← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 79

Sashe 63

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu don Allah abin da kuke mini ya dace, haka za mu shiga ku kunyata ni? Maganar gaskiya ku zo na sallame ku, ku koma gida."

"Wallahi ba ka isa ba Mudi! Ka gudu ka barmu ka bi mace tsawon shekaru, kuma yanzu Allah ya sa mun gano ka kace mu koma ƙauye. Ai nan zama nan kwana."

Tsananin baƙincikin abin da ya furta ya ishe ya buɗe baki zai yi magana sai Jummai ta maƙale jakar buhunta ta riga shi da cewa,

"To in ban da ya raina mana hankali, mu shigo irin wannan gidan ya ce mu koma ko shiga, ai ni ko kayana ba zan ɗauko ba, domin yadda maiƙo da zaƙi ya sa ya maƙale a jikin mace haka muma zamu zauna muci arziki."

"Ƙwarai kuwa Jummai, domin ƙauye zan koma na kaso matata da 'yayana."

Zare idanunsa ya yi yana faÉ—in,"Ku zauna a ina, wai ni wa ya gaya muku inda nake?"

Wani irin ranƙwashi ta kai ma kanta har sai da ya ce ƙas tana dariya ta maƙale a bango tare da ɗaga ƙafa.

"Wallahi abokinka Shafi'u, shi ya gaya mini za ka dawo birni, ni kuma da na ji haka na dame shi da ƙyar ya bani adireshin gidan, kuma ba shi na ciyo muka taho."

Ƙuta ya yi bai ce komai ba ya fara tafiya wanda suka bi bayan shi da gudu suna murna

"In isasshiyar matarka ba za ta yarda ba to ta ɗauke ni 'yar aikin zan yi, amma na rantse ba zan koma ƙauye ba."

"Ni kuma gadi amma babu maganar komawa, ai sai a yi mana dariya."

Be tanka musu ba ya ƙarasa shiga cikin falo cikin jin kunya, sosai domin bai san wani irin tarba za su samu da ga Hajiya Baaba da kuma Mom da Jannah.

"Kai dakata! Dakata!! Ku kuma daga ina? Idan bara kuke yi ai sai ku tsaya daga ƙofa ba, wai ka shigo mana da su ba Jabiruu." Hajiya Baaba ta ce tana kallonsu cikin ƙyanƙyani.

Shiru ya yi yana sosa kanshi sai kuma ya ce," 'Yan'uwana ne suka zo daga ƙauye."

"Gaya mata Mudi, mu É—in ba mabarata bane muma 'yan gidane."Cewar Bala.

Da sauri Jannah da ta fito daga cikin É—akinta jin muryar dad ta tsaya tana kallonsu.

Yadda take kallonsu zai bayyana maka mamakin da take yi.

"Dad, waÉ—annan ne 'yan'uwanka." Ta tamabaye sa cikin tsananin mamaki tana wani yatsina fuska tamkar ta ga kashi.

" 'Yan'uwansa na jini kuwa, domin Yaya Bala shi ne farko sai Ya Mudi ni ce 'yar auta Jummai." Ta faɗi tana washe baki tare da riƙe gefen rigar dad tana yamutsa gugar da tasha.

"Waye kuma Mudi?" Ta ce da sauri tana watsa mata kallon ƙyanƙyani.

"Jannah da gaske 'yan'uwana ne domin babu ƙaryar abin da ta faɗa."

"Laah! Wai kana nufin Murjanatu ne ta girma haka? Ikon Allah girma ba wuya. Ke Murjanatu ta ho 'yata." Ta ƙarashe maganar za ta rungumeta.

"Please don Allah dakata! Dad, na kasa yadda waÉ—ananne 'yan'uwanka? Please do explain, saboda fitowar da na yi akan ka É—auke ni ka kaini gurinsu." Ta faÉ—a cikin muryar kuka.

"Hehe, nananye, to ai ko yanzu ba ta ɓace ba, domin za ki iya bin su a koma ƙauye ayi daka da surfe. Kin dai gani ga dangin uban na ki nan da kike ta mana ɗagoshi da su." Cewar Hajiya Baaba tana dariya cikin tsokana.

"Don Allah ka fahimtar da ni domin na kasa yadda waÉ—annan kucakan sune 'yan'uwanki."

"Tabbas ba ni da waÉ—anda suka fisu, kamar yadda sune gatanki."

"No dad!" Sai ta sa kuka sosai tana faÉ—in,"Su ba 'yan'uwana bane I have nothing to do with them."

"To sai kije ki zaɓo waɗanda kike so su zama 'yan'uwanki, domin a lokacin da nake gaya miki uban na ki ba kown kowa bane kasa yadda kika yi, saboda yana cikin arzikin 'yata. Kin ga yanzu dole aure tun da ba ki da dangin zuwa, sai ki gane gata zan yi miki." Ta ƙarashe maganar tare da juyawa za ta bar falon

Mom da jin hayaniya ya sa ta farka daga baccin da take yi ta fito tana zuba hamma.

Turus ta yi ganin waÉ—anda suke falon tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda kai suka san ta dawo Nigeriya da inda take.

Tsuru-tsuru suka yi domin a tunaninsu za ta yi musu rashin mutunci ko ta kore su, amma sai suka ga akasin hakan duk da abin da suka yi mata ya dawo mata tamkar sabo.

"Barkanku da zuwa, baƙi muka yi?" Ta furta cikin sakin fuska tana ƙarasowa gurinsu.

"Sannu da zuwa Ya Bala, sannu da zuwa Anty Jummai." Ta furta a tare lokacin da ta ƙarasa gurinsu, wanda ganin sakin fuskar da ta yi musu yasa suka rage tsoro suna ƙaƙalo murmushi.

Tsananin mamaki ya kama Jannah matuƙa take ta gasganta maganarsa cewar 'yan'uwansa ne, sai ta rinƙa kallonsu cikin tana yamutsa fuska.

Da sauri ta juya ta shige cikin É—akinta, daidai lokacin da Hajiya Baaba wanda fitowar mom, ya sa ta tsaya taga wani irin tarba za ta yi musu.

"Ba za ki kawo wa 'yan'uwanki ruwa ba." Ta ce tana dariyar mugunta.

Mom ta ba da umurnin a kawo musu abinci wanda suma ci har da dabbe. Bayan sun gama ta nuna musu É—aki akan suje su yi wanka.

Falo suka dawo suka haye kujera suna ta kallo da ihu da shewa.

Jannah ta fito daga ɗakinta za ta shiga kicin domin matuƙar yunwa take ji, idanunta ya kumbura ya yi luhu-luhu saboda kukan da ta ji.

Wayarta a hannunta tana ta neman phone ɗin Huzaifah da iyayensa suka karɓe wayarsa.

Tsayawa ta yi cikin tsananin takaici da baƙinciki tana kallon su Bala da Jummai da suke zaune kan kujer suna ihu akan kallon da suke yi.

"Kai ka ga mini shegen mutum da mugunta ya kama mutum da duka ji yadda ya ji masa rauni." Jummai ta furta tare da miƙewa da sauri za ta je gaban tibin.

"Wallahi rama masa na kai, ni kam na tsani mugunta." Ta ƙarashe mganar cikin muryar kuka hawaye shaɓe-shaɓe daidai lokacin da mutum ya coka masa wuƙa a ciki, sai ta fashe da kuka da saka ƙara za ta nufi gaban tibin.

"Wallahi ya sokai, wannan sam ba shi da imani."

"Ke banza, shashasha fim ne fa, ke duk shiri ne bai mutu ba. Da yake ba ki shigowa birni ya sa ba ki sani ba, amma ni nasha kallon irin finafinan nan, duk da ni ma da fari na É—auka mutuwa zai yi."

"Ai Bala, yanzu kana nufin tashi ya kai?" Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki.

"Me zai hana ke jar bula suka shafa masa kamar jini."

"Yau ga lalalattun banza, wanga him ai ba abin kallo na bane, a kahe mana hi."

"A ke, barmu mu kalla ai shine birnancin kuma. Ke dai zauna muga abin mamaki." Suka zauna suka cigaba da kallo ba tare da sun damu da yadda 'yan falon suke kallon su ba.

Wani banzan kallo Hajiya Baaba ta yi mata tana mata dariyar ƙeta da ta ke tsaye tana kallonsu tamkar ta shaƙe su su mutu.

"Kin ga fa danginki na kallo da yake ke ba É—iyar mutunci bane, kamata ya yi kizo ki taya su."

Wani banzan kallo ta yi mata domin ta san duk takalarta take wanda ta ci alwashin ba za ta ƙara mata magaba ba.

Wucewa kicin ta yi tana harararta da su Bala ba tare da ta ce mata komai ba, wanda Hajiya Baaba ta ci gaba da gyara hularta tana dariya ƙasa-ƙasa.

A ƙofar kicin ɗin suka ci karo da mujee, wanda da gangar ta sanya kafaɗa ta bangajeta har abincin da ta ibo a flate ɗin ya zube.

"Ka ga mini yarinya mara mutunci, wallahi Maijidda ki tsinka mata mari har sai hannunki ya kwanta tun ba ba ta da kunya."

"Ƙyale ta Hajiya Baaba, ƙuruciyace za ta bari." Ta ce tana ƙoƙarin tattara abincin da ta zubar.

"In ba da duke ni ba sai ki zo ki duke ni. Na gaya miki ki fita idanuna domin yanzu mun yi hannun riga dake."

"Au ni ma fitsarar za ki yi mini bari na taso ki gani don ba zan ɗauka ba." Ta ce tare da miƙewa cikin fushi.

Hannu ta É—aga za ta wanka mata mari amma sai Mujee ta tare ta.

"Don Allah ki yi haƙuri karki biye mata."

"Ki barni da ita ta san halina sarai, domin wallahi sai na sanya kiyi amarci da kubburerren fuska mara mutunci kawai."

"Ki kashe ni shi zai fi mini domin auren nan da kike so ki ƙaƙaba mini is more than beaten Hajiya Baaba, you are killing me!"

"Kin ci albarkacin Maijidda da kin yaba wa aya zaƙinta mara kunya kawai." Ta koma ta zauna taci gaba da gyara hularta ba ta ƙara tanka mata ba.

"Haba Jannah, ki yi shiru mana muje na zuba miki abinci..."

"Dallah! Malama ƙyale ni!" Ta ce cikin tsawa tare da juya ta koma cikin ɗaki ta ci gaba da kuka, abincin da ba ta ci ba ke nan duk da yunwar da take ji.

Bayan dad ya dawo ya yi wanka ya ci abinci. ÆŠakinta ya fara shiga amma sai ya ga tana kwance tana baccin da ga gani da tsiya aka yi shi, domin ko kwanciyar daÉ—i ba ta yi ba.

Gyara mata kanta ya yi yana kallonta cikin tsananin tausayi domin ya san Hajiya Baaba ta shiga rayuwarta na raba ta da masoyinta.

Wayarta da take waƙa ya ɗauka ya kashe tare da jona wayar a caji ganin ba bu caji da yawa. Ƙofar ya ja mata ya rufe sannan ya fita.

ÆŠakin su Bala ya shiga suna zaune suna ta aika ma cikinsu abinci.

"Ya Mudi ka dawo?" Jummai ta ce masa tana yagar cinyar kaza.

"Eh, na dawo." Ya ba amsa a gajarce.

"Kai wallahi gidannan akwai daÉ—in zama ka na cin daÉ—in ka. Irin waÉ—annan girki shi ya sa ka yi kyau ka zama tamkar balarabe. Sam yanzu bana ganin laifin ka ba, domin ko ni da zan samu wata Hajiya ta yi wuf da ni, da gudu zan amince aradu."
Chapter 63 · 0% Book details