← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 79

Sashe 75

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta shi ki wuce ciki domin yanzu ke matar wani ne." Ta ce tare da kamata wanda ta fisge ta kama ƙafafun mahaifinsa da ya fara tafiya domin ya sare ba za ta amince ba ɓata bakinsa kawai yake.

"Don Allah karka tafi ka gayawa Huzaifah ya buɗe wayarsa zan kira shi mu gudu muje can mu yi aure." Ta ƙara faɗi cikin kuka.

"Au ki gudu ki ban ni da jin kunya ko kina ganin an fara zuwa bikin, to in kika ga kin leƙa waje sai kin gudun wawiya kawai." Ta ce tare da kamata ta riƙe tamau ta shigar da ita ciki wanda ta yi ƙoaƙrin ƙwacewa amma ta kasa.

"Haba 'yannan, to ko mahaifinki na riƙe ai bai isa ya ƙwace ba." Ta ce tara da kaita har cikin ɗakinta ta rufe ƙofa.

"Ummu!Ummu!! Shikenan, Hajiya Baaba, ta raba ni da masoyina Huzaifah na shiga uku!" Ta ce tare da ƙara rushewa da kuka ta faɗa jikinta.

Huzaifah kwance a tanƙamemen falon su yana riƙe da wayarsa da dad ɗinsa ya karma tun ranar da suka je gidan su Jannah.

Har yau zuciyarsa ba ta daina tunanin wulaƙancin da Hajiya Baaba ta yi musu ba, wanda ya cika da mamaki ya gasganta kura ce da fatar akuya.

"My son, the you mean you will keep thinking about her? Ka na son na rasa ka ne? Ka san cewa ba zan iya rayuwa in har babu kai ba." Mom É—insa tace cikin muryar kuka tana share hawaye.

"I love her mom, I really love her like crazy. Tun ranar da muka haÉ—u a filin jirgi na ji a raina da ita kawai zan iya rayuwa. Ita É—in tamkar maganaÉ—isu ce a cikin rayuwata, don Allah ku taimaka ku ba ni ita karku sanya zuciyata ta buga."

Sai ya riƙe hannun dad ɗinsa yana dannawa a kan ƙirjin shi da ke harbawa fat! Fat!! wanda har sai da mahaifinsa ya cire da sauri saboda irin ƙarfin harbawar da take yi.

"Ka ji ko dad, harbawar da zuciyata take yi ƙara mini sonta take a cikin zuciyata wanda in har ban same ta ba zan iya mutuwa. I have to give you my will cus I'm gonna die, I can't make it without her." Kamar ƙaramin yaro ya saka kuka tare da rungume mahaifinsa da yake kallonsa cikin tausaya.

"Ya kamata mu koma gidansu Jannah mu ƙara roƙonta saboda in har ɗana ya mutu na rantse sai na yi shari'a da ita." Cewar mom da take zubar hawaye domin ba ta taɓa ganin abin da ya ƙwallafa ransa akai har ya kaishi zubar da hawaye da kwanciya ciwo.

"Na nawa saboda, I went to Zariya jiya, amma in vein don ya rage one weeks aurenta da shi."

"What!" Ya ce tare da miƙewa tamkar zai zura.

"No, it can't be her. Jannah ba za ta bari ayi mata aure ba da ni ba." Ya ƙara faɗi cikin zautuwa sai kuma ya sa kuka ya koma ya kwanta yana suratai kamar ya zare.

"Innalillahi! Suma yake yi fa kar ya mutu." Cewar mom ganin idanunsa na ƙyafƙyaftawa.

Da sauri dad ya kama shi ya rungume yana kiran sunansa.

"Jannnahh." Ya ja sunan tare da yi masa wasali da gunna sai kuma ya yi shiru can ya buÉ—e idanu ya fara tari sai aman jini, wanda ya É—aga hankalin iyayensa suka sa ihu tare da kiran direba.

Dad ya taitaye shi ya sanya a mota yana girgiza shi da kiran sunan shi amma ina sai aman jini yake yi.

A lokacin da suka isa asibitin da ƙyar likitoci suka yi nasarar dawo da shi cikin hayyacinsa ya daina aman jinin, amma bai daina kiran sunan Jannah ba.

Doctor ɗin ya fito yana share zufar goshinsa wanda yana buɗe ƙofa suka yi kansa.

"How is he likita? Ya farfaÉ—o ya jikinsa." Suka tambaya cikin tsananin tashin hankali.

"Please, do whatever you can to make him to have yarinyar da yake faÉ—i." Cewar likitan yana kallonsu.

"Ba zai iya samunta ba saboda kwana biyu ya rage a ɗaura mata aure doctor, da ace kuɗi na amfani da zan yi na samar mishi yarinyar, amma iyayenta ba sa buƙatar kuɗi, saboda suna da su." Ya ƙarashe maganar cikin rauni yana share zufar goshinsa.

"Mafitar ceton rayuwarsa shine a samar masa da abin da yake so."

"Hakan ba zai yiwu ba doc na gaya mata babu yadda za a yi na shawo kan iyayenta."

"Innalillahi! Yanzu rasa shi zan yi kenan? Don Allah likita ka yi wani abu wallahi shine kawai É—a namiji da Allah ya ba ni."

"To ku yi masa viser ya bar Ƙasar nan, zan haɗa ku da wani doc a India yana da sani sosai akan zuciya in sha Allah zai samu sauƙi saboda ya kamu da ciwon zuciya gab take da ta buga."

"Innalilahi!"Suka furta a tare suna hawaye.

"Ok, I will give me the doctor's numba." Dad ya ce a firgice tare da É—aukar wayarsa ya kira akan a fara nema masa viser na su duka ukun.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi viser suka nufin India ba tare da ɓata lokaci ba.

A lokacin da suka isa Ƙasar India hankalinsu ya tashi kwatankwacin tashin gwauron zabi! Don babu numfashi suka isa da shi, wanda jinin su ya yi sanyi tamkar ƙarƙarar dake cikin firij.

Suna kallon shi ta gilashin É—akin an sanya masa oxygen yana kwance shememe kamar gawa sai cikinsa da yake É—an motsi alamun akwai numfashi a jikinshi.

"Ke kam wannan tsohuwa sam ba ki yi man adalci ba sai Allah ya sakawa waÉ—annan yara saboda son zuciyarki ki nemi ki kashe mini É—ana É—aya tal da na mallaka." Ta ce cikin matsanancin kuka tana jin kamar ta É—auki bindiga ta harbe ta har lahira.

A ranar da mom ta shirya za ta taho sai aka kira ta kan wata mata ta haihu 'ya'ya biyu babu jini babu abincin da za ta ci ballantana kayan da za a sanya wa jariran ga shi mijin ya mutu."

"Innalillahi! Kai maza anya wasu suna tausawa mata kuwa? Dole na zo na taimaka mata ina ganin ke Hajiya Turai, ki je garin nan da za ku je ni da Mujee, sai muje cikin shiri daga nan mu wuce Zariya, kin ce sai jibi za ku zo ko?"

"Eh, kon san dole na jira baƙinan mu taho."

"Ok tom shikenan, don Allah ki karɓo mini kayan mata na SURAIYA D kin san ba kowa ne maganin mata nake iya siye ba, amma sai nata saboda yana da inganci kuma akwai aiki sosai."

"Haka ne km SURAIYA D kayan matan ta ingantattu ne, ko ni bana iya amfani da ko wanne sai na ta. Ki ce wannan ango babu ragi tsakaninsu domin Uwa ba da mama kusan na dubu É—ari biyu kika siya."

"Eh, so nake ta kama mini shi a hannu kamar yadda na riƙe mijina, sannan surukin nawa tsadadde ne mai aji da ilmin addini, wanda ya san haƙƙin aure da sanin darajar mace, kin ga dole na yi mata gyara."

"Allah Sarki! Aiko na tausaya masa domin ya zo hannu don kayan mata na SIRAYYA D ka yi amfani da kaɗan ya ka ƙare ina ga kuma an sha da yawa."

Mai buƙar kayan matan SURAYYA D *Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

"Eh, haka nake so 'yata ta zamo zinariya a gidan aurenta kamar yadda na zamo, don Allah ki dafa duk sauyoyin nan in za ki zo."

"Yauwa na manta na ce zan gaya miki waÉ—annan magungunan ki fara mata kamar haka:

Kyaran jiki
Ki samu kokumba ki yi blending a tace a sai ki shafa a jikinki. Sau biyu ya kamata a yi, kin ga ko bayan auren sai ta ci gaba.

Maganin warin jiki:
Kanumfari lalli a haɗa a jiƙa a shafa a gaba.

Siddir
A ije mata siddir a gidanta ya fi ƙarfin aljanu.

HaÉ—in ayaba:
Ki sayi ayaba ki ɓare ayi blending 7-or 10 ya niƙu sai ki zuba milk the quantity you want then sai ki sugar ki aje a frij in ya yi aanyi kisha.

Sannan ki sanya ta kullum bayan asubahi ta rinƙa karanta YA WADUDU ƙafa ɗari hudu yana saka soyayya tsakanin masoya da kawo buɗi. Bari dai na barki da waɗannna in sha Allahu in zan taho zan dubo masu yawa harda addu'oin sace zuciyar miji da zaman lafiya."

Ajiyar zuciya mom ta yi mai ƙarfi a ranta tana tunanin yadda za ta iya tunkararta da magungunan.

"Na gode sosai Allah ya bar zumunci."

"Ba ki da matsala, sai mun zo ki gaishe mini da Hajiya Baaba uwar biki."

"In sha Allahu." Ta ce tare da kashe wayarta sannan suka shirya suka kama hanyar ƙauyen.

Jannah ta ci kuka har ta bawa uku lada tamkar za ta shiÉ—e duk ta rame ta fita hayyacinta.

Sosai Aby ya tausaya mata sai dai ba shi da abin da zai yi mata sai addu'a.

Dad kan dole ya shiryo ana saura kwana biyu biki ya kamo hanya don rarrashi jin taƙi ci ta ƙi sha.
Hankalinsa ya tashi ganin yadda ta koma wanda har sai da ya zargi kansa.

Ganinsa ta faɗa jikinsa ta yi kuka ta yi kuka tamkar za ta shiɗe wanda ya tausaya mata har sai da ya yi ƙwalla, domin tsananin tsanarsa da take yi ya bayyana a idanunsa.

Saboda tsabar kuka ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take wanda yake barazanar tafiya da numfashi

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 36-37*
Chapter 75 · 0% Book details