← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 79

Sashe 66

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To munafukai, duk na ji abin da kuka ce. Na ce kuna gulmata kun ƙaryata, yanzu mai za ku ce da na kama ku da kunnuwana."
Da sauri suka waiga suna mamakin ganinta a jingine da ƙarfen bene tana karkaɗa wayarta cikin isa da gadara.

"Ban sani ba, ai duk abin da muka faÉ—a haskiyane saboda mun zo gidanku kin gama raina mu har ki kalli idanun Anty Nahlin kice mata munafuka." Ummu ta ce.

"To malama kike so na kirata? Kuna ta wani gulma ba ku tausaya mini halin da nake ciki ba, ai duk na gane halinku kuma zan yi maganinku. Don kawai ina da wanda nake so ne da sai na yadda an yi auren kuga yadda zan wahalar da É—an'uwanku na mai da shi tamkar almajirina na shishshuka masa rashin mutunci son raina sai na ga uban abin da za ku yi ku masu É—an'uwa."

"Jannah, Anty Nahlin kike gaya ma haka?"

"Ki barta saman zan hauro na zane ta kuma ta san babu wanda zai ce mini komai."

"To mai ya hana ki ai gani a gabanki bismillah." Ta ce cikin tsiwa wanda ya tunzura ta ta fara hawa benen da sauri.

Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki!

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 31-32*

*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*

*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki." A tunaninki bari zan yi ki duke ni? Muguwa kawai." Ta ce cikin tsoro.

"Matsoraciya ai da kin tsaya ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa dake." Cewar Nahlin cikin ɓacin rai.

"Ga rashin kunya sai shegen tsoron tsiya, ai ni addu'a zan yi Allah ya sa auren nan ya ƙullu, ko don ya koya mata hankali ta rinƙa girmama mom." Ummu ta ce suka ci gaba da kallo.

Tun da ta san tsiyar da ta shuka ba ta sakko ƙasa ba ko da ta ji yunwa frij ɗin dad ta buɗe ta yi ɓarnarta son ranta.

Tana kwance akan gadonsa gabakiɗaya ji take rayuwarta komai ya tsaya mata cak. Ko sallah ba ta tashi ta yi ba har sai da dad ya dawo sannan ta buɗe ƙofar ta faɗa jikinshi tana hawaye.

A tunaninsu wani ƙaryar za ta yi musu sai ta ba su mamaki don ba ta yi masa ƙorafin komai ba sai cewa da ta yi,
"Dad, I miss you." Ta furta tana riƙe da hannunta.

Ledar tsarabar da ya yi musu ya miƙawa kowa na ta sannan ya ije na Jannah yana ƙoƙarin buɗe mata robar ice cream.

Da kanshi ya fara ba ta sai kuma ya miƙa mata ya shige bayi don ya yi wanka.

Washegari da safe bai sakko ƙasa ba har sai sha ɗaya lokacin duk suna zaune a falo suna kallo.

Kwana biyu da tafiyar Hajiya Baaba, da mom duk sai gidan ya zama babu daÉ—i, domin tsoro yake ba su. Ko bacci za su yi sai tsoro ya kama su saboda girman gidan.

Zaman gidan sai ya yi musu babu daÉ—i domin shi kansa dad, sai dare yake dawowa, in bai fita da wuri bane ya fita takwas na safiya.

Ranar da ya cika sati É—aya da tafiyar mom wanda ta gaya musu saura kwana tara ta dawo, suka cika da murna ganin an janye strike don haka suka fara shirin komawa Zariya cikin farinciki, ban da Jannah da take contemplating whether to stay or not, saboda ita kanta ba daÉ—in zaman gidan take yi ba.

Haka dai a ranar da aka yi call off ta wuni cikin tunanin ba tare da ta samu mafita ba, saboda hankalinta ya fi karkata da ta koma, amma in ta tuna auren sai ta ga gara zamanta a Abuja. In ta hanga a wata mahangar ta ga zaman kaÉ—aicin da take yi sai ta yanke shawarar gara ta koma Zariya duk abin da zai faru ya faru, saboda ko sun yi mata auren ita ce mai zaman ta ga yadda za a yi ta zauna.

Cikin wanann halin na tsaka mai wuya wanda take ganin rayuwarta yana gaba kura baya siyaki. Ta kwanta ba tare da ta samu mafita ba, tana ganin su Ummu suka haɗa kayansu cikin farinciki don har sun kira mom, sai dai rashin sa a wayarta ba ya shiga amma sun bar mata tsaƙon kar ta kwana na shirin tafiyarsu.

Cikin fargaba yake sakkowa da troley É—insa yana ja zuciyarsa cike da tsoron yadda zai tunkareta ya sanar masa da tafiyarsa.

Ilai kuwa ganinsa da jaka ya sa ta miƙe a zabure.
"Dad, traveling?" Ta ce tana kallon shi da idanunta har sun fara kawo ruwa.

Bai amsa mata ba har sai da ya sauko ƙasa ya riƙe hannunta suka zauna kan kujera.

"Eh Jannah, tafiya ta kama ni ban san da tafiyar ba, and I must go it is an important."

"No, you will no go anyway I know it is mom that send you."

"Haba Jannah, na gaya miki tafiya zan yi and I will stay a bit long." Ya ƙarashe maganar cikin tsawa domin ya san in ba haka ya yi mata ba zai sha fama da ita.

A maimakon ta saduda sai ta sanya kuka.
"Babu ind za ka dad, ita ba ta zauna ba kai ma ba ta barka ba, gabakiɗaya ta takurawa rayuwarka. Ga shi su Ummu za su koma Zariya sai a barni ni kaɗai a wannan ƙatoton gidan, ni wallahi ba zan iya zama ba, saboda yanzu I can't stay in loneliness, na saba za ma cikin mutane."

Dafe kansa ya yi cikin rashin dubara."So what do yo want Jannah? You know I must go cus na yi reserving flight ko so kike mom ta yi asara."

"Eh, Let her do. Ban damu ba in dai za ka kasance dani don ba zan iya zama daga ni sai masu aiki a wannan gidan ba."

"Am sorry but I have to go. nan da awaya É—aya zai tashi I have to be hurry."

"I said you are not going anyway." Ta ce tare da riƙe rigarshi tana kuka.

Ransa ya ɓaci ya juyo ya kalli su Ummu da suka yi tsuru-tsuru suna kallonta.

"Nahlin, gobe za ku wuce ko? Mom told me that.I wished you safe trip and ku kula da karatu. Ga wannan mom ta ce a baku ku riƙe za ta yi booking flight na ku, sannan anjima direba zai kai ku shooping. Choose whatever you like it is on her."

"Ok, thanks dad, mun gode Allah ya ƙara buɗi."

Kallonta ya yi sai ya fisge rigarsa." Ba kya jin magana, karki manta ni mahaifinki ne, in na gaya miki magana you must obey haba you have to give me that respect I earned." Ya ƙarashe maganar cikin tsawar da ya firgita ta matsa gefe tana zare ido.

"Na gaya miki planning É—ina akan auren ki, amma you didn't agreed. Hajiya has power and authority that I can do anything than tha..."

"Leave me alone!" Ta ce tare da ƙara matsawa da fisge hannunta da ya yi.

"Na gane kai ma mom ta zuge ka da kuÉ—i, I understand that you were living in object puverty that's why mom manipulating you with money and make you like her errands boy. Your family are poor that is why you married mom to be rich. Saboda money sai ka kasa bani farinciki dad, ka na gani za a yi mini auren dole da wanda ba na so! Why did you marry mom becouse of money why dad?"

Sai ta fashe da kuka tare da durƙushewa.

"I love Huzaifah like crazy I want him to be my wedded husband, please do something."

"I'm sorry that I can't help, but you have to understand that my love to your mom is genuine."

"Isn't dad!"

"To shikenan, tun da ba kya jin magana you always do as you wish, sai ki je kiyi abin da za ki yi, kuma daga yau na cire hannuna akan maganar aurenki." Ya ce cikin fushi tare da É—aukar jakarsa.

"Nahlin, ku gida gida zan kira in ji kun sauka lafiya." Ya kama hanya zai fita yana jin yadda kukanta ke ƙona masa zuciya.

"Ni ma zan bi su do the viser with me I can't stay alone." Ta ce cikin muryar kuka.

Jiyowa ya yi ya kalleta sai kuma ta ba shi tausayi ya kasa ce mata komai domin ya sani suna cutarta da yawa, ya yi tunanin dawowarsu zai ba ta farinciki, sai ga shi maganar aurenta ya taso wanda shi ne sanadin dagula komai, ba shi da zaɓi wanda ya fi ta koma gidan Aby ta amince da auren, domin zaman ta da rayuwarta acan sai ya fi mata fiye da nan da ba su da lokacinta.
Chapter 66 · 0% Book details