Sashe 3
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
kasa bacci sai juye-juye take ga shi wani irin sanyi da yake shiga jikinta. Da sauri ta miƙe ta ɗauko maganinta, domin tana jin kamar ciwonta ne zai tashi, amma sai dai ko da ta sha maganin ba ta ji sauki ba, sai ƙaruwa da yake yi. Miƙewa ta yi a hanakali ta yi ɗakin dad. "Dad ka buɗe mini ƙofa ba ni da lafiya." Ta ce jin ya ji ƙwaƙwansa ƙofar da ta yi. Da sauri ya buɗe ƙofar ya kamata suka shiga. Maganinta ya ɗauko ya ɓalle mata tasha, sannan a hankali sanyin ya fara ruguwa bacci ya kwasheta. Kamar yadda ta faɗa sai da ta yi sati biyu sannan ta dawo da misalin bakwai na yamma. A ranar ba su gaɗu da Jannah ba, don tana dawowa ta kulle kanta ta fara baccin gajiya. Jannah kuwa da ta dawo daga school ta samu ta dawo, tsaki kawai ta yi ta shige ɗakinta, ko kaɗan ba ta yi murnar dawowarta ba. Dad ne yake da rawar jiki da murna, har take away fita ya yi mata, wanda ba ta ci ba sai dai aka sa a frig sakamakon naunanyar baccin da ya kamata. Washe gari da safe tana zaune tana shan tea Jannah ta fito cikin doguwar riga iya gwiwa. "Hi," ta ce mata tare da neman guri ta zauna tana ƙoƙarin zuba abinci. Sai abin ya ba ta dariya sosai, ta san haushin abin da ya faru take yi."Jannah na dawo kuma.." "Excuse me please, I got to take this call." Ta ce tare da ɗaga mata hannu ta shige ɗakinta. Ganin hakan ita ma ta shirya ta tafi ofis. Tsaƙar dare da misalin biyu saura kwata Jannah ta fito daga ɗakinta cikin rawar sanyi tana kiran sunan dad tunawa jin za ta mutu. "Dad please ka taimaka mini." Ta furta tare da fashewa da kuka. Mom ce ta ji kukan sakamakon ba bacci take yi ba aiki take yi a laptop ɗinta, wanda da sauri ta fito ta kamata." Lafiya Jannah, ciwon ne ya tashi?" Ta tambayeta ba tare da ta jira amsa ba ta ruga ɗakinta don ɗauko magani. Duk da ta ba ta amma sai bai lafa ba, wanda hakan ya ta hankalinsu matuƙa musamman dad da ya ƙe jin kamar ya mai da ciwon a jikinsa. Sai kusan asuba sannan ta samu bacci ganin haka koda gari ya waye mom ba ta tashe ta aba akan su je asibiti sai da ta ba ri don kanta misalin sha ɗaya saura ta tashi. A lokacin dad ya tafi gurin aiki sakamakon kiran gaggawa da ya samu wanda kan dole mom ita za ta kai ta. Bayan sun isa asibitin likita ya yi gwaje-gwajen sannan ya ɗago kansa ya ce, "You should take Jannah back to Nigeria due to her situation. I believe that's the best solution for her illness. The climate in Nigeria is much warmer than in London, which might be beneficial." Ya karashe maganar yana duba files ɗin da ke kan teburinsa. Shiru ya ratsa na wasu ƴan daƙiƙa daga bisani ta katse shirun, bayan ta ɗan dogon nazari tare da kallonta da take ta rawar sanyi haƙoranta suna haɗuwa, ya yin da ta takure guri ɗaya. Duk wanda ya kalle ta ya san tana jin sanyin har cikin bargon ƙashinta ganin yadda ta yi. "I will make a decision, and whatever I decide, I’ll let you know. If going back to Nigeria will cure her illness, then I have no choice but to send her, even though I wanted her to complete her secondary school in London. I’ll be praying for the right solution," Ta ba shi amsa cikin jimamin halin da Jannah ta ke ciki." "Alright, take your time to think it through and come up with a solution," ya furta ya na examining yanayin yadda take rawar sanyi. Ɗaukar jakarta ta yi da kama hannun Jannah ta ce, "Alright, doctor. Let's catch up later. Thanks. Ya mike tare da rataye rigar likitancinsa yana taka mata ya ce, "it's my pleasure to assist someone as generous as yourself. " Murmushin ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fice daga ofis, zuciyarta cike da jimamin ciwon 'yar gudaliyarta. Haushi ko tsabar takaici zata kira abin da ta ke ji oho, ganin yadda 'yan jarida suka cika gaban asibitin. Jannah ta kalli 'yan jaridar ta juya tana kallon mom da ta haɗe rai tamkar hadarin da ke shirin zubda ruwa, duk da yanayin fuskarta ya nuna she didn't have the time to give them her full attention, but she needed to do something that would provoke a reaction. After all, those journalists were just so frustrating to deal with. Kamar karamar yarinya ta sake ihu da karfi. "Mum, I'm feeling absolutely frozen. Please do something that'll make you stop talking to those blabbermouths," ta furta cikin shagawaba da rawar sanyi a hakorarta. Cikin sauri ta juya ta kalleta sai kuma ta maida kallonta ga direba Maris. Idanunsa suka firfito ganin tsantsar bacin rai a fuskarta. "I'm so sorry, ma'am. It's not my fault at all, and I had no idea how they managed to track down your whereabouts. I just saw them, just as unexpected as you did." Ya furta muryarsa cike da tsoron ta domin ya san abubuwa guda biyu ta tsana wanda yana fatar kada rana ta kasance ya karya doka. Sai a lokacin ta tuna ta yi waya da sakatarenta, Pedris. It must be him! Ta ayyana hakan cikin ranta dai-dai lokacin da suka karaso gurin ta tare da jefo mata tambayo yi marasa iyaka. Ba tare da ta furta musu kalami ta ja hannunta suka shiga cikin mota, yayin da direbar ya ja motar da karfi, ya bar su jiki a sanyaye suna kallon hanyar da ta wuce. Jannah ta kwantar da kanta a kan saman kujerar ta ja karamin tsuka tare da faɗin, "Bloody cunts." Misalin ƙarfe goma na dare suna zaune a falo yayin Jannah take kwance akan akan doguwar kujera, har zuwa lokacin a takure take duk da cewar sanyin ya ragu ba kamar ɗazu ba. Daddy ya rage ƙarar tibin da yake saureren labarai tare da gyaran murya ya ce, "I was thinking the same as Doctor said Halee. You have to feel sorry for her and go back to Nigeria. It’s time for us to face reality and stop avoiding it. Abin da ya faru ai ya faru. " Shiru ta yi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk cewar ta yi kewar ƙasarta, sai ai tana ganin ba wannan lokacin ya kamata ta koma gida Nigeriya ba, domin a wannan lokacin sam ba zata iya ɗaukar damuwa ba, musamman da take son saka hannun jarinta a kamfanin Badoon. "I'm thinking she should go alone cus I don't have a plan for going back in ya so she can stay at Ya Muhammad’s house kafin na gama abin da zan yi na koma, ka san har yanzu James ya ƙi yarda na yi investing din share guda biyu a cikin kashi goma na hannun jarin." Daddy ya ɗan musƙuta tare da ƙara rage sautin tibin. "Har yanzu kin ƙi fahimta ta Halimatu, a ko da yaushe burin ki ki rinƙa yin lamuranki da kanki, duk cewar kin san ni mijinki ne ya kamata ace ni na ɗauki ragamar komai, bawai ina ƙalubantar lamuranki ba ne, sai dai ni ya kamata na jagoranci duk kan lamuranki, domin ita ‘ya mace has limitation. " Ya ɗan numfasa yana kallonta ganin yadda lokaci guda fuskarta ya canza ta haɗe rai tamkar wacce aka aiko wa da tsaƙon mutuwa. Ta ɗan ja fasali tare da kauda kanta barin kallonsa, bayan wasu ƴan daƙiƙa ta mai da ganinta garesa. "Ina tunanin mun gama wannan maganar kuma mun yi alƙawarin mantawa da ita a tsakaninmu." Ta ce ba tare da ɗauke kanta daga garesa. Ya ije remote ɗin hannunsa tare da takowa a hankali ya ƙaraso in da take zaune, daida lokacin da ta juya masa baya. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.