← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 79

Sashe 56

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa ta yi ta nufi kicin ɗin ba tare da ta ce komai ba lokacin da Aby ya ce,"Ki duba ma ta ba za ki rasa na serchet ba."
"To." Ta amsa sannan ta shige kicin É—in.

Mom zaune a bayan mota da waya a hannunta tana duba tsaƙonnin da aka turo mata ta twinter. Daina duba tsaƙon ta yi tana kallon tanƙamemen get ɗin da aka rubuta Alcharity Foundation Center da rubutu manya a saman get ɗin.

Idanunta suka kawo ruwa ta sanya hannunta ta share daidai lokacin da direba ya yi parking.

"Barka da dawowa shugaba." Ma'aikatan gurin suka rinƙa faɗin haka cikin girmamawa.

Hannunta take ɗaga musu cikin murmushi har ta ƙarasa cikin ofis ɗin.

"Barka da dawowa uwar marayu haƙiƙa ƙungiyarmu ta yi kewarki ƙwarai."

Rungume juna suka yi cikin farin sake ganin juna.

"Na yi kewarku gabakiÉ—ayanku musamman ke aminiyata." Ta ce tana murmushi.

Kujera ta isa gareta ta zauna tana kallon Hajiya Turai da ta ƙaraso ta nemi kujera kusa da ita.

"Ba ni da lokaci sosai ina files ɗin da na ce ki aje mini, sannnan kin tura ma wannan matar da za a yi mata aikin ƙoda?"

Wayarta ta ciro tare da shiga cikin hotuna tana faÉ—in,"Tun daren jiya na tura musu domin har anyi aiki, jiran farfaÉ—owar matar kawai muke jira."

"Good! Aikin ki na kyau, Ubangiji ya bamu ladar hakan."

"Amin." Ta amsa sai kuma ta mai da hankalin akanta bayan ta karɓi wayarta da ta gama kallon hotunan ta miƙa mata ta mayar cikin al'jihunta.

"Wannan matar da ta damu kan tana son ganinki, yanzu haka mun yi waya da ita tana kan hanya ina fatan za ki jira ta, saboda yanayin matar tana cikin tsananin buƙata, amma ta ƙi yadda mu taimaka mata dole ke take son gani."

"Eh, zan iya jiranta, amma in har ta ƙara minti biyar ba ta ƙaraso ba sai dai gobe, domin ina da meeting." Ta ƙarashe maganar tana duba agogon hannunta.

"In sha Allahu za ta ƙaraso."

"Allah ya sa hakan." Ta ci gaba da duba files É—in da take yi.

Wayar Hajiya Turai ta yi ƙara da sauri ta miƙe tana faɗin,"Yauwa ga ta nan ma ta iso."

"Ok, ki shigo da ita ciki."

Fita ta yi tare da É—aga mata kanta wanda ba ta cika minti goma ba, sai ga ta sun shigo da wata mata cikin wani yagalelen hijabi da doguwar rigar da ta mutsutsutsuke.

Duk yadda mom ta so karta toshe hanci sai da abin ya faskara, domin wani irin wari take jin yana tashi, wanda ba ta san lokacin da ta kai hannu ta toshe hancinta, tana jin yadda kayan cikinta ke hautsinawa ba, inda Allah ya taimaketa ba ta karya ba don babu abin da zai hana ta amayar da kummmalon.

"A uwa ba da mama ko dai na fita da ita ne? Na ga yadda kike ɓata fuska kar dai kiyi amai? Sai da na gaya mata ta nemi duk irin taimakon da take so za mu ba ta, amma ta n ce dole sai ta ganki"Hajiya Turai ta furta cikin ɗaga murya tana mamakin matar.

"A'a, kar ki damu ƙyaleta." Ta furta tana ƙoƙarin daure warin amma ta kasa.

"Wayyo Allah na shiga uku! Yanzu Halee, nufinki ba ki gane ni ba? Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Khamis ka cuce ni kai mai da duniyata mara amfani in har zan yi canzawar da Halee, za ta kasa gane ni. Ni kam mene ne amfanina a rayuwata"

"Mujee!" Ta furta cikin tsananin mamaki da tare da sakin wayarta ta ƙaraso gareta ta kama ta, ba tare da ta damu da warin ba."

"Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi? Ta riƙe ta tana girgiza ta tare da kallon mamaki ganin yadda ta joma tmkar mahaukaciyar da ta shekara tana hauka.

" Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsa ko ɗaya, sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta.

"Zuciyata ta kasa yarda kece wannan Mujee, ina iyayenki suka bar ki cikin wannan halin?"

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 26-27*

*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*

*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi?" Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsawa sai sharɓar kuka take.

"Don Allah Hajiya ki saketa karki shafa ma jikinki warin da take yi, idan ma kin san ta ne, to ki bari ta daina wannna warin."

"Ƙyale ni Hajiya Turai ba ki san wace ce ita a gareni ba, saboda ita ɗin ƙawace a gareni, wanda ƙawancenmu ya rikiɗa ya zama 'yan'uwanta tana daga cikin mutanen da suka ƙarfafa mini kafa wannan ƙungiyar ta kuma taimaka da hannunta har da gudummuwarta, daga baya bayan ta yi aure na neme ta na rasa. Don Allah ki bamu guri."

Jin abin da ta faÉ—i ya sa ta É—auki wayarta ta fita tana waiwayon matar cikin tsananin mamaki, domin farkon zuwanta sun yi tunanin mahaukaciya ce.

"Me ya faru kika dawo haka, ina Kham É—in ki? Ta ya ya akai ya barki cikin wannan halin duk da irin son da ya nuna miki, domin zan iya cewa soyyarku ita ce na farko da ya fara jawo hankalina na fara soyayya."

Kuka ta ƙara fashewa da shi."Me kike so na gaya miki akan Kham domin abubuwa da dama sun faru, wanda tuna su sawa yake na tsani kaina da ranar da na fara saninsa a duniya. Haƙiƙa ya cutar da rayuwata. Halee, labari ne mai tsayi wanda ba zan iya gaya miki a halin yanzu ba, domin yunwa na ke ji rabona da abinci kwana biyu kenan, ni kaina dauɗar jikina ji nake kamar zan amayar da 'yan hanjina."

Ƙara kallonta ta yi cikin mamaki tana ƙara mamakin wai Mujee 'yar ƙwalisa ta dawo haka! Lallai rayuwa ba abin taƙama bace, in ta tuna da turare in har bai kai 50k ba duk ƙamshinsa ba ta iya fesawa.

"Kai wai me wasu maza suka mai da mata ne? A kodayaushe sun mai da mu wulaƙantartu su yi duk rashin mutuncin da suka ga dama akanmu saboda sun san Allah ya haɗa rayuwarmu, ba za mu iya rayuwa sai da su ba?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ɓacin rai tana kallon yadda aminiyarta ta koma saboda tabon ɗa namiji wanda ita ma tana ɗauke da shi."

"Mu je gidana ki yi wanka ki canza kaya, sannan ki ci abinci sai mu tuna bayan rabuwa." Ta ce tana kama hannunta cikin rashin ƙyanƙyani.

A lokacin da suka fito mutane suka rinƙa kallon su cikin tsananin mamakin ganin tana riƙe da hannun matar da in ta matso su za su iya guduwa domin ba ta da marana da mahaukaciya.

A mota babu wanda ya iya magana a tsakaninsu sai Mujee, da take kallon unguwar da suka shigo mai tsananin kyau da gidaje masu kyau na fitar hankali.

A lokacin duka mutanen gidan suna zaune a falo suna kallo ban da Jannah da ta ke zaune gefen dad tana ta chatting da Huzaifah yayin da fuskarta ke saukar da wani irin tsadadden murmushi.

Da sallama ta shigo cikin falon Mujee na biye a bayanta, wanda ta tsinke da kyawun gidan sai kawai ta fara tasbihi ga Allah MaÉ—aukakin Sarki, domin wannan gida ya cancanci a kira shi aljannar duniya.

Da sauri Jannah ta miƙe cikin zabura ta ɓoye a bayan da wanda shi ma ya miƙe yana kallon matar cikin mamaki da tuna son inda ya taɓa ganin fuskarta.

"Mom, who is she? She looks like mad woman." Ta ƙarashe maganar tana toshe hanci don har ta ji amai zai zubo mata.

"Watch your mounth, she is friend of mine. We ran off today."

"No way! This is absolutely impossible this mad woman to be your friend, mom." Ta ce tare da rugawa cikin bayi ta fara kera amai.

"Halima yanzu taimakon ya wuce ki taimaka a waje sai ƙin kawo su gida, ai wannan gidan mahaukata ya kamata ki kaita." Cewar Hajiya Baaba cikin zare ido.

Ta kalli dad da fuskarsa take cike da alamun tambagar wace ce, tare da mata kallon sani ta ce,

"Na san ba lallai ba ne ku iya gane ta ba, domin duk kusancin da ke tsakaninmu na kasa gane Mujee, 'yar Kaduna wacce muka yi Jami'a har tana zama a gidammu." Ta ƙarashe maganar cikin kuka tana rungume ta.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'in!Duniya ina za ki damu? Ke Mujidatuu, mai ya same ki ina mahifiyarki Hajiya Maryama da mahaifinki Alhaji Sani."

Kuka ta fashe da shi ta nufi Hajiya Baaba za ta rungume amma sai ta matsa tana toshe hanci saboda wani irin ƙarni da ya dumfaro ta.
Chapter 56 · 0% Book details