← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 79

Sashe 77

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ajmal ka cuce ni saninka bai yi maka amfani ba rayuwatavta ƙare mama, ki turo Ya Najib ya zo ya ɗauke ni ina tasha ba zan iya tarar abin hawa ba, dama mun yi da shi zai zo ya ɗauke ni amma ya tafi kai ta asibiti." Ta ce ba tare da ta lura titi take nufa tana maganar ba sai kawai ta ji ana faɗin "Ke!Ke!!." Wanda ya sa ta yi sauri ta waigawa tare da ɗora hannu a sama ganin ƙatuwar mota ta tunkarota gadan-gadan.

Mom tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa ƙauyen. Ɗaukar matar da jarirai suka yi wanda kai tsaye asibiti suka wuce ganin yadda suke cikin mawuyacin hali.

Bayan an duba matar da ɗaura mata jini sannan ta biya tare da bada maƙudan kuɗi da za su kula da kansu.

Saboda tafiyar da za su yi ba ta wani jima ba suka kama hanyar Zariya.

Sun É—an yi tafiya mai nisa suna tafe suna hira da Mujee.

"Inyaa!Inyaa!! Inyaaa." Suka ji kikan jarirai a cikin bayan motarsu wanda ya sanya suka saki salati tare da waigawa.

"Innalillahi! Mun shiga uku. Jariran 'ya'yan aljanu muka É—auko a bayar motar?" Mom ta tambaya cikin tsananin tsoro da tashin hankali.

Da sauri direba ya gangara ya yi parking zuciyarsa cike da tsananin tsoro da mamakin yadda aka yi jarirai a cjkin motar, wanda ya tabbatar da 'ya'yan jarirai ne.

Cirko-cirko suka yi sun kasa isa gurin boot ɗin motar ballantana su yi ƙoƙarin buɗewa sai zare ido suke yi.

Direba ne ya yi namijin ƙoƙari ya ƙarasa jikinsa na kyarma ya buɗe boot ɗin tare da rintse idanunsa kar ya ga aljanu, wanda tun yana yaro ya san cewar duk wanda ya ga aljani kwanan shi ya ƙare.

"What!" Mom ta furta cikin tsananin mamaki tana kallon yaran da suke cikin kwali suna canyara kuka.

"Mujee, this is absolutely impossible! WaÉ—annan ba yaran da muka kai wa mahaifiyarsu taimako ba ne."

"Mun shiga uku, wallahi sune garin ya akai suka shigo cikin motar nan."

Mom da gumi ya jiƙata sharkaf ta share zufar zuciyarta saboda bugawa tamkar za ta sinke, domin ta gane sharri za a ƙulla mata.

"Someone is behind this Mujee, sharrin maƙiya ne, kuma da makusancina a ciki. Shikenan, rayuwata ta ƙare na shiga uku."

"Tabbas sharrin abokan takara ne Hale.."

"A'a duk wanda ga aikata wannan ya san da duk motsina na jikina n..."

Ajmal kuwa, suna isa cikin asibitin ya fahimci ya manta da wayarsa wanda ya tabbata a falon Aby ya ciro ta domin ya yi chatt da Mushiirat.

Da sauri ta ɓalle motar ta fito da sauri ganin ya fita burinsa ya rigata shiga karsu jera tare, wanda ta gane lagonshi ta haɗa da sauri ta isa gare shi tana kallonsa suna tafiya.

Tamkar ya shaƙeta haka ya ji ga kunyar yadda mutane suke kallon shi duk da sun san 'yar'uwarsa.

"A'a Ya sheshk, kai ne haka da yammar nan?" Cewar doctor Irfan yana kallon Jannah da ta shigo a bayansa.

Ba bu wanda ta kalla a cikinsu ta samu guri ta zauna tare da fito da wayarta tana kallon tiktok duk matsanancin zazzaɓin dake damunta amma burinta ta ƙuntata masa.

"Madam ce ba lafiya?" Ya tambaye sa ganin tun da ya ba shi hannu ya kasa ce masa komai domin zuciya ta tuƙo shi.

Bai tanka masa ba haka Jannah ba ko kalli inda Irfan yake ba.

Ganin haka ya ɗauko abin gwajinsa ya fara duba ta yana kallon yadda take kallonsu a wulaƙance.

"Zazzaɓi ne mai zafi ya kamata kuma ta saka damuwa a ranta. Zan ba ta magani sannan za a yi mata allura guda biyu har na tsawon kwana uku."

Wani irin zabura ta yi ta miƙe tare da ja baya domin idon akwai abin da ta tsana be wuce allura ba, don ba ta yi tunanin zai ce zai yi mata allura ba da ba ta zo ba.

Murmushin mugunta ya kubce masa ganin ya gano lagwanta daidai lokacin da ta ce,"Kai mugu don't inject me, just give me meds." Ta ce tare da bayyana tsoronta a fili.

"Ba ki da kunya ko? Irfan ka haɗa mata duka allurar, saboda ka san jibi ne bikinmu cin amarci ba zai bari muzo ba." Ya ce fuskarsa a murtuke wanda ya sanya ta daka tsalle ta miƙe tana mazurai.

"Haba, sai ka ce ba ka san yadda ake allura, dole biyun É—in za a yi mata inyaso na zo gida na arasa mata sauran."

"Na rantse babu wanda ya isa ya yi mini allura sainka ce wacce ta zo a sume da ƙafafuna na zo ni na ma daina jin ciwon na warke." Dariya ta so ta kubce wa Irfan ganin yadda ta tsorace tana mazurai.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 37-38*

*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*

*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Ba ke iskanci da taɓara ba, kin ciwon ƙarya kina ta zuba iskanci sun biye miki, zan yi maganinki."

"Ma za Irfan haÉ—a ruwan allurar." Ya ce yana nannaÉ—e hannun rigarsa.

"Wayyo na shiga uku! Dad zan kira na sanar masa don ba zan yarda a yi mini allurar ba." Ta ce tana ƙoƙarin kiran dad wanda ya wafce wayar ya aje kan kujera, ya sanya hannunsa ya damƙota da take ƙoƙarin ficewa da gudu.

Wani irin ƙara ta canyawa wanda ya sanya har ya sake ta ya ƙara damƙota da hannunsa ɗaya yana toshe kunninsa tare da ɗaga hannunsa zai mareta.

"Ba ki da hankali ne za ki ƙwala kamar mahaukaciya?"Ya ce cikin zafi da tsawa.

"No, please karka duƙeta ka ka yi haƙuri, ka san akwai waɗanda suke tsoron allura.

"Ƙyale ni Irfan in har ban duketa ba, ba zan ji daɗi ba. Za ayi mata allura kamar za a kasheta. Mushiirat da kanta take yi wa kanta allura, sai ita za ta zauna tana buɗe baki."

"Mushiirat, babba ce ita kuwa wannan da ƙuruciya."

Tsaki ya yi ya ƙara damƙota da ƙarfi sosai." Caka mata allurar sauri nake yi, in ta ƙi bari ka karya allurar a ciki."

Wani irin ihu ta ƙara saki sosai take kuka duk ta cika ofis ɗin da ihu da ƙara.

Lokacin da ya tsira mata allurar sai da ta yi wani irin ƙarar da ya fi wancan, wanda haushi ya sa ture ta ta faɗi ƙasa.

"Abin da nake gudu kenan, a haÉ—a ka da yara suyi ta maka hauka. Jibi abin da take yi wannan haukar."

"Walllahi Allah ya isa kuma saina gaya wa dad mugaye kawai." Ta ce cikin muryar kuka tana taɓa inda aka yi mata allurar.

Da sauri ya ƙarasa guri ta zai ɗauke ta da mari." Haba, don Allah karka biye mata."

"Ka na ji fa zaginmu take."

"Ka kyaleta ku dubi yadda ta yi har cikin zuciyarta ba ta son allurar."

"Allah ya sa ya zama ajalinta."Ya a ransa a fili kuwa É—aukar wayarsa ya yi suka yi musabuha yana faÉ—in,
"Bari na wuce matar kirki yau za ta dawo."

"A masha Allah na ji ance ta samu ƙarin girma Allah ya sanya alhairi."

"Ai da yake kwanyarta na ja don ni kaina ban yi tunanin za ta ci jarabawar ba." Ya ce cikin farinciki da murmushi É—auke a fuskarsa.

Haka suka fito suna tafe tana kuka wanda ko kallon inda take bai yi ba, wanda ya haɗa harda gudu ya shige motarsa ya tayar. Ganin haka taƙarasa da sauri ta shiga.

Suna tafe tana kuka da jan majina yayin da take jin inda aka yi mara allura yana tsikarinta, wanda in har ba ta sa ƙanƙara ba sam ba za ta ji sauƙi ba.

Da takaicin sawa da ya yi aka yi mata allura da zafin allurar suka ishe ta sai ta sanya ƙara ta ci gaba da kuka, wanda ya sanya cikin tsananin ɓacin rai ya gangara titi ya yi parking ɗin motar.

"Ke fito daga cikin motar nan domin ba za ki kashe ni da takaici ba " Ya furta cikin ɓacin rai yana watsa mata mugun kallo.

"Ba zan fito ba kuma na rantse ka yi ka maida ni gida in ba haka ba sai na ta kwarara maka ihu ince sato ni."

"Ok, haka kika ce? To Allah ya ba ki sa a ki fara tun kafin na fasa miki bakin ihun."

Ga mamakinsa sai ya ga ta sa fuskarta a saman kujerarsa tana goge ruwan hawayen da ya ƙi tsawa, sai kuma ta fyato majina ta goge, wanda ya sa ya ji tamkar zai yi amai yana kallonta cikin ƙyanƙyani.

"Ƙazamiyar banza fito mini daga mota na rantse sai dai ki nemi abin hawa." Ya ce tare da finciko ta ya direta a waje ya shige motarsa.
Chapter 77 · 0% Book details