Sashe 74
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Ya is calling ya ce yana gurin aje motoci." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba za ta tanka ba sai kuma ta ji ta ce,
"Wa kenan?"
Haushin tambayar ya sa ta ji tamkar ta tsinka mata mari duk da tana tausayin halin da take ciki. Sai dai, kuma ba ta son rashin zuwanta ya shafeta don haka ta daure ta cije ta ce,
"Ya Ajmal, tun É—azu ya aiko ni ban ganki ba ina ta neman.."
"Ya makance ne da ba zai iya shigowa gidan ba yake nema na na yi masa jagora?" Ta ce a gatsale bayan ta miƙe.
"Jannah, ki kama kanki tsaƙo ya bani kuma na isar in kin.."
"To kije kice masa na ce ba zan zo ba, Allah ya sa makantar ta tabbata ya dauwama anan har ƙarshen rayuwarsa. In kuma ba makanta ya kama sa ba, to in ya isa ya zo ya jani."
"Jannah, ki fita.." Nahlin ta fara magana cikin fushi dai kuma ta kasa ƙarasawa ta juya ta koma domin ta san ko kasheta zai yi ba za ta zo ba, kuma in ta daɗe duk laifin zai iya ko awa kanta, wanda tuna hakan ya sanya ta wuce kamar kububuwa.
Tsaki ta yi ta ci gaba da neman layinsa tana hawaye.
"Ta ce ba za ta zo ba."
"Ok." Ya ce domin ya yi tunanin hakan wanda har zai ɗaga waya ya kira Aby sai ya fasa tare da yanke shawarar ya je da kansa ya yi mata warning wataƙila ta iya sawa a fasa aure.
Har Nahlin ta juya ta fara tafiya bayan ta yi masa sai da safe a ranta tana tausayinsa na jawo masa raini da aka yi, amma sai ta ji ya ƙwala mata kira wanda ta juyo ta ƙaraso, tana addu'ar Allah ya sa ba ƙara aikenta zai yi ba, domin ita kanta haushin rainin da baƙaƙen maganganun da take faɗi take ji.
"Tana ina ne?" Ya tambayeta ba tare da ya daina danna wayarsa ba.
"Tana gurin bishiyar lemo zaune."
"Shikenan, je ki sai sa safe." Ya ce tare da zaman shi a mota har sai da ta ɓule sannan ya fito, domin kunya yake ji wai shi zai ta ka ya je gurinta.
A lokacin da ta ji alamun tafiya hawaye take yi amma jin ƙamshin da ta tabbata ba na Nahlin ba ne, ya sa ta fara kuka da ƙarfi.
"Wayyo Huzaifah masoyina don Allah ka ɗauki wayata, domin kai kaɗai nake so kuma nake ƙauna, saboda bayan kai kaɗai sauran mazan duk losaraye ne."
Ta ƙaraso tana faɗin hakan kuma ya ji ta bai tanka mata ba.
Hotonsa ta yi zumming tana shafa fuskarsa."Ina matuƙar son gemunka domin na ka baya ka a da irin na bagidajen mazan da suke ajewa kamar na buntsu.."
"Ke!" Ya ce cikin tsananin fushi wanda ko gezau ba ta yi.
"Saboda iskanci na aika a kira ki kika ki zuwa, na zo shine za ki fara gaya mini magana don kin raina ni ko?"
Banza ta yi da shi sai kuma ta ɗago ta kalle shi daidai lokacin da ya leƙa wayar yana kallon hoton Huzaifah.
"Shi kan dai murna za a yi masa da rabuwa da jaraba da ya yi, ni kuma a jajanta mini. Sai ya taɓe baki ganin ba ta ce komai ba, wayarsa ya ciro wayarsa tare da nuna mata hoton.
"Ki kalli wannan hoton."
Kallon banza ta yi kamar ba za ta kalla ba sai kuma ta kalla a wulaƙance.
"Na gani gidan kifi ne, ba ka da jari ne kake son na roƙi mom ta ba ka?" Ta ce mishi a gatsale.
"A'a." Ya ce tare da dariyar mugunta ya mayar da wayar a aljihunsa.
"Na zo na nuna miki na kuma yi miki albishirin da cewar matuƙar kika yadda aka yi auren nan, a daren amarcinki a nan za ki kwanta.
Juyowa ta yi da sauri tana kallonsa yayin da take son gasganta abin da ya faÉ—a.
Gira ya É—aga mata sai kuma ya É—ora da ce,
"Matuƙar kika ba yi abin da za a fasa auren nan ba aka kawo ni ki gidana, sai kin gwammace dama guba kika sha kika mutu, domin ina da matar kirki kamila mai kame kanta da alfasha mai zan yi dake ballagaza."
Kuka ta saka da ƙarfi sai kuma ta ga babu amfanin haka ta juya ta kalle shi ta saka dariyar takaici.
"Ka kwantar da hankalinka domin in har ban sha guba na mutu ba, zan yi sanadin ranmu ni da kai domin ba zan taɓa yarda na jawa kaina abin kunya na auren bagidaje irinka ba."
"Ok, haka kika ce." Ya tambayeta cikin mamakin rashin kunyarta.
Ɗaga masa kai ta yi tare da balla masa harara za ta wuce sai kawai ransa ya ɓaci ganin kallon da take masa ya sa ƙafarsa a tsakaninta kafafunta wanda ta harɗe ta faɗi ƙasa wayarta ta fashe.
Tsabar baƙinciki da zafin faɗuwar ya sa ta canyara ƙara wanda sai ga mutanen gidan a gurin har da Hajiya Baaba.
"Lafiya Ajmal? Na lura ba za ku taɓa barinmu mu huta ba."
"Da ga na zo zancan shi ne ta yi mini rashin kunya shine na fara koya mata yadda ake yiwa miji magana domin matata, haka take mini ba, ka ga gara na koya mata don kar ta ɓata mini tarbiyar matata." Ya ƙarashe maganar tare da kallonta yana murmushin mugunta.
"Ba zan iya ba da kuɗin zance ba Hajiya Baaba, domin ko lokacin da nake zuwa zance gurin Mushirat, in har ta ɓata mini rai bana bada kuɗin zance."
Murmushin mugunta ya yi y fice tare da faÉ—in,"Sai da safe."
Hajiya Baaba, ta kalle ta da take kuka sosai ga baƙincikin sabuwar wayar da ta siya ya fasa har ta ƙi kawowa. Kuka ta ƙara rushewa da shi.
"Wallahi Allah sai ya saka mini akansa da wacce ta haɗa auren, ba zan taɓa yafe wa ba." Ta ruga da gudu tana kuka.
"Fitsararra! Kin dai ji haushi wallahi, saboda ko wace mace in aka zo zance kuÉ—i ake ba ta, amma ke tsabar rashin kunya ya jawo miki, duka kika samu, to wallahi ba zan takurawa kaina ba, iya abin da ya samu za mu kai miki." Ta wuce tana bambami ba tare da ta kalli su Aby ba.
Dad ɗin Huzaifah ya shiga cikin matsanancin tashin hankali, ganin ya ƙi ci ya ƙi sha sai kuka da kiran sunanta wanda ganin haka ya sanya shi yi wa Zariya dirar mikiya, ba tare da shawarar mom da take ta yi masa tsiya ganin zai kashe kansa a banza ba.
Bai sha wahalar ganin Aby ba wanda ya karɓe shi cikin mutunci ya yi mishi karɓa ta ban girma duk da ba a san da zuwan shi ba.
"Ni ne mahaifin yaronan Huzaifah, wanda yake son Jannah, na san kuna da labarin mun zo lokacin suna Abuja, yanzu ma na ƙara zuwa akaro na biyu, saboda yarona he is in critical condition. Na roƙe ku don Allah.." Ya ce hakan tare duƙawa a ƙasa yana hawaye.
"Yarona zai mutu kuma shi kaÉ—ai Allah ya ba ni É—a namiji, ku taimaka ku bar yaran su yi aure."
Aby sai ya ji babu daɗi ganin mutum da girma kamar sa da muƙami yana roƙonsa. Sai dai, ko kuka ya yi baya tunanin za ta amince da idanunta ya rufe na ɗaukar fansa a kan dukanninsu.
"Ka yi haƙuri Hajiya Baaba, ba za ta amince ba, domin idanunta ya rufe fansa kawai take so ta ɗauka. Mu ɗin mun yi kuskure wanda ya shafi yaronmu. Ina fatan yaronka ya samu lafiya."
"A lokacin da muka je Abuja bamu ji da daɗi ba, amma don Allah ka ƙara kira mini ita na ƙara roƙonta ko za a dace."
Jiki a sanyaye ya miƙe bayan ya sanar masa da yana zuwa ya shige sashinta wanda ya same ta da uban tulin kaya a gabanta tana gyarawa ta a za saka a cikin mota a kai gidan
Ajmal saura ne wanda ba a kai ba.
"Hajiya Baaba, mahaifin yaron nan ne ya ƙara zuwa a karo na biy.."
"Kai dakata! Da hankalinka kake ƙoƙarin neman aure cikin aure? Ni ban ga wani abin damuwa don ya rasa Jannah ba, saboda ban taɓa ganin ubanka sai ranar da aka kai ni ɗakina, kuma muka yi zamanmu lafiya lau, har da ya mutu sai da na yi kwanaki ban dawo hayyacina ba, amma su da yake yaran ƙarshen zamani ne wai sun iya soyayya har yake shirin kashe kansa. To kace masa ya mutu kansa don ba ni za a turmuƙa a rami ba." Ta ce tare da cigaba da aikinta.
Ganin ba ta da ninyar zuwa ya shigo da shi har cikin sashin na ta wanda tana ganinsa ta ci magani ta ci gaba da aikinta ba tare da ta kalle shi ba.
"Barka Hajiya, m..."
"Kai dakata! Yi waje ka ba ni guri domin babu kalmar da za ka yi amfani da ita na sa a fasa auren nan, kuma kun san ai haramunne neman aure cikin auren, amma saboda mugun son zuciyarka kake son a fasa don a bawa É—anka da yake gwal ne."
Jannah da take kwance tana kuka cikin bargo haƙoranta na karkarwa don ta bata da gaske auren za a yi mata. Tun ranar da aka yi danki ta kwanta ciwo take kuka da shuka rashin mutunci da ihu amma a banza don tana fanin ba duka ta rufe ta da shi ba babu yadda za a yi ta fasa auren
Jin an ambaci mahaifin Huzaifah ya sa ta diro daga gadon daga gadon da take kwance wanda Ummu ke gefenta har hawaye ta yi mata akan ta tashi tasha ko ruwan tea, amma ta ƙi.
Ganinta kawai suka yi a gabansu cikin kuka ta kalli mahaifinsa ta ce,"Dad, where is Huzaifah? I miss him. Don Allah ka gaya masa ya zo gare ni domin zuciyata ba za ta iya É—aukar girman rashinsa ba."
"Munafuka dama lafiyarki lau, kike ma mutane iskanci ki kwanta kina numfarfashi, amma yanzu daga ambaton Huzaifah kin sheƙo da gudu kina gudu bamfaleƙe."Cewar Hajiya wanda ba ta bi ta kanta ba.