka raina ni." Ya yi maganar tamkar wanda ya ke tambayar kansa da tsabar takaici ƙarara a fuskarsa. A zafafe ya miƙe ba tare da ya ɗauki wayarsa da take kan gado ba zai fice, sai dai kiran da ya shigo cikin wayar ya sanya shi dawowa da sauri ya ɗauki wayar domin ya manta da ita. A tunaninsa amininsa ne ya gaji da kiran sa, amma jin kiran wayar ya tabbatar masa da wannan natacacciyar tsohuwar ce, wacce ta ƙi mutuwa mu ci gumba kamar yadda yake tsokanarta. Ya san uzurin ta ne ya tashi ya sanya ta kira shi, don haka ya ƙi ɗaukar wayar ya juya cikin ɗakinsa don ya rufe sashinsa ya fice ba tare da ta sani ba, ballantana ta ɓata masa lokaci da suruntunta na marasa kan gado. Lokaci guda ya ji ransa ya ɓaci a dalilin kiranta, duk da cewar shashinta ya yi ninyar zuwa domin ya shuka wa yaran gidan rashin mutunci don ya yi ninyar dukannin su sai ya yi musu wanka da ruwar sanyi duk da irin hunturun da ake yi, amma da ya tuna ba kanwar lasa bace domin zai ita cewa a tarihin rayuwarsa bai taɓa ganin mace mafaɗaciya ba irin Hajiya Babaa, in tana faɗa har wani girgiza take kamanninta na canzawa. Don haka ya fasa ɗaukar motarsa ya fice gidan cikin sanɗa ba tare da ya bari kowa ya gan shi, duk da cewar bai sai Ammy ɗinsa na tsaye a gefen windon ɗakinta tana kallon fitarsa, duk da cewar ba za ta yi masa magana ba. Murmushi kawai ta yi tare da sakin labulen tana girgiza kai don ta san dawan garin. Hajiya Babaa da take ta famar kiran Ajmal baya ɗauka, tsaki ta ja ta janyo farin gilashin dake cikin gidansa ta maƙala a yar takurarriyar fuskarta da ta fara nuna tsufa da manyanta, sai dai daular da take ciki ya hana bayyana hakan ƙararar. "Ɗan ƙwal’uba! Ja'iri wanda bai yi gado abin kirki ba sai tsiya da muskilanci irin na wancan mara mutuncin uwar tasa, mai kama da tsinƙe ana bata abinci, amma babu amfani. Dama ina zai ɗaga wayata ya raina ni bani da amfani a gurin sa. Ke Nahlin kike ko Hahl." Ta ja tsuka ta ɗora cikin ɗaga murya. "Ku yi ta saka wa kanku sunaye masu wahala da sunan wayewa, ƙila sunan aljanu aka saka miki, domin tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin sunayen nan ba, ko acan karkararmu." Ta ƙarashe maganar tare da ɗauko robar lacasera da take sha, sannan ta ɗauko ɓallin goran da ke kan gefen kujerar da take zaune, ta gutsira tare da jefawa a bakinta. Hakan ya sa Nahlin ta ji cikinta ya yamutse wani irin amai ta ji zaizo mata, tun tana yarinya ta tsana sai dai babu yadda zata yi, domin ko da ta ƙauracewa shashin kan dole ta dawo, saboda ƙorafin da Hajiya Baaba ta kai wa daddy cewar yaran suna ƙyamarta. A dalilin haja Aby ya yi faɗa tamkar zai zane su. Don haka ta kauda kanta tana jin wani irin amai na taso mata. Ba tare da Hajiya Baaba ta damu ba, ta kauda kanta tana tauna goron duk da cewar ta ga yadda take wani yatsina, amma ta riga ta saba musamman Ajmal wanda ya sha amai akan hakan, sai dai babu yadda za su yi da ita, domin ta zaman musu ciwon ido nan gari nan bari. Nahlin ta miƙe da sauri zata bar ɗakin amma sai Hajiya Baaba ta yi kiranta tare da cewar. "Iskancin ya tashi kenan ina kiransa ya ƙi ɗaukar wayata, Allah ya shigo da shi lafiya zai same ni har cikin ɗakina." Ta ƙarashe maganar tare da jefa sauran ɓallin goron a bakinta. Sai kuma ta kalli Nahlin dake riƙe da murfin ƙofar falon zata fice ba tare da tace maka ƙala ba. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
Chapter 8 · 0% Book details