Sashe 24
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Wani irin razana ta yi tare da dafe ƙirji."Na shiga uku ni jikar mai gishiri! Bulala ɗari? Aiko ya ibo ruwan dafa kansa. Ma za muje na ga uban da ya tsaya masa a duniyar nan. Motar 'yan sanda zan sa Halimatuu ta ɗauko masa makarantar gabaki ɗaya ya shafe su."
Daɗi sosai ta ji ganin ƙaryarta ta ƙarbu. Sai ta share majina tare da miƙa mata hannu. "Ina jin ma ya karya ni. Ni kawai a cire ni a makarantar sai a ɗaukar mini malami a gida." Ta fakaici Hajiya ta yi murmushi sai ta ƙasa sakin kuka ta ce,
"Mugu azzalumi kawai! Ya san irin kuɗin da nake kashe wa jikina da man da nake shafawa, salon ya ɓata mini jiki. Yana ji da fuskarsa kamar ta biri."
"Mu je ki ga abin da zan yi masa, don sai ya yi dana-sanin dukanki. Shalelen jikata zai duka..
Kama hannunta ta yi suka nufi makarantar daga shiga ajin ba ta yi wata-wata ba ta kwaÉ—a masa mari har biyu.
"Uban wa ya tsaya maka za ka duki jikalle ta, ka san waye uwarta da abin da take shirin za ma?"
"Faɗa mishi Hajiya. Ƙila ya ɗauka yar gidan talakawa ce, wato ga matsiyaciya ya dake ni ya daki banza, mom zan kira sai ta wulaƙanta kaf zuriyarku."
Malam Aliyu da zuciya ta turniƙe shi sai ya tsaya yana kallonta ganin yadda take zuba uban masifa bakinta har kumfa yake yi.
Malam Kamal ne ya shigo da sauri jin hayaniyar dake tashi a cikin ajin, wanda ya cika da mamakin ganinta tana faÉ—a.
"Haba Hajiya! in rai ya ɓace bai kamata hankali ya gushe ba. Kiyi haƙuri abi komai a sannu-sannu. Ke Jannah wuce ki shiga aji."
"Ta je ina? Allah ya kyauta, sai ka ce ba ta da gata. Ai tabar islamiyar nan kenan."
"FaÉ—a musu." Cewarta tana gyara zama hijabinta tare da kaÉ—a kanta.
Nahlin jin muryarta da ga cikin ajinsu ya sa ta sheƙo a guje cikin ɓacin rai." "Hajiya Baaba, wannan wane irin zubar da ka.."
"Rufe mini baki shashashar banza! Saboda ba ki da hali maimakon ki taso ki ceci 'yar'uwarki, amma kina ji an kamata an yi mata bulala har É—ari saboda rashin mutunci."
"ÆŠari?" Suka haÉ—a baki gurin tambaya. Majina ta ja tare da sakin kuka
"Ƙarya na yi? Haka fa ya rinƙa dukana kamar ya samu jaka." Kama hannunta tayi suka fice ya yin da take yi wa malamin gwalo. "
A hanya jawo mishi tsinuwa d jafa'i ta rinƙa yi har suka shig cikin gida.
"Hajiya Sanyi na ke ji ba ni da lafiya." Tsaki ta buga tare da kama ta tana faÉ—in,
"Ma za hau gado ki kwanta. Bari na É—auko ruwan zafi na daddana miki jikinki, haka kawai saboda mugunta ya tashi kashe mini jikata É—aya tal da na samu."
Murmushin jin daÉ—i ta yi. "Yauwa Alhamdulillahi na huta da fita zuwa islamiya." Sai ta É—auki wayarta don ta sanar da daddy.
Hajiya Baaba kuwa hnakalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin tana matuƙar sonta sosai. Gani take kamar Halimatu ce a gabanta. Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi tare da ƙara janyo mata bargon ta rufe ta, don a tunaninta bacci za ta yi.
"Ina sonki fiye da yadda nake yi wa mahaifiyarki, don ma wani lokacin ba ki da mutunci da ko tsinke ba zan bari ya taɓa ki ba." Ta furta a ranta ta ɗauki robar ruwan zafin ta fita bayan ta ja mata ƙofa.
Tana fita ta saki dariya tana rawa. Wayarta ta ɗauko ta kunna data. Numbar Hazaifah ta kira suka fara hira, yayin da zuciyarta ke cike fall da farin ciki, domin ita a ganinta karatun takur ne a gareta, don ko lokacin da take London so huɗu a wata ake mata karatu, kuma duk lokacin da malamin yazo sai dai ta ce ba ta iya ba ya biya mata, don haka take jin kamar an cire mata ƙaya.
Aby na dawowa ko parking bai gama ba Hajiya ta fito tana bambami tare da rantsuwar ba za ta ƙara komawa makarantar ba.
Saboda tsabar takaici kasa ce mata komai ya yi, sai da ya ɗauki tsawon lokaci yana sauraren ta, sannan ya fara ba ta haƙuri cikin ladabi. Girgiza kansa ya yi kawai ya wuce sashinsa.
Haka kuwa aka yi. Hajiya ta shafa ma idanunta toka akan ba za ta ƙara zuwa islamiya ba, duk da irin haƙurin da Aby ya ba ta ya kuma sanar mata da ya gargaɗe su akan ba za su ƙara dukanta ba, amma ƙememe ta nuna ba shi da iko da it ta hana zuwa.
"Ni ma naga ba jahila ba ce, sai da na sauke kur'ani, kuma É—an haddar nan da hadisai na sani, don haka zan fara koya mata kafin a samu wata makarantar."
Jin abin da ta ce babu yadd zai yi kan dole ya haƙura domin ita ce mai faɗa a ji a gidan. Fatan shi Ubangiji ya ba shi damar yi mata biyayya har ranar da mai rabuwa za ta raba su.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ajmal ba ya nan, domin ya tafi Ƙasar Cairo zai yi tsawaon watanni uku.
A ranar da ake sa ran dawowarsa. Gidan ya kacame da aiki ba matsaƙa tsinke sa toye-toye ake yi, yayin da ƙamshi ya cika gidan.
It kanta Hajiya Baaba ba'a barta a baya ba, gurin zama ta shirya masa tuwon shinkafa da miyar ganye har da dabbu masu rai da lafiya sanin cewar yana so.
Jannah dake falonta tana kallon Arewa24 wani lokacin kuma tama danna wayarta. Juyo wa ta yi ta kalli Hajiya da take ta safa da marwa a kicin É—in.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 10-11*